Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Ciwon Shawara Daga Zogale

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Ciwon Shawara

Kalmar shawara tana cikin jerin suna jinsin mata. Wata irin cuta ce mai sa yawan mutuwar jiki tare da mayar da ido rawaya (launi mai ruwan ɗorawa), daidai da bayamma (BUK, 2006 sh. 410). Kalmar Bayamma tana nufin ciwo mai tsotse jinin mutum. Akan kira ta mayanƙwamiya, ko fara ko ta sama. Fara wata irin cuta ce da yunwa take haddasawa; takan tsotse jini ta sa kwaɗayi, musamman ga yaro, har ya diga ramewa.

Yayin da aka dubi waɗannan ma’anoni da idon basira, za a ga cewa duk suna ishara ne ga ciwon shawara. Abin da ya wanzar da bambanci shi ne bambance-bambancen karin harshe da ya wanzu a tsakanin daulolin ƙasar Hausa.

Shawara a ilimin likitanci wasu cututtuka ne masu halayya da suka kusan yin kama, domin yadda sukan shafi gaɓoɓi daban-daban na jiki. Waɗannan cututtukan akasarinsu suna da alamomi iri ɗaya ne, sai dai sanadiyyarsu sun bambanta.

a.  Wasu suna ganin shawara ce takan kawo mutuwar jiki da rashin jin karfin a gaɓoɓi da yawan kwanciya da yin barci da rashin sha’awar cin abinci da rashin jin daɗin rayuwa gaba ɗaya.

b.  Wani zubin takan zo har da amai da ciwon ciki, fitsari yakan sauya ya kasance launinsa ya zama mai kama da ruwan ƙwai., Ƙwayar idanu kuma takan zama kore ko kuma mai ruwan ƙwai.

c.  Yana iya zuwa da yawan zazzaɓi ba mai zafi ƙwarai ba.

Bincike ya tabbatar da cewa ƙananan ƙwayoyin cuta ne suke shiga jiki su haifar da cutar shawara, kamar yadda Abdulƙadir (1990 sh. 13) ya nuna. Ya kuma bayyana cewa, ciwon yakan faru ne sakamakon lalacewar wasu ɓangarorin ƙwayoyin halittun jiki saboda tsufa ko gajiya.

Alamomin kamuwa da shawara sun haɗa da:

a.  Sauya kalar (launin) ido da fatar jiki zuwa kore ko ruwan ƙwai

b.  Ciwon naman jiki

c.  Kasalar guiwowi

d.  Ciwon ƙirji

e.  Amai da gudawa

Idan lamarin ya tsananta, sai a fara zubar da jini ta hanci da baki da naman jiki da fitsarin jini, kamar yadda Abdulƙadir (1990 sh. 17) ya nuna.

Yayin ƙoƙarin magance wannan ciwon, sai a dafa ganyen zogale tare da kanwa ‘yar kaɗan. A ci, a kuma sha ruwan don maganin shawara (Baba da Aiki, 2015). 

Post a Comment

0 Comments