Ticker

6/recent/ticker-posts

Asalin Samuwar Maganai

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Asalin Magani

Duk wata cuta da Allah Maɗaukakin Sarki ya halitta, sai da ya saukar mata da magani. Hadisan Manzon Allah (S.A.W.) da dama sun jaddada hakan. A wani hadisin, Manzon Allah (S.A.W.) ya ce:

مَا أَنْزَلَ اللَّهُ دَاءً إِلَّا أَنْزَلَ لَهُ شِفَاءً

Mā anzalallāhu dā'an illā anzala lahū shifā'an.

Fassara

Allah bai saukar da cuta ba, face sai da ya saukar da maganinta.

(Sahih al-Bukhari: 5678)

A wani hadisin na daban, an rawaito cewa:

عَنْ أُسَامَةَ بْنِ شُرَيْكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: كُنْتُ عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَجَاءَهُ أَعْرَابِيٌّ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَنَتَدَاوَى؟ قَالَ: «نَعَمْ، يَا عِبَادَ اللَّهِ، تَدَاوَوْا، فَإِنَّ اللَّهَ عَزَّ وَجَلَّ لَمْ يَضَعْ دَاءً إِلَّا وَضَعَ لَهُ شِفَاءً، إِلَّا دَاءً وَاحِدًا»، قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، وَمَا هُوَ؟ قَالَ: «السَّامُ».

'An Usāmata bni Shuraykin raiyallāhu 'anhu qāla: Kuntu 'inda n-nabiyyi allallāhu 'alayhi wa sallam wa jā'ahu a'rābiyyun fa-qāla: Yā Rasūlallāhi, a-natadāwā? Qāla: «Na'am, yā 'ibādallāhi, tadāwaw, fa-innalāha 'azza wa jalla lam yaa' dā'an illā waa'a lahū shifā'an, illā dā'an wāidan». Qālū: Yā Rasūlallāhi, wa mā huwa? Qāla: «As-sāmu».

Fassara

An ruwaito daga Usamah bin Shurayk (Allah ya yarda da su) ya ce: Ina zaune a wurin Annabi (S.A.W.) sai wani Balarabe na ƙauye ya zo ya ce: 'Ya Manzon Allah, ko zan nemi magani?' Ya ce: 'E,' ya kai bawan Allah, ku nemi magani, lallai Allah Maɗaukakin Sarki bai sanya wata cuta ba sai da Ya sanya mata magani, sai dai cuta ɗaya.' Sai suka ce: 'Ya Manzon Allah, wace cuta ce?' Sai ya ce: 'Tsufa.'"

(Sunan Abi Dawud: 3855; Sunan al-Tirmidhi: 2039; Sunan Ibn Majah: 3436)

Bugu da ƙari, Manzon Allah (S.A.W.) ya jaddada cewa Allah ya saukar da magani ga kowace cuta, sai dai kawai idan ba a san maganin ba. Ya ce:

مَا أَنْزَلَ اللَّهُ دَاءً إِلَّا أَنْزَلَ لَهُ شِفَاءً، عَلِمَهُ مَنْ عَلِمَهُ، وَجَهِلَهُ مَنْ جَهِلَهُ

Mā anzalallāhu dā'an illā anzala lahū shifā'an, 'alimahu man 'alimahu, wa jahilahu man jahilahu.

Fassara

"Lallai Allah bai saukar da cuta ba, sai da ya saukar da maganinta. Duk wanda ya san maganin cuta, ya san shi. Wanda bai sani ba, bai san shi ba (maganin). Waɗanda suka jahilce shi, ba su san maganin ba."

(Sahih al-Bukhari: 5678; Sunan Ibn Majah: 3436; Sunan Abi Dawud: 3855)

Waɗannan hadisai suna tabbatar mana cewa, dukkan cuta tana da magani, sai dai idan al’ummar da take fama da cutar ba su fahimce ta ba ko kuma ba su san maganin ba.

Magani ya samu ne tun bayan da Allah maɗaukakin sarki ya halicci Annabi Adamu A.S sai ya sanar da shi dangogin ilmomi masu yawan gaske cikin yardarsa (Alƙur’ani, 2: 31). Daga cikin ilmomin kuwa har da ilimin cututtuka da yadda za a magance su. Haka ya halitta wasu tsirrai a doron ƙasa domin amfanin Annabi Adam da zuriyarsa. Aka kuma fahimtar da su hanyoyin sarrafa su a matsayin maganin yunwa da na cututtuka.

Yayin da zamani ya shuɗe, mutane suka ƙara yaɗuwa da bazuwa zuwa sassa daban-daban na duniya, sai Allah ya kimsa wa ɗan’adam hikima da basirar haɗa wasu itatuwa da sinadarai domin su kasance maganin wata cuta da ake buƙatar warakar da ita. A cikin jinƙansa da rahamarsa, wasu lokutan ya jefa wa ɗan’adam tunani a ransa, in aka yi amfani da abu kaza zai yi maganin ciwo kaza da kaza.

Wasu lokutan kuma a mafarki za a gaya wa ɗan’adam, ya yi amfani da wani abu don maganin wata cuta. Wani zubin kuwa, murya kawai mutun zai ji kamar daga sama, ana umurtar sa, ya yi amfani da abu kaza domin magance cuta kaza. Haka kuma, iskoki suna iya sanar da mutane sirrukan magunguna.

Akan kuma sami magani ta hanyar gwaji da kwatantawa, musamman ta la’akari da yadda dabbobi da tsuntsaye suke amfani da ’ya’yan itatuwa da hakukuwa da ganyaye yayin da suke cikin yanayin rashin lafiya, da yadda suke nuna halin ko-in-kula da su a lokacin da suke cikin ƙoshin lafiya (Adamu, 2003 sh. 10).

Yaɗuwar al’umma sakamakon hayayyafa da nuna kyakkyawar biyayya, ya wanzar da ɗorewar mallakar asiran magani daga hannun masana magunguna na haƙiƙa. Kyakkyawar biyayya ta sau-da-ƙafa takan sa a sanar da waɗansu daga cikin zuriya ko waɗanda suka yi barance asiran magungunan da Allah ya sanar da masanansu. Ta waɗannan hanyoyi ne aka ci gaba da gadon asiran magungunan gargajiya a ƙasar Hausa. Kuma ta irin wannan hanya ce ilimin sirrin magungunan da zogale yake ƙunshe da shi ya ci gaba da bunƙasa har ya kawo wannan marrar da ake ciki. 

Post a Comment

0 Comments