Ticker

6/recent/ticker-posts

Ka’idojin Bayar Da Magani Da Karbarsa

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Ƙa’idojin Bayar Da Magani Da Karɓarsa

Kalmar ƙa’ida Balarabiyar ce da aka samo daga Larabci, wadda Larabawa suke kira da suna ƙa’idatun. Ana kuma taƙaita ta zuwa ƙa’ida a harshen Larabcin. Ta hanyar taƙaitawar ce Hausawa suke amfani da kalmar. Kalmar ƙa’ida (ƙaa’idaa) tana cikin jerin sunayen kalmomin Hausa jinsin mata, jam’i kuwa ya kasance ƙa’idoji . Kalmar tana ɗauke da ma’anoni daban-daban da suka haɗa da:

a.  Doka – Wannan kalmar tana nufin umurnin hukuma, jam’i kuwa a ce dookooki.

b.  Iyaka – Marabar wani abu da wani abu

c.  Tsari – Daidaitawar abubuwa ko kuma shiryuwarsu

d.  Kyakkyawar ɗabi’a

Idan aka yi la’akari da waɗannan ma’anonin, a wannan fagen za a iya cewa, ƙa’ida tana nufin yadda aka shata ko tsara bayar da magani da karɓar sa bisa tsari na musamman.

Kula da mai ciwo ta hanyar ba shi taimako da magani, lamari ne da yake buƙatar ilimin magunguna da na yanayin cututtukan ɗan’adam tare da kyakkyawar ƙwarewa. Rashin sanin makamar cuta tare da jahiltar magani sukan haifar da babbar illa ga maras lafiya fiye da cutar da take addabar sa. Sakamakon haka yakan haifar da salwantar rayuwar marasa lafiya.

Akan samu wasu jinsin mutane da suke da’awar mallakar ilimin magunguna, har sukan yi kasadar bayar da shi, - alhali kuwa sun jahilci lamarin. Ganin irin yadda waɗansu mayaudaran mutane suke cutar da al’umma ne ya sa shari’ar Musulunci ta shata dokoki domin tabbatar da kariya ga rayuwa da lafiya da kuma dukiyar al’umma. Masu irin wannan yaudara sukan yi ne domin tara abin duniya kawai ta hanyar zalunci. A bisa haka ne ma ake da fitacciyar ƙa’ida da take cewa:

مَنْ تَطَبَّبَ وَلَيْسَ لَهُ عِلْمٌ، فَهُوَ ضَامِنٌ

Man taabbaba wa laysa lahū 'ilm, fa-huwa āmin.

Fassara

Duk wanda ya yi aikin likitanci alhali ba shi da ilimin fannin, to yana da alhakin (abin da ya lalata)."

Tsokaci: An kawo wannan a cikin Al-Majmu' Sharh al-Muhadhdhab (Imam Nawawi), Juzu'i na 6, Shafi 10. An kuma kawo shi a cikin Al-Muwatta' (Imam Malik) Kitab al-'Aql, a ƙarkashin hadisi mai lamba 2328 (a matsayin ƙa'idar fiƙihu).

A wannan ƙa’ida ta fiƙihu za a fahimci cewa, duk wanda ya jahilci aikin bayar da maganin gargajiya ko na zamani, ya kuma yi kasadar bayar da maganin, zai ɗauki alhakin sakamakon abin da hannayensa suka aikata. Dalili kuwa shi ne, sun gudanar da aikin da ba su mallaki iliminsa ko kuma ba su ƙware a kansa ba, har suka haifar da illa (lahani) ga al’umma, waɗanda suka cutar ta hanyar yaudara.

Duk jahilin da ya yi kasadar ba da magani, shi zai ɗauki nauyin aikinsa da ya aiwatar ga lafiya ko kuma rayuwar al’umma, a haɗuwar malamai. Abin nufi a nan shi ne, idan majinyaci ya mutu a sakamakon aikin jahilin mai ba da magani na gargajiya ko na zamani ko wanda bai ƙware ba, biyan diyya ya wajaba a kansa ko hukumar da ta ba shi izinin gudanar da aikin.

Idan ƙwararren masanin magani ya ba marasa lafiya magani, yana cikin halinsa na sani, sai maganin ya wanzar da wata illa, a nan shi ma zai biya diyya. Dalili shi ne bai tsaya ya yi ƙwaƙƙwaran bincike da nazari kafin ya bayar da maganin ba.

Yayin da maras lafiya ya gabatar da kansa ga wanda ya san shi ba masanin magani ba ne domin ya magance masa wata cuta da take addabarsa, idan har wata illar ta auku gare shi, to babu wata diyya da za a ba shi. Dalilin hakan shi ne, shi da kansa ya taimaka wajen halaka kansa.

Idan kuwa ƙwararren masanin magani, likita ne ko na gargajiya ne wanda ya mallakin izinin gudanar da aikinsa, ya je wurin ƙoƙarin magance wata rashin lafiyar wani ɓangaren jiki, sai ya haddasa wata illa ga wani sashe na daban a sakamakon kuskure; a irin wannan yanayi za a biya diyya ga maras lafiya. Kodayake akwai ra’ayoyi guda biyu na biyan diyyar. Idan mai bayar da maganin ba Musulmi ba ne, zai biya daga cikin aljihunsa. Idan musulmi ne, za a biya diyyar daga aljihun baitil malin Musulmi (Abuai-Rub, 2003 sh. 125). 

Post a Comment

0 Comments