An ciro daga littafin:
An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768
Tuntuɓa Domin Samun Littafi: Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354
3.2.2 Bunƙasar Sabis Ɗin Intanet
A
ɓangare guda
kuwa, shi ma sabis na intanet ba lokaci
guda aka samar da shi cikin siga da tsarin da yake a yau ba. Bayan haka, bai
kasance nau’i ɗaya
kawai ba. Akwai nau’o’in sabis na intanet daban-daban.
Masana na samar da rabe-raben intanet ne ta la’akari da faɗin wurin da sabis na intanet ɗin yake kaiwa.[1] Fitattu daga cikin nau’o’in sabis na intanet su ne:
1. Keɓantaccen Sabis Ɗin Intanet - (Personal Area Network (PAN))
Wannan
shi ne nau’in sabis na intanet da ya shafi wuri
guda kawai. Yawanci ana samar da shi ne domin amfanin mutum ɗaya. Sau da dama sabis ɗin ba ya wuce faɗin
mita goma (10). Misali, idan mutum ya tura bidiyo ko hoto daga kwamfuta zuwa
wayarsa ko daga waya zuwa kwamfuta, to ya yi amfani ne da irin wannan nau’in
sabis. Haka ma mutum na iya kunna sabis ɗin wayarsa na hawa intanet domin ya ba wa kwamfutoci ko wayoyi sabis.
Duk ire-iren waɗannan
ana kiran su da suna PAN.
2. Sabis Ɗin Ƙaramin Wuri - (Local
Area Network (LAN))
Wannan
nau’in sabis ne da ya shafi ma’aikatu ko gidaje ko
masana’antu. Za a iya samun ma’aikata mai kwamfutoci kamar guda goma (10) amma
dukkanninsu suna amfani da sabis guda ne. Bayan haka, ƙwaƙwalen kwamfutocin na iya
kasancewa a haɗe
wuri guda. Wannan zai sa duk sauyin da aka yi a kwamfuta guda ya kasance ya
shafi sauran kwamfutocin. Bayan haka, akan samu babban ofishi a ma’aikata da
yake ɗauke da kwamfutoci da
yawa a ciki. Ana iya tsara yadda dukkannin kwamfutocin za su riƙa tura takardun da za a
gurza (printing) zuwa na’urar
gurza takardu (printer) guda. Sabis ɗin da ya haɗa
kwamfutocin shi ake kira LAN. PAN daban-daban ne suke haɗuwa su ba da LAN.
3. Sabis
Ɗin Yanki - (Metropolitan Area Network (MAN))
Wannan
nau’in sabis ne da yake karaɗe wani yanki. Nau’in sabis ɗin da ake samu a manyan jami’o’i da suke da gine-gine da dama na iya
kasancewa MAN.
Bayan haka, ana iya samun wata ma’aikata da take da gine-gine ko ofisoshi a
wurare daban-daban a cikin gari guda ko garuruwa da suke kusa da juna. Idan
haka ta faru, ana iya amfani da sabis ɗin MAN domin taƙaita adadin kuɗi
da ma’aikatar za ta riƙa kashewa ga sabis. PAN daban-daban ne suke haɗuwea su ba da LAN. Su kuma LAN sai su haɗu su ba da MAN.
4. Sabis Na Dogon Zango - (Wide
Area Network (WAN))
Wannan
nau’in sabis ne da yake mamaye dogon zango. Yana kasancewa
tsakanin gari da gari ko ma ƙasa da ƙasa. Babban misali a nan shi ne, akwai bankunan da suke da cibiyoyi a
dukkan jahohin Nijeriya, inda kuma ake samun nau’o’in sabis-sabis da dukkannin
cibiyoyin da suke jahohin suke amfani da su a tare. Manyan kamfanonin fassara suna da tsari makamancin
wannan. Misalan wannan sun haɗa da kamfanonin fassara da suke da
ma’aikata da dama, waɗanda
kuma suke amfani da tsarin sabis guda. Ko a ɓangaren raba fayilolin fassara za a iya kallon wannan. Idan akwai
fayiloli 20, za su kasance a kwamfutocin dukkannin ma’aikatan. Sannan
kowannensu zai riƙa kallon fayil da aka riga aka yi aiki a kansa.[2] Yayin da PAN suka haɗu suka ba da LAN, su kuma LAN za su haɗu su ba da MAN. MAN kuwa su ne suke haɗuwa su ba da WAN.
A
Nijeriya, akwai kamfanoni da dama da suke samar da sabis ɗin intanet. Akintaro, (2023 SL. 4) ya bayyana cewa, zuwa watan Nuwambar shekarar 2023, Hukumar
Kula Da Harkokin Sadarwar a Nijeriya, wato Nigerian Communications
Commission (NCC) ta ba da lasisi a
kamfanonin da suke bayar da sabis ɗin intanet 253. Ya zayyano kamfanoni goma daga cikinsu waɗanda suka fi yawan adadin kwastomomi a Nijeriya. Su ne kamar
haka:
Jadawali Na 4: Kamfanonin Samar Da Sabis Ɗin Intanet Da Ƙiyasin Yawan Kwastomominsu
|
|
Kamfani |
Adadin
Rajista |
|
1. |
Spectranet
|
113,747 |
|
2. |
Tizeti |
19,126 |
|
3. |
IPNX
|
14,871 |
|
4. |
Starlink
|
11,207 |
|
5. |
VDT
Communications |
6,611 |
|
6. |
Cyberspace
Network Limited |
4,130 |
|
7. |
Ngcom
Limited |
3,956 |
|
8. |
Radical
Technology Network Ltd |
3,647 |
|
9. |
Suburban
Broadband Ltd |
3,627 |
|
10. |
Cobranet
Limited |
3,401 |
Madogara: Akintaro (2023)
[1] Domin
samun ƙarin bayani game da ayyukan da aka gudanar kan
sabis ɗin itanet,
ana iya duba Bourgeois (2016) ko Dordal (2020).
[2] Domin ƙarin bincike game da nau’o’in haɗakar sabis ɗin intanet, ana iya ziyartar https://www.javatpoint.com/types-of-computer-network ko https://www.router-switch.com/faq/types-of-networks.html ko https://www.belden.com/blogs/network-types ko kuma https://afteracademy.com/blog/What-are-the-different-types-of-network.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.