WANDA AKA GABATAR A KWALEJIN KOYON LARABCI DA ADDININ MUSULUNCI TA SHABAB DAKE UNGUWAR DOSA KADUNA. RANAR JUMA’A 1 GA FEBRAIRU 2013.
BALLAGAZAR UWA: TSAKURE
A KAN WASU DAGA CIKIN ƊABI’UN IYAYE MATA MASU
RA’AYIN KO-IN-KULA
DAGA
MU’AZU SA’ADU KUDAN
SHIMFIƊA:
Ma’anar Ballagaza:
Na nufin mace mara
kamun kai,da rashin kishin kai,da rashin natsuwa,kuma makwaɗaiciya. Haka kuma ana
iya cewa mai ƙarancin wayau,mara tsafta,kucaka ko ƙazama. Ana iya
kiranta da sauna ko sakarya,kosagalaɓa,ko samodara,amma dai suaanta na yanka shi
ne “Ballagaza Bankaura. ”
Hoton Ballagaza:
Da zarar ka yi kaciɓis da Ballagaza kana
iya ganeta,tun daga ɗaurin zani. Domin
Bahaushe yace,sakaryar mace tun daga ɗaurin zani ake ganeta,saboda idan ta tashi ɗaurawa ta ɗaura da dama. Daga
can ƙasa ta saki leɓen kishiya.
Kai ba kitso, ƙafa babu ƙunshi, Ga jirwaye a
sha-raɓa da ƙwauri.
Kaushi da ƙauje sun ɓata ƙafar ƙazama,fuska kuwa babu
mai ba koya (hoda) Babu su ja-gira a fuskar kucaka, Hannayenta ma babu wanki
Ba ta yanke farce
bare tai suwaki,kaga haƙoranta sun zube babu fiƙa.
Idan a cikin gida ka
hango ta duba,shi ɗaurin zanin ta ɗaura shi kandame (a ƙirji) ,Can a jima ya
koma ture (iyaka cinya). Kai Allah wadai da siffar ƙazama.
Ma’anar Uwa:
Duk macen ta ɗauki ciki na haihuwa
na tsawon watanni 7,ko 9,ko12,ta haifeshi. Wannan ita ce ake kira uwa ga abin
da ta haifa,yana iya kasancewa jariri (na miji) kojaririya (‘ya mace).
Faɗaɗa Ma’anar Uwa:
Baya ga
ma’anar uwa ta asali,sai Bahaushe kuma ya ɗauki Kalmar ya faɗaɗa ma’anarta. A inda
yake amfani ita ga wasu abubuwa da dama,kamar haka:
1. Uwar ɗaki (mutum ya samu wata mata wadda ta
girmeshi ya rinƙa girmamata. Ita kuma tana lura da shi,ko kyautata masa
da tausayi kamar yadda uwa kan yiwa ɗa).
2. Uwar goyo (matar da ta riƙe ko goya mutum tun
lokacin yayen daga shan nono,wasu kuma da ɗan girmansu. Wani riƙon kuma na tabanni
ne,mace ta ɗauko yaro,ko a tsinta
ta mai da shi ɗanta).
3. Uwargida (matar da
mai gida ya fara aura kafin amarya).
GABATARWA.
Da sunan Allah Mai
rahama Mai jinƙai, Mai kowa, Mai komai, Mai aikata abin da Ya so, ga
wanda Ya so, a sadda Ya so, a yadda Ya so, ko ana so ba a so dole bayi su so. Tsira
da amincin Allah su tabbata ga shugaban halittu Annabi Muhammadu, da Alayensa
da Sahabbansa.
Wannan muƙala zata ɗan taɓo, wasu daga cikin ɗabi’un iyaye mata waɗanda Bahaushe ke ƙyama ta kowace fuska.
