Ticker

6/recent/ticker-posts

Maganin Ciwon Suga Daga Zogale


  An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Suga a Jikin Bani Adam

Jikin bani Adam yana buƙatar wani nau’in sinadarin suga da ake kira a Turance “glucose” wanda yake cikin jini domin gudanar da wasu muhimman ayyukan da suka danganci lafiyar jiki. Irin wannan nau’in suga yana bayar da kuzari ga jiki wanda ake buƙata wajen narkar da abinci da kuma rayuwar ƙananan halittu (cells) da suka tattaru da yawa suka gina jikin ko halittarsa.

Suga shi ne makamashin da yake ba wa jikin ɗan’adam kuzari domin rayuwa. Hanyoyin sadarwar ƙwaƙwalwa a jiki wato ‘nerves’ da jajayen halittun jini (red blood cells) duk suna amfani da wannan makamashi, wato suga (glucose) domin samun rayuwa. Ana samun sa ne daga nau’o’in abinci masu samar da kuzari kamar: Shinkafa da dawa da gero da masara da sauransu. Yayin da ɗan’adam ya ci abincin da yake ɗauke da suga fiye da yadda jikinsa yake buƙata, cikin ikon Allah sai wani sashen jiki da ake kira da suna mikin ciki (pancreas), kamar yadda Jinju (1990 sh. 239) ya kira shi, wato saifa kamar yadda mahauta (rundawa) ke kiranta, sai ta samar da ruwan sinadarin insulin da kan sa jikin ya tsotse sugan.

Ciwon Suga

Akwai dalilai da dama da sukan wanzar da ciwon suga a tsakanin al’umma. Wannan yakan faru ne a daidai lokacin da ɓangaren jiki, wato mikin ciki (pancreas) ta samu matsala har ta kasa samar da ruwan sinadarin insulin wanda yake maganin cutar suga, wanda kan sa jiki ya tsotse suga (glucose) da ya zarce kima. To sai adadin da yake cikin jini ya yi yawa ya haifar da illa ga jikin.

Ƙiba ma tana sa wuraren da ake tsotse suga a jiki su ƙi aiki. A bisa haka, idan babu wannan sinadari ko muhallin tsotsewar yana da matsala, sai sugan ya taru a cikin jini, har ya kawo illa ga wasu sassan jiki kamar ƙananan magudanun jini (jijiyoyi) na:

a. Idanu

b. Zuciya

c. Ƙoda

d. Ƙwaƙwalwa

e. Fata

f. Ƙafafu da sauransu

Hakan yana faruwa ne a sakamakon taruwar suga a cikinsu. Yana kuma yi wa wasu jijiyoyin lakka aibu, kamar na dubura da hanji da sauransu. Irin wannan illar ce take wanzar da yawan fitsari da jin ƙishirwa da zafin jiki da ciwon ƙoda da ciwon mafitsara.

Yayin da suga ya yi yawa a cikin jini har yakan buge mutum ya faɗi a some. Haka idan ya yi ƙaranci, musamman ga masu fama da matsalar. Wannan ne ya sa ya zama dole gare su da su dinga zuwa asibiti ana daidaita musu suga don ya kasance tsakatsaki.

Ana iya gadon sa. A bisa haka, wanda iyayensa da kakanninsa suka yi fama da matsalar, shi ma sai ya rinƙa zuwa asibiti ana masa awon suga a ƙalla sau ɗaya a cikin shekara.

Zogale a Fagen Warkar Da Ciwon Suga

Itaciyar zogale tana taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalar ciwon suga. Akan samu wasu lokutan sai an haɗa ta da wasu abubuwan, wani lokacin kuwa ita kaɗai ta wadatar kamar yadda za a gani.

1. A nemi furen zogale a haɗa da citta mai yatsu a dafa, a rinƙa sha kamar shayi. Yin haka yana maganin cutar da take haddasa yawan fitsari wato diyabitis.

2. A haɗa zogale da yaɗiya a dake, a dinga zubawa a ruwan zafi ana sha sau uku a yini, wato da safe da rana da dare. Aiwatar da wannan haɗin kamar yadda aka zayyana yana kawar da ciwon suga da izinin Allah (Alaramma, 2015).

3. Haka kuma, wanda yake fama da irin wannan lalurar, sai ya ɗebo ganyen zogale tun da safe kafin rana ta fito. A shanya shi a wajen da ba hasken rana har ya bushe. In ya bushe sai a rinƙa dafa shi kamar shayi ana sha da madara, sau biyu a rana. A kula da zuwa wajen awo. Idan ba sauran ciwon suga sai a daina sha (Jafaru, 2011). Binciken Godinez (2015) ya tabbatar da cewa: “Shan Ruwan zogale a kowace rana yana magance illar ciwon suga a jiki.” Shi ma Samuel (2013) ya bayyana zogale yana daidaita sukari da yake cikin jinin jikin ɗan’adam.

Lura: Gayen zogale da za a ɗiba kafin fitowar rana ba shi da alaƙa da tsafi ko sihiri. Akan yi hakan ne kawai domin samun ganyen gabanin zafin rana ya doke shi. Sakamakon zafin ranar yana iya kawar da wasu sinadarai da suke cikinsa.

Post a Comment

0 Comments