Ticker

6/recent/ticker-posts

Hausawa Da Gwagwarmayar Bida a Duniyar Intanet

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

Hausawa Da Gwagwarmayar Biɗa a Duniyar Intanet

4.0 Shimfiɗa

Kamar yadda aka kawo a babi na biyu, Hausawa sun biyo matakai daban-daban dangane da biɗa da tanadinsu. Sauyin zamani ya riƙa samar da sauye-sauye a harkokin da suka shafin tattalin arzikinsu. Sannu a hankali har abin ya kai duniyar intanet a yau. Farfajiyar duniyar intanet kuwa tana da matuƙar faɗi. Nau’o’in kasuwanci da sana’o’in da ake gudanarwa a cikinta suna da yawa. A intanet za a iya samun makamantan duk waɗansu hadahadar kasuwanci da ake gudanarwa a duniyar zahiri.

Intanet ya kasance hanyar samun kuɗi ga mutane da dama. Wannan yana faruwa ne ta manyan hanyoyi guda biyu kamar haka:

a. Gudanar da wata sana’a ko kasuwanci a kan intanet domin samun kuɗi

b. Amfani da intanet domin inganta ko bunƙasa kasuwanci ko kuma sana’ar da aka saba gudanarwa

Wannan babin ya mayar da hankali kan fito da nau’o’i da yanaye-yanayen biɗa na Hausawa waɗanda suka shafi duniyar intanet. Bugu da ƙari, ya mayar da hankali wajen yin ƙarin haske game da damarmakin da Hausawa suke da su a ɓangarori masu yawa na kasuwancin duniyar intanet. An kawo hanyoyi daban-daban na samun kuɗi ga Hausawa a duniyar intanet. An bibiya tare da nazartar kafafen intanet domin sake fahimtar damarmakin da Hausawa suke da su na neman kuɗi ta hanyar dijital. Haka kuma, an tattauna da wasu Hausawa waɗanda suka rungumi ƙwadagon kan intanet a matsayin hanyar dogaro da kai tare da fita daga taskun talauci.[1]

4.1 Ƙwadago a Kan Intanet (Online Freelancing)

Wannan littafin ya fassara kalmar ‘freelancing’ da ‘ƙwadago’ a Hausa. Kalmar ƙwadago ba baƙuwa ba ce ga Hausawa. Ko bayan amfani da ita a maganar yau da kullum, kalmar ta ratsa rubuce-rubucen Hausa masu tarin yawa. Manazarta da dama sun yi ƙoƙarin bayyana ma’anarta. A ma’ana ta ƙamusu, Sa’id et al. (2006 sh. 289) an bayyana ƙwadago da cewa shi ne “... yi wa wani aiki don ya biya kuɗi, musamman aikin gona.” A fahimtar wannan ma’ana, duk wani aikin da za a aikata, sannan wanda aka yi wa aikin ya biya kuɗi, to sunansa ƙwadago. Wannan ma’anar ta yi daidai da wadda Umar (1983 sh. 5-6) ya bayar, a inda ya ce ƙwadago “wani salo ne na sanya mutum ya yi aiki a biya shi.”

Ma’anar da Yahaya (2023 sh. 93-94) ya bayar ta bambanta da waɗannan, musamman a wurin da ya nuna cewa ƙwadago ya keɓanta ne ga maza kawai. A fahimtarsa, kalmar ƙwadago tana da ma’ana ɗaya da ta lebura. Ya kuma nuna cewa sana’a ce da ta jiɓinci maza zalla wajen aiwatar da ita domin ana amfani da ƙarfi ne yayin gudanar da ita. Ta haka ne kuma Hausawa suke kallon dukkanin wani mutum wanda yake yin wahala tare da nuna ƙarfi a matsayin ɗan ƙwadago ko lebura. Bugu da ƙari, Hausawa sukan kira aikin da sunan ƙwadago ko ga-aiki ko leburanci.

Ra’ayin Yahaya (2023) bai kai ya kore sauran ra’ayoyin ba. Dalili kuwa shi ne, ko bayan ma’anar da Umar (1983) ya bayar, akwai waɗanda suka bayar da ma’anoni makamantan nasa. Sun haɗa da Kabakawa (2012 sh. 41) inda ya bayyana cewa:

Kusan kowane irin aiki mutum zai yi don a ba shi ladarsa ƙwadago ne, amma duk da haka, ma’anar aikatau ko ƙwadago ta fi ƙarfi a kan aikin da bai wuce na yini ɗaya ba. Saboda haka an fi samun ‘yan ƙwadago daga cikin matafiya, kamar almajirai da ‘yan-cirani da ‘yan kakkaɓar raɓa, su ne kan kewaye gari suna neman aikin da za su yi a rana a biya su.

Za a iya lura da cewa, wannan ma’anar ta jaddada batun cewa ƙwadago yana nufin aikin da mutum zai yi a biya shi. Nuhu (2020 sh. 198) ya bayar da ma’ana makamanciyar wannan. Ya nuna cewa, ƙwadago yana nufin “yi wa wani aiki domin biyan kuɗi.”