Idan aka dube su ta mahanga al’ada sun saɓawa al’adun Bahaushe. Haka kuma idan aka dube
su ta mahanga addinin musulunci,nan ma sun saɓawa addinin. Domin sun yi ban-tafin
makafi da shari’ar musulunci,saboda ɗabi’un sun yamma,ita kuma shari’a ta yi gabas.
saboda haka babu inda suka haɗu. Idan kuma muka kalli waɗannan ɗabi’u a hankalce,sai muce sun saɓawa hankali. Wannan
muƙala
na nufin ta fito da wasu daga cikin ɗabi’un iyaye mata, tare da nuna irin nauyinsu
da matsayinsu a mizanin al’adar Bahaushe. Bisa dalilin ƙyamarsu da ake yi,tare
da gudun aikatasu ne ya sanya ake kallon mai yinsu shi ma ya zama abin ƙyama. Don haka duk
macen da ta kasance tana aikata irin waɗannan ɗabi’un,ita ma ta zama abin ƙyama ke nan ga
mijinta, da danginta,da abokan zama,kai da ma sauran al’umma baki ɗaya. In ban da
‘ya’yanta, ko su ma don ya zama dole.
Wannan shi ne
dalilina ko hujjata da suka sanya na kira muƙalar da suna ‘’Ballagazar
Uwa’’. Bayan haka wannan muƙala riga ce da babu
wuya duk wadda ta saya ta huda ta sanya, to ita ce ballagazar Uwa. Domin haka
zaɓI ya rage ga mai
shiga rijiya,ko dai ki zama uwa ta ƙwarai,son kowa ƙin wanda ya rasa. Ko
kuma ki zama ballagaza uwa ba a bin sha’awa ce ba.
1. Rashin kamun kai: Zan fara da halin
ballagaza na fari,watau rashin kamun kai. Duk matar da ta zama mara kamun
kai,ba ta da daraja a idon kowa. Kaɗan daga ɗabi’un mace mara kamun kai sun haɗa da : cin abinci
akan hanya,ko a kasuwa,ko kuma a cikin taron jama’a. Haka kuma takan kasance
mai yawan Magana tare da ɗaga murya. A kasuwa
kuma ta yi ta yin surutu da maza babu gaira babu dalili. Misali wajen ‘yan
tireda,da masu yari (ɗan kunni da sarƙa) da masu bulawus da
sauransu. Wata saboda rashin kamun kai, har dariya tare da ba a zaka ji suna yi
da wasu watsattsun maza wanda idan ba a yi sa’a ba, sai ɓarna ta auku.
Illolin Rashin Kamun
Kai:
Zubar da mutumcin
kai,da na ‘ya’ya,da na miji,wanda kan iya haifar da aukuwar ɓarna,misali kamar
kwartanci,ko fyaɗe, ko magannun banza.
2. Rashin natsuwa: Ɗabi’a mai bin wannan
ita ce rashin natsuwa, dukkan mace ana bukatar da ta kasance mai natsuwa a
al’amuranta gaba ɗaya. Matuƙar a ka ce ta rasa
natsuwa, to ta zama cikakkiyar ballagaza. Bisa hujjar cewa ana alaƙanta natsuwa da
hankali ne,rashin ta kuma ana dangantashi da hauka. Duk abin da mace zata yi
ana bukatar natsuwa tun daga Magana,ko tafiya,ko aikin girki,ko rainon yara ko
miji da sauransu. Mace ta ƙwarai kan yi Magana da mijinta cikin
natsuwa,babu hargowa. Haka kuma idan tana yin Magana da ‘ya’yanata takan yi
masu a natse ba hayaniya,don su ma su koya.
Tafiya: Game da tafiya mace
natsattsiya an so ta rinƙa yin tafiya cikin natsuwa ba faram-faram ko
bagazan-bagazanba. Akwai tafiyar da mace zata rinƙa yi wadda ta
dace,idan ta fito daga gida tafiyar natsuwa ake so. Idan kuwa a gida take to
rinƙa
yiwa mijinta yauƙI,tafiyar toron giwa (ƙasaita) don ta burge
shi kuma ta ɗaure abin ta a gida. Domin
idan ba ta yi ba,wata a waje ta yi masa ta ƙwace shi.
Aikin girki: Dangane da aikin
girki kuwa, shi ma ana son natsuwa. Domin dole sai in akwai natsuwa ne za a
samu abinci mai tsafta kuma mai daɗI, sannan kuma ayi shi akan kari (da wuri). Mace
mai yin daren tuwo ba ta da kwar jini,akwai wata Karin Magana mai cewa: “mai
daren tuwo kya ci da buzuzu”. Ya dace `mace ta iya girki,sannan kuma ta
koyawa ‘ya’yanta,don kar su yi aure ba su iya ba, daga a baya a zo a ji kunya.
Rainon ‘ya’ya da na
maigida: Dangane
da rainon ‘ya’ya da na maigida,ana iya cewa sai mai natsuwa kan iya yinsa cikin
ƙa’ida.
