An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
Intanet ya samu ne a shekara ta 1983. Samuwar
kafafen intanet ya zo da wani juyin-juya-hali a kusan dukkanin al’amuran
duniya. Sauye-sauyen sun shafi Hausa da Hausawa ta fuskoki daban-daban. Tuni
duniya ta karkata kan amfani da intanet domin gudanar da al’amuran yau da
kullum. Daga ciki kuwa har da abubuwan da suka shafi:
a. Addini
b. Ilimi
c. Kiwon lafiya
d. Shugabanci
e. Siyasa
f. Tattalin arziki
Tafiya ta yi tafiya inda duniyar intanet ta
kasance wata duniya ta daban da take buƙatar wakilcin Hausa da
Hausawa. Harkokin tattalin arziki masu yawa da suka shafi biɗa da tanadi sun
koma kan intanet. Abin har ya kai ga an samu kasuwanni daban-daban a kan
intanet waɗanda Hausawa suka fara shiga ana damawa da su. A cikinsu ana
hadahadar saye da sayarwa tamkar yadda ake yi a duniyar zahiri. Wannan kuwa ya
shafi har da hadahadar kuɗaɗen intanet.
A ɓangare ɗaya kuwa, an samu sauye-sauye ta
fuskar ƙwadago a duniya. Shigowar intanet ya buɗe ƙofar gudanar da ayyukan ƙwadago masu yawa a kan intanet. Nau’o’in ƙwadagon da ake gudanarwa a duniyar intanet waɗanda suka
shafi Hausawa sun haɗa da:
a. Baje haja/koli
b. Bincike
c. Dillanci
d. Gyaran hotuna da na’urori
e. Hadahdar kuɗaɗe da
kadarorin intanet
f. Intanet da na’urori
g. Kimiyyar harshe
h. Tallace-tallace
Duk waɗannan sun samar da wani sabon babi
tare da kafa ayar tambaya game da alƙiblar kasuwanci a duniya.
Dole ne Hausawa su yi la’akari da alƙiblar kasuwancin duniya
domin su ma su taka kyakkyawar rawan kiɗan zamani. Wani abin da ya kamata a
mayar da hankali kansa kuma shi ne, da dama daga cikin ayyukan ƙwadagon kan intanet suna da alaƙa da al’ada. Misali ayyukan da suka shafi kimiyyar harshe
kamar fassara da fassaran kan sikirin, duk suna da alaƙa ta kai tsaye da al’ada. Haka abin yake dangane da
tsarawa da gyaran bidiyoyi da hotuna, ko kuma ɗora ƙunshiya (content) a kan kafafen intanet a matsayin hanyar
neman kuɗi. A taƙaice ke nan, al’amari ne wanda yake buƙatar Hausawa su shiga ciki a dama da su domin bayar da
kyakkyawan wakilci ga al’adu da harshe da adabinsu.
Wannan littafi ya yi nazari tare da kawo
bayanai dangane da damarmakin da Hausawa suke da shi waɗanda suka shafi biɗa da
tanadi a duniyar intanet. An raba littafin zuwa babuka shida (6). Babi na farko
ya kasance shimfiɗa. A cikinsa an yi waiwayen harkokin da suka shafi biɗa da
tanadi na Hausa na gargajiya. An tattauna ma’anoninsu da ƙunshiyarsu. Bayan haka, an duba biɗa da tanadi na Hausawa
a zamanance.
Babi na biyu kuwa ya mayar da hankali kan
muhimman batutuwa da suka shafi neman kuɗi. Sun haɗa da sana’o’i da kasuwanci
da fatauci da sauran lamuran Hausawa masu alaƙa da tattalin arziki da suka gada kaka da kakanni. Daga
nan kuma babin ya duba sana’o’i da kasuwancin Hausawa a zamanance – wato
sauye-sauye da aka samu a sakamakon tasirin zamani.
Babi
na uku yana ƙunshe da bayanai game da intanet. Ya fara tun
daga kan ma’anar intanet har zuwa tarihin samuwa da bunƙasarsa. Bugu da ƙari, ya kawo bayanai game
da tasirin intanet a kan Hausa da Hausawa. A ɓangare guda kuwa, babin ya yi
tsokaci game da tasirin su Hausawa a kan intanet.
Babi
na huɗu ya mayar da hankali kan hanyoyin neman kuɗi a kan intanet. Kai tsaye an
dubi damarmaki daban-daban na ayyukan samun kuɗi waɗanda Hausawa za su iya
shiga a dama da su. Sun haɗa da ayyukan ƙwadago a kan intanet da
tallace-tallace da dillanci da sauran ayyuka da suka shafi kimiyyar harshe ko
kwamfuta da na’urori.
Babi
na biyar kuwa ya kawo bayanai game da hanyoyin tanadi masu alaƙa da intanet. Wannan ya shafi yadda ake adana kuɗi a
akawun na bankuna da lalitocin kan intanet. Haka kuma, ya haɗa da adana kuɗaɗe
ko kadarorin intanet ko kuma kuɗaɗen ƙasashen waje.
Babi na shida shi ne na ƙarshe a littafin. Ya kawo bayanai game da matakan naƙaltar biɗa da tanadi a duniyar intanet. A cikin babin, an kawo bayanai dangane da abubuwan da ake buƙata domin samun nasarar neman kuɗi a kan intanet. Sun haɗa da ilimin kwamfuta da ƙwarewa a ɓangaren da aka ɗauka da tanadar na’ura da dai sauran abubuwa da ake buƙata. Bugu da ƙari, an kawo bayanai game da tagomashin biɗa da tanadi a duniyar intanet, wato jerin alfanu da ke tattare da ayyukan neman kuɗi ko tanadi masu alaƙa da intanet. Bayan wannan, babin ya kawo bayanai game da ƙalubale da matsalolin da suke tattare da ayyukan neman kuɗi da tanadi a kan intanet.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.