Lura da dukkannin waɗannan ma’anoni da aka bayar, ana iya cewa ƙwadago nau’in aiki ne inda ma’aikacin ba shi da takamaimai albashi da ranakun aiki ko yarjejeniyar aiki ta dindindin da wani kamfani ko ma’aikata. A maimakon haka, yakan gudanar da ayyuka ne ga waɗanda suka buƙaci ya yi musu aiki sannan a wuraren da aka buƙaci ya yi. Lura da waɗannan bayanai, kalmar ‘ƙwadago’ ta dace da fassarar ‘freelancing.’ Ma’anonin ƙamusu da na manazarta da dama sun kawo ma’anar kalmar freelancing a matsayin ‘aikin cin gashin kai’ wato dai aikin da mutum yake zaman kansa. Akan biya shi duk aikin da ya kammala a maimakon tsarin albashi.[2]

Shigowar intanet ya samar da sauye-sauye a harkar ƙwadago. A yau abin yana kasancewa ta manyan fuskoki guda uku, kamar haka:

i. Ƙwadagon da ake nemo ɗan ƙwadago a kan intanet, a ba shi aiki a kan intanet, ya kammala shi a kan intanet, sannan a amfana da sakamakon aikin yayin da yake kan intanet. A irin wannan nau’in ƙwadago, babu buƙatar mai bayar da aiki ya ga ɗan ƙwadago ko ya ji muryarsa. Bugu da ƙari, aikin da za a gudanar kacokan a kan intanet ake aiwatar da shi. Haka kuma, sakamakon aikin abu ne da zai kasance a kan intanet, ba wanda za a sauke shi ƙasa zuwa duniyar zahiri kafin a amfana da shi ba. Misalan nau’o’in ƙwadagon kan intanet da suke ƙarƙashin wannan rukuni sun haɗa da: (a) bayar da tsaro a kafafen intanet da (b) gwada kutse a kafafen intanet da (c) gina kafafen intanet, da sauran makamantansu.

ii. Ƙwadagon da ake nemo ɗan ƙwadago a kan intanet, a ba shi aiki a kan intanet, amma kammalallen aikin da kuma sakamakonsa za su kasance ana amfani da su ta hanyar tu’ammuli da su kai tsaye a duniyar zahiri. Fassararriyar takardar amincewa da halartar gwajin wani magani babban misali ne na wannan nau’in ƙwadago.[3]

iii. Ƙwadagon da ake nemo ɗan ƙwadago ta kan intanet, amma aikin da zai gudanar yake kasancewa a duniyar zahiri. Misalan wannan sun haɗa da (a) tafinta da kamfani zai nemo a kan intanet domin ya yi tafintanci a zahiri a wani wurin da aka ayyana; (b) mai koyar da harshen da za a nema a kan intanet domin ya je wani wurin da zai koyar a zahiri na tsawon wani lokaci.

A yau, Hausawa da dama sun rungumi harkar ƙwadago a duniyar intanet. Nau’o’in ƙwadagon da suke yi sun shafi fannonin ƙwarewa da dama. Daga cikinsu akwai ɓangarorin:

a. Kimiyyar harshe

b. Intanet da na’urori

c. Hotuna da bidiyoyi

d. Bincike 

Yana da kyau a fahimci cewa, duk ire-iren waɗannan ayyukan a yau suna da gurbi na musamman a al’ada. A matsayinsu na nau’o’in sana’o’in wasu Hausawa suka kama a matsayin hanyar dogaro da kai, ba su da waɗansu sunaye da suka wuce kasuwanci da sana’o’i. Kasancewar sun samu ne a zamanance sannan sun shafi fasahohin zamani, hakan bai sauya musu suna ba. Ko da ma dai, a kowace gaɓa a tarihin ɗan’adam, akan samu sababbin abubuwa da suke bijiro wa rayuwarsa. Da zarar ya karɓe su a matsayin hanyar gudanar da rayuwa kuwa, shikenan sun nashe sun koma cikin al’adarsa.[4]




[1] “Talauci shi ne rashin samar wa rayuwa ingantattun abubuwa da take buƙata waɗanda suka haɗa da abinci da kiwon lafiya da kyakkyawan muhalli da ilimi da kuma sutura.” (Sarkin Gulbi, 2007 sh. 47)

[2] Domin ƙarin bayani game da ma’anar kalmar ‘freelancing,’ ana iya duba (Downey, 2024) da (Merriam Webster, 2024b).

[3] A irin wannan yanayi, kamfanin fassara za su nemo mai fassara a kan intanet. Za su ba shi fassarar, yayin da shi kuma zai kammala ya tura musu ta kan intanet. Takardun da aka fassara kuwa, za a gurza su sannan a gabatar da su hannu da hannu ga waɗanda za su rattaba hannu cikin harjejeniyar amincewar.

[4] Haƙiƙa Hausawan da za su taso bayan ƙarnuka biyar, ba za su koyi tunanin jayayya game da kasuwanci da sana’o’in kan intanet a matsayin wani ɓangare na al’adun Hausawa ba.

Post a Comment

0 Comments