Tabbas mace natsuwa ce ke iya tattalin ‘ya’yanta da mijin ta. Dole ne ta kiyaye
ɗabi’un ‘ya’yanta masu
kyau da marasa kyau. To haka shi ma mai gida ya kamata ta kula da kyautata
masa, ta fuskar kwantar masa da hankali,lallashinsa a wajen Magana,shimfiɗa,da dukiyarsa, da
mutuncinsa. Mace mai dabara kan ɗaure mijinta kyakkyawar ɗabi’a. Tun daga
tsaftaceccen abinci mai daɗI, da kuma tsaftar jiki,da na muhalli. Kuma ta kasance
mai daddaɗar Magana cikin murya
tattausa,tare da shagwaɓa da narkewa.
Kyautata shimfiɗa: Kyautata shimfiɗa,a shimfiɗu kuma a shimfiɗar,ban da musu a
shimfiɗa. Haka kuma,ki kula
da abubuwa uku a game da shimfiɗa,kamar 1. kafi shayi (shimfiɗar bayan sallar asuba).
2. Yaushe gamo? (idan mai gida zai tafiya). 3. Yaushe rabo? (idan maigida ya
dawo tafiya). Bahaushe yace: “igiyar ido tafi ƙiri ɗauri” ma’ana idan
mace ta iya kallo,kuma ta yiwa mijinta to baya iya zuwa ko’ina (fari, ko ina
zuwa?,ko ya da carbi).
3. Ɗabi’ar kwaɗayi: Bayan wannan kuma,sai
ɗabi’ar kwaɗayi. Matuƙar a ka ce mace
makwaiɗiya ce,to haƙaƙa tana cikin haɗari. Domin Bahaushe
yace : “kwaɗayi mabuɗin wahala”ko “idan da
kwaɗayi da wulakanci” ko
“idan baki ya ci dole ido yai kunya”. Da sauran maganganu da dama masu nuna
illar kwaɗayi a rayuwa. To don
haka duk macen ked a kwaɗayi ballagaza
ce,saboda tana iya faɗawa haɗarin kwartanci. Kwaɗayi ya ƙunshi son abin duniya
(kuɗI da komatsan duniya)
,ko kuma son cin daɗI kamar nama,ko
kifi,ko kayan ƙwalam da maƙulashe. Yawan son
abin duniya ke sa mace karɓar kyauta,ko roƙo a inda bai dace ba.
An sha samun matan da aka yiwa kyauta daga baya abin ya zama fitina. Ko kuma
wasu matan a saboda tsire ko balangu ko kaza ko kuma atamfar anko, sai su bad a
kansu. Wasu kuma a saboda kuɗI,ko a wurin talla,sais u bad a kansu a ballagazar arha.
4. Rashin kishin kai:
A
game da rashin kishin kai kuwa,ana iya cewa shi ma wani hali ne na ballagazar
uwa. Duk inda a ka samu mace wadda ba ta san ƙimar da darajar janta
ba. To wannan it ace Ballagaza. Da farko dai ba ta da kishin kanta,ba ta kishin
miji,sannan ba ta kishin ‘yarta. Tura ‘ya talla rashin kishi ne,kuma yana yin ɓarna ba kaɗan ba.
Kishi a rashin kishi:
kishin
banza (kishin mai dadaro). A inda take ƙyamar mijinta ya ƙara aure, amma kuma
yana da farka a waje. Ta ƙi zama da kishiya, amma ƙawar Alhaji ko
Amimiyarsa ko abokiyar aiki za ta zo gidan,kuma ta karɓe ta hannu bibiyu. Duk
ɓarnar da miji zai yi
indai ba maganar kishiya to daidai ne.
Bisa la’akari da
bayanan da suka gabata. Kai tsaye muna iya cewa,duk macen da ta kasance da ɗaya daga cikin waɗannan ɗabi’u da aka lissafa.
To ta zama mara wayau,kuma ba ta da tsafta, kuma ta zama ƙazama. Ta zama
Ballagaza komai ilminta,komai barikinta, tana yin ɗigirgire ko kan-tafi
da rayuwarta.
