An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Ƙaiƙayin Jiki
Kalmar jiki tana cikin kalmomin Hausa jerin sunaye jinsin namiji, jam’i
kuwa akan furta su da lafazin jikunaa ko jikkunaa a karin harshen
Sakkwatanci. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Sassan
da suka haɗu suka ba da surar mutun ko dabba ko wata halitta ta
daban, kamar yadda BUK (2006 sh. 217) suka nuna. Yayin da Abubakar (2015 sh. 225)
ya bayyana ma’anar da: “Gundarin ƙashi, tsoka da
fatar mai rai.”
Idan aka dubi waɗannan ma’anonin da idon basira, kai tsaye za a iya cewa, jiki
shi ne surar halittar ɗan’adam ko dabba wanda yake ƙunshe da mabambanta ƙasusuwa da jijiyoyi da tsoka (nama) da kitse da kayan
ciki lulluɓe da fata.
Ƙaikayin jiki kuwa, shi
ne rashin jin daɗin jiki da kan haifar da yanyami mai sa jiki zogi da raɗaɗi, wanda kan sa sai
an sosa fatar jikin domin a sami jin daɗi. Shi ma ƙwayar cutar baktiriya ce take haddasa shi. Masana kamar
Axe (2016) da Samuel (2013) sun nuna cewa amfani da zogale yana ƙara wa jiki ƙwarin garkuwa da
kariya daga kamuwa da cututtukan da suke wanzar da ciwon jiki. Yayin da aka
bayyana ta a matsayin maganin matsalar fatar jiki, musamman ƙurajen jiki.
Ta fuskar magance ƙaiƙayin
jiki kuwa, sai a samu ɗanyen ganyen zogale cikin
tafin hannu uku (3) a daka, a tarfa ruwa kimanin babban cokali huɗu
(4). A tace da ƙyalle
fari mai kyau. Ruwan ne za a riƙa
shafawa a wurin da yake yin ƙaiƙayin. Za a shafa maganin ne sau uku (3)
a rana har tsawon kwana bakwai (7) (Jinju, 1990 sh. 73) da (Garba Wanzam 2014). Masanan sun tabbatar da ingancin
maganin tare da rashin samun
wani lahani (aibu/cutarwa) a jikin ɗan’adam.
Ƙaiƙayin Al’aura
An riga an san ma’anar ƙaiƙayi, abin da ya
rage a kawo ma’anar al’aura. A luggance, kalmar tana cikin jerin kalmomin suna
jinsin mata, kamar yadda Garba (1990 sh. 5) ya bayyana. Asalin kalmar Balarabiyar
ce da aka aro daga harshen Larabci. Kalmar tana ɗauke da ma’anar tsiraicin
mace ko namiji.
A tsarin addinin Musulunci, tsiraicin namiji ya kama daga cibiyarsa zuwa
bakin guiwa. Yayin da mace duk jikinta ya kasance al’aura sai tafin hannayenta
da fuska. A fagen wannan nazari kuwa, ana nufin jelar namiji (mazaƙuta ko alƙalami ko zakari ko
bura ko gaba), a ɓangaren jinsin mata kuwa, ana nufin, farjin mace
(matuccin mace ko gutsu ko gindi ko gato ko duri ko tsele ko ɗangalso), kamar
yadda al’ummomin ƙasar Hausa suke kiran su a sassa
daban-daban. Don haka a nan, ana nufin ƙaiƙayin da yakan faru ga waɗannan sassan farjin
na namiji ko mace.
Akwai wata cuta da take addabar mutane musamman mata, a inda sukan
fuskanci matsalar matsanancin ƙaiƙayi a daidai farji ko dubura. Ire-iren
waɗannan
mata sukan fuskanci matsalar rashin son saduwa da maigida, a sakamakon mummunan
ƙaiƙayi
bayan jima’i. Dangane da maganin matsalar, sai sami saƙe-saƙin (ɓawon
icen) zogale a dafa tare da jar kanwa ‘yar kaɗan. Za
ta sha kofi ɗaya (1) safe da yamma, ta kuma riƙa yin tsarki da ruwan maganin (hira da Hayin Tulawa).
Haka su ma maza masu fama da
ƙaiƙayin
matsematsi, suna
iya yin amfani da wannan haɗin, don nema samun waraka. A
binciken Axe (2016) kuwa, ya nuna cewa amfani da zogale yana ƙara sha’awa a tsakanin ma’aurata. Ke nan yana kawar da
illolin da suke haifar da ƙaiƙayin al’aura. Ire-iren waɗannan
illolin kuwa ƙwayar cutar bakteriya
ce take haifar da su. Don
haka cin zogale ko shan ruwansa, muhimmin garkuwa ne ga jikin ɗan’adam.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.