Bisa wannan dalili
ya zama wajibi ga dukkan namiji ya ɗauki
matakin riga-kafi. Babban riga-kafin kuwa shi ne,zaɓarwa ‘ya’yansa uwa ta gari tun kafin yin aure. Dole ne ya
yi taka tsantsan,ya yi kaffa-kaffa wajen neman matar da zai aura.
ZAƁARWA 'YA'YA UWA TA GARI.
Wajibi ne ga dukkan mahaluki mai hankali da yayi niyyar
yin aure, to ya yi ƙoƙarin zaɓarwa 'ya'yansa
uwa ta gari, ma'ana mai tarbiyya da son addini. Kar ya bi son zucEiya ya auro
mace don kyau, watau kyakkyawa, ko 'yar wane, watau mai nasaba (mai kuɗi, sarauta, muƙami). Wannan magana ta yi dai-dai da wani bayani da
Manzon Allah (S. A. W) ya yi cewa ku auri mace ma'abuciyar Addini. Domin yace
in ka yi aure don kyau, to lallai kyau kan ƙare in ta tsufa, ko nasaba don mulki na iya ƙarewa, amma shi Addini ba ya ƙarewa.
Bayan haka, zaɓarwa 'ya'ya uwa ta gari kamar hutar da kai ne, domin in
ka haifi yara da mace ta ƙwarai, to kamar
ita ce makarantar su don zasu koyi komai na ƙwarai daga wurinta. Saboda masu hikima sun ce uwa ita ce
makarantar farko ga yaro. Haka kuma in mutum ya kuskure ya auri Ballagazar mace
mara tarbiya, to ya kashe kansa da kansa, kuma yaransa sun shiga uku. Babban
dalili shi ne, ita ba ta da tarbiya, ba ilimi balle addini, to a nan ina
makarantar farko take? Sai dai su koyi zagi da miyagun halaye.
MATSAYIN
UWA:
Matsayin
uwa ga ɗan da ta haifa ba ƙarami ba ne, saboda
kuwa wannan matsayi, Allah (S. W. T) Mahaliccinmu ne ya ba ta shi. Wani abin
lura shi ne, tun daga ranar da miji ya kwanta da matarsa suka sadu, Allah (S. W.
T) Ke nuna ikonsa watau in aka samu shigar ciki. Tun daga wannan rana ta dinga
gwagwarmaya da wannan ciki tun yana ɗigon maniyyi kwana arba'in (40) , ya koma
gudan jini kwana arba'in (40) , ya koma gudan tsoka kwana arba'in (40) , sannan
ya zama ɗan tayi ke nan, daga
nan har halittunsa su haɗu, duk wannan
al'amari na faruwa ne, a cikin jakar mahaifa a cikin uwa.
Wannan rayuwa da jariri kan yi a cikin duhun
jakar mahaifa a cikin uwa ya gudana ne kamar haka: -
1. Da farko dai yana samun abincinsa ne ta
hanyar cibiyarsa da take haɗe da wasu hanyoyin jini, a wannan hali ne duk irin
abincin da uwar da ta ci, to shi ma tayin (ɗan jinjiri) zai samu ta hanyar cibiyarsa da
jijiyoyin jini kan ɗauko.
2. Na
biyu shi ne jini na yawo ne watau zagaya jikin ɗan Adam ne tare da taimakon aikin
zuciya, ma'ana bugun zuciya, shi wannan bugawa da zuciya take yi kan aika da
jini a dukkan sassan jiki gaba ɗaya, wanda kuwa ya haɗa har da ciki inda ɗan tayin jariri yake
kwance ko ɗan tare da mahaifa.
Wannan kaiwa da komowa da jini ke yi, tare da
taimakon bugawa da zuciya kan yi, yana gudana ne har tsawon lokacin da jariri
ya ɗauka ya saba kuma bai
san wani bugun zuciya na daban ba, sai wannan watau na uwarsa.
Babban dalilin da yasa yaro kan gane
mahaifiyarsa bayan an haife shi. Akwai wani bayani da wani malami ya yi kamar
haka: -
“Jariri yakan gane ko bambance bugun zuciyar
uwarsa da na wata mace daban, wannan ya haifar da zarar jariri na kuka alhali
yana hannun wata da ba uwarsa ba, matuƙar uwarsa ta karɓeshi ta kifa shi a ƙirjin ta zai ji bugun
zuciyar ta wanda ya riga ya saba, to da ya ji sai ya yi shiru.
DANGANTAKAR YARO DA IYAYE DA GADO
Akwai wata dangantaka a tsakanin yaro da
iyaye, baya ga haihuwa da raino da tarbiyarsa. Wannan dangantaka kuwa ita ce ta
fuskar gadon wasu halayensu ko ɗabi'un su, ko cututtuka. Ana gadon wasu halaye ko ɗabi'un iyaye, wannan
kuwa ba Bahaushe kaɗai ba har da masu
ilimin kimiyya (scientist, Behavioral Sciences) ,
sun tabbatar da wannan. Sukan kira shi da turanci “heredity”. A al'adar
Bahaushe ana hasashen cewa lallai yaro kan gaji jin kunya, haƙuri, natsuwa, basira
daga iyaye, haka kuma yaro kan gaji rashin kunya, da saurin fushi, da faɗa,da hargagi da daƙiƙanci. Ban da wannan
kuma a kan gaji sata, kyauta, rowa da sauransu.
Bayan wannan kuma akwai wasu cututtuka da akan
gada daga iyaye musamman uwa. kamar hauka, amosani, jini (sicler) , kuturta,
hawan jini, ciwon suga da sauransu. Yaro kan gaji wasu cututtuka daga iyayensa,
a wani lokaci ma har daga kakanni ko dai daga wani a zuriya.
Baya ga wannan kuma sai wani gado da yake ba
sabun ba, Duk da yake ana samunsa, kamar wajen inda jika na wajen 'ya mace kan
gaji kaka na wajen uwa, kamar sarauta ko jagoranci, roƙo, ilimi. Domin a kan
samu wani yaron da kan nuna alamar jagoranci ta fuskar yadda yara ke binsa ko a
wajen wasa, wasu ya kan ɗore har girma, inda
za ka bincika sai ka iske akwai wani kakansa wanda ya taɓa yin jagoranci ko
sarauta.
Haka kuma yaro kan gaji roƙo ta wajen kakansa
akan samu wasu suna zama maroƙa ko mawaƙa. To, amma da za a
bincika sai a iske ya gaji roƙo ta wajen kakansa ɓangaren uwa.
Dangane da ilimi kuwa, akwai wasu da yawa zaka
iske sun zama malama, amma da za a bincika, sai a iske iyayensu basu yi ba,
amma kakansu na wajen uwa ya yi.
Bugu da ƙari, wasu daga cikin
Hausawa na yin aure ne ta hanyar binciken zuriyar da mata ta fito, shi ya sa ma
ake cewa: “mai son miya ya auri tsohuwa” mai son shimfiɗa ya auri budurwa”
“mai son ɗan ƙwarai ya auri isassa”
kowa ya auri sakarai yana da takaici”. Sau da yawa a kan samu saɓani tsakanin iyaye da
'ya'yansu a lokacin aure, saboda su iyaye suna da tarihi na zuriyar, ko sun san
asalin iyayen yarinyar, shi kuwa bai sani ba. To a ƙarshe dai abin da
iyayen ke gudu, shi ne, irin wancan gado. To, amma kuma in kyakkyawan hali ne,
sai ka ga har ƙoƙarin haɗa aure ake da zuriyar su wane. A irin wannan hali ne
Bahaushe kan ce: “ai wane ya sha a mama ko ya tsotsa a mama”. Ma’ana ya gaji
uwarsa. Akwai karin maganganu da dama da suka tabbatar da wannan tunani kamar
haka: -
i. Harbi
ga ɗan jaki gado.
ii. Barewa
tai gudu ɗan yai rarrafe?.
iii. Haifi
ka ga kamarka.
iv. Duk
faɗin gida magajinsa ɗaya.
v. Mai
son ɗan ƙwarai ya auri isassa.
Shi kuwa Malam Aliyu Namangi Zariya a wata rubutacciyar waƙa mai suna waƙar ƙazama cewa ya yi: -
WAƘAR ƘAZAMA
1- Ya Allah Rabbana taimake mu,
Mu gargaɗI ‘ya uwa ga auren ƙazama.
2- Auren tsohuwa hasara ga yaro,
Gwammaci tsohuwa da auren ƙazama.
3- In ba ka son tan e ba kau tambaye ni,
In Allah Ya yarda ka san ƙazama.
4- Mummunan halin ƙazama na fari,
Ba ta face miji na sai da dama.
5- Mai son cin tuwonta sai ya ci gashi,
Susan kai hagu na tofi da dama.
6- Hanci majina idanunta kwantsa,
Dattsa ya daɗa wa bakin ta girma.
7- Sai ka ga tai jagal da suma da dauɗa,
Ga bauli a kwance tashin ta fama.
8- Ba mai son kitso bat a kasa aski,
Taba ya dafe haƙoran ƙazama.
9- Gude ba ƙoƙari baga kasa girki,
Ga haɗama a zuci ƙoshin ta fama.
10- Ran girkinki ba a ƙoshi da jiɓi,
Shi naman miji ki cinye shi a tsama.
11- In ta ga ka fito kamar za ka azure,
Sai sababi ya tashin don ɓata girma.
12- Kaji, bar neman fita ina tsame nama,
Yau dai kai rabon a zage ka kaima.
13- Tun da ka sai kitse ya narke a girki,
In aka zo rabo rabawarsa fama.
14- Wanda ka bashi ƙanƙana sai y arena,
Kowa so shike shi karɓa da girma.
15- Ran nan ma ka sai ƙashi na ci zagi,
Gun ƙwarin gidanka mai ya da girma.
16- In tace da ni ƙazama in rama,
Wanda ya san kumatu ya san ƙazama.
17- In tace ina ci ne in rama,
Domin ga tasalla ƙoshin ta fama.
18- Kwana goma jeer haifanta goma,
Ba taran miji ga haifan ƙazama.
19- Ita ko bante ta ƙetare sai ta haihu,
In ka san kuɗI su ƙare a suna.
20- Ya Alah daɗa wa matanmu tsabta,
Ka da Allah ka ba mu mata ƙazama.
21- Tun da mijin ƙazamiya zai ji kunya,
Can aljanah babu mata ƙazama.
HAƊARIN TALLA GA ‘YA MACE
Haɗari na nufin mummunan sakamako
da zai iya biyo bayan aikata wani aiki. Ko wane mugun matsayi da za a iya faɗawa a dalilin aikata wani aiki bayan ko ana cikin yinsa.
Talla kuma na nufin a ɗauki abin sayarwa don a zagaya ko kuma a zauna ana yin bayani abin da ake
sayarwa saboda a jawo hankalin mai buƙata saboda ya saya.
Dangane da haɗarin talla ga ‘ya mace, ana iya cewa abubuwan da yarinya ke iya gamuwa ko
faɗawa cikinsu ba tare da ta so ba, ko ba ta so ba. Babban
haɗarin talla ga ‘ya mace shi ne faɗawa fasiƙanci, watau zina. A wasu lokutta ko da yarinya
kamammiya ce wata u ta na da tarbiya to da zarar ta fara talla, sai abokan
tallar watau ƙawayenta sun gurɓata mata tarbiya ta hanyoyi daban daban. Ko kuma mazaje da sukan kira ta
don sayen abin sayarwa, wasu ba da zuciya ɗaya suke saye ba. Akwai masu kiranta kamar za su saya sai su fara yi mata
zancen banza, tun tana ƙyama sai ka ga yau da kullum ta
fara sabawa har saiske tana kokuwa da maza ba kunya ba tsoron Allah.
Bayan wannan, yarinya kan koyi rashin kunya a
inda za ta koyi miyagun maganganu, ciye-ciye a titi, kokaye-kokaye, zage-zage
da sauransu.
Waɗannan bayanai da suka gabata ba
a ɓoye suke ba, a sarari suke domin kuma ‘yan matan
da suka yi cikin shege a wuraren talla ba za su ƙirgu ba. Wasu yaran kuma sun ɓace gaba ɗaya har abada an rasa su.
Bugu da ƙari, shi dai tallan nan a wasu a kan yi shi ne don a yi wa yarinya kayan ɗaki watau danki, wanda wani lokaci kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Domin ribar da ake samu a wurin talla ba ta taka kara ta karya
ba. In aka tattara jarin watau uwar kuɗin da ita ribar sai a iske basu
kwaranye abin da ake buƙata, kamar tallan goro, gyaɗa, ƙosai, tuwo da sauransu.
Bayan haka, a sanadiyyar tallar nan yarinya kan
yi asara goma da goma domin kuwa ta kan yi asarar karatun addini da na zamani (boko).
Kai a bar ma maganar ilimi hatta tarbiyya da bgirki mai talla kan yi asararsu. Ta
fuskar ibada nan ma a kan yi asararsa kamar sallar azahar, la’asar, magriba da
isha’i, don kuwa an shagala da talla ba za a damu da an gaji ba a maganar
ramuwar sallar. Talla kan yi illa ga wasu yaran ba a sani wani lokaci sai ciwo ya ci ƙarfinsu sannan ake ganewa, wasu kuma a wurin
tallar suke ɗaukar cutar, wasu a wurin tallar suke gamuwa da
iskoki (aljanu).
To Jama’a ina mafita?:
Tun da mun riga mun ji ɗabi’u da siffofin ballagazar uwa. ashe ya zama wajibi mu tambayi kanmu ni,da
kai,da shi. Bisa abin da ya dace mai hankali ya yi,domin kar mu faɗa rami. Mun dai ji matsayin uwa ga ‘ya’yanta,tun daga wajen gado,da koya
tarbiya da sauran al’amura na yau da kullum. Ke kuma mace wajibi ne ki kula
tare da kiyaye waɗannan ɗabi’un, don ki kare kanki,da
‘ya’yanki,har da mijinki daga ɓata suna ko halaka.
KAMMALAWA;
A ƙarshe wannan muƙala ta ɗan taɓo, wasu daga cikin ɗabi’un iyaye mata. Tabbas
su ne waɗanda Bahaushe ke
kyama ta kowace fuska. Idan aka dubesu ta mahanga al’ada,da addinin
musulunci,da kuma a hankalce sun saɓawa al’adu,da addinin Bahaushe. Idan kuma
muka kalli waɗannan ɗabi’u,sai muce sun saɓawa hankali. Wannan
muƙala
ta fito da wasu kaɗan daga cikin ɗabi’un ne, tare da
nuna irin muninsu,da nauyinsu da matsayinsu a mizanin al’adar Bahaushe. Bisa
dalilin ƙyamarsu da ake yi,tare da gudun aikatasu ne ya sanya ake
kallon mai yinsu shi ma ya zama abin ƙyama. Don haka duk
macen da ta kasance tana aikata irin waɗannan ɗabi’un,ita ma ta zama abin ƙyama ke nan ga
mijinta, da danginta,da abokan zama,kai da ma sauran al’umma baki ɗaya. In ban da
‘ya’yanta, ko su ma don ya zama dole.
Mun
riga mun ji irin illolin da waɗannan ɗabi’u suka yi,ko zasu yi mana, ta fuskoki marasa iyaka,
kuma ta kusurwoyi daban daban. Domin haka,ina fatan wannan muƙala, ta zama kamar
matashiya ce ga masu hankali daga cikinmu maza da mata. Allah Ya tsare mu Ya
bamu ikon gyarawa amin. Assalamu alaikum.
MANAZARTA
Ladan Y. (1980) Zaman
Duniya iyawa ne. Northern Nigeria Publication
Company Zaria.
Maryam S. L. (1993) Kishi
kumallon mata Bushara Publication House, Gusau.
Madauci I. (1963) Al'adun
Hausawa Northern Nigeria Publication Company, Zaria.
Sadiya G. Y. (2005) Talauci
Hauka ne? Super Print Press. Kano.
Saulawa I. (2000) Jagorar
fahimtar tavin Hankali. Katsina
Printing Presss.
Zindani A. A. (2000) Human
Development Muslim World League Printing Press Makka. Saudi Arabia.
Yunus I. (2005) Wa'azi
a Muhadara, Masallacin Jumu'a na
Kinkinau,Kaduna.
Zainab M. K. (2008) Hira
da ita a gidanta No. 1 Ƙofar Fada Kudan.
Stone & Cozon (1985)
New Biology for Secondary School
Amina M. S (2009) Kallabi.
Jaridar Leadership Hausa.
21/5/2009.
Umma U. S. (2008) Don
Iyali. Jaridar Nasara,20/10/2008.
Bello M. (2009) Kiwon
lafiya. Jaridar gaskiya tafi Kwabo.
26/3/2009.
Safiya J. (2006) Himma
dai mata. Jaridar gaskiya ta fi Kwabo.
20/4/2006.
Brown. l. J. (1975)
The Evolution of Behavior,printed in the United State of America.
Choge
B. (1990) Waƙar Sakarai ba ta da wayau. Ballagaza bankaura.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.