Ticker

6/recent/ticker-posts

Barna Ba Ki Da Dadin Ji, Balle Gani: Tsokaci A Kan Matsayi, Da Tasirin Barna A Mahangar Al’adar Bahaushe

TAKARDAR DA AKA GABATAR A TARON ƘARAWA JUNA SANI NA WATA-WATA DA AKE GABATARWA A TSANGAYAR ADAMTAKA A JAMI’AR SULE LAMIDO KAFIN HAUSA, WATAN FEBURAIRU SHEKARAR 2024

ƁARNA BA KI DA DAƊIN JI, BALLE GANI TSOKACI A KAN MATSAYI, DA TASIRIN ƁARNA A MAHANGAR AL’ADAR BAHAUSHE

DAGA

MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD Ph.D.

Phone: 07030803404; Email muazusaadukudan299@gmail.com

SASHIN HARSUNA NIJERIA DA KIMIYYAR HARSUNA

JAMI’AR SULE LAMIƊO, KAFIN HAUSA.

 Abstract

The essence of this research is based on the fact that many research works did not pay much attention to havoc despite its cultural role on the lives of Hausa people. This parer thus aims to explore the concept of havoc and its impact on the Hausa people. Methods used in undertaking this research include studying books, journals, and articles as well as exploring the internet to understand the research area which is Hausa land. The paper will engage in explaining the role that havoc plays on the nature of the life of a Hausa person. It will begin by defining the concept of havoc and its classifications, where it takes place, reasons for its occurrence and who wrecks it. I employ functionalist theory of culture in order for the research to highlight how the Hausa culture views havoc and considers the gravity of its consequences. The paper will explore how the Hausa oral literature engages with havoc. Finally, the paper will highlight the findings of the research, observations and conclude.

Tsakure

 Dalilin wannnan bincike shi ne, kasancewa an yi nazarce-nazarce da yawa game da wasu rayuwa dama, sai dai kash an ɗan kau da kai game da wannan batu wato ɓarna, duk da irin tasirin da take da shi a rayuwar Bahaushe. Manufar wannan bincike shi ne, nazarin ɓarna, matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike, sun haɗa da nazarin wasu bugaggun littattafai, da mujallu, da muƙalu, da yanar gizo, Dangane da muhallin bincike, shi ne, Ƙasar Hausa. Maƙalar za ta kawo bayanai tare da fito da rawar da ɓarna take takawa a yanayin rayuwar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, fagagen da ake yinta, da dalilan yinta, da masu yinta. Na ɗora nazarin bisa Ra’in bincike a kan ra’in morau wanda da Turanci ake kira Functionalism Theory of Culture, saboda bincike ya kawo irin yadda al’adar Bahaushe ta ɗauki ɓarna da muninta, da sakamakonta, Maƙalar za ta kawo jirwayen ɓarna a adabin Bahaushe na baka, daga ƙarshe sai sakamakon bincike, da shawarwari sai kammalawa da manazarta.

Muhimman kalmomi: Ɓarna, Daɗi, Ji, Gani

1.0 Gabatarwa:

Wannan maƙala na da ƙudurin yin nazari a kan ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da irin kallon da ake yi mata tare da rawar da ɓarna take takawa a yanayin zamankewar Bahaushe. Da farko za a kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, da fagagen da ake yinta, sannan da dalilan yinta, da lokutan aukuwarta ko aikatata, da wuraren faruwarta da kuma masu yinta. Tun daga mutane, da dabbobi, da tsuntsaye, da ƙwari da tsutsotsi da kuma wasu abubuwa marasa rai, da kuma hanyoyin riga-kafin aukuwarta. Bugu da ƙari wannan nazari zai hararo irin yadda zamantakewar Bahaushe ta ɗauki ɓarna, muninta da kuma sakamakonta, tare da matsayin masu yinta, kamar a wajen harkar neman abinci ko sana’a, da magani da sauran harkokin yau da kullum. Haka kuma za a kalli irin yadda Hausawa kan yi, ko kuma a dubi irin halin damuwa da wasu mutane kan shiga idan suka ji ko suka samu labarin an yi masu ɓarna ballanta kuma a yi a gabansu wato su gani da idonsu. Wannan dalili ya sanya na yi wa maƙalata take suna da cewa: “Ɓarna Ba Ki Da Daɗin Ji, Balle Gani” Maƙalar zata kawo dukkan bayanai ta mahangar Bahaushiyar al’ada, sannan kuma da jirwayen ɓarna a adabin Bahaushe na baka, daga ƙarshe sai kammalawa da manazarta.

1.1 Manufar Bincike: Manufar wannan bincike ita ce, nazarin ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe.

1.2 Hanyoyin Gudanar da Bincike: Hanyoyin da aka bi don gudanar da wannan bincike, sun haɗa da nazarin wasu bugaggun littattafai, da mujallu, da muƙalu, da hira da jama’a, da kuma wasu rassan adabi, da yanar gizo,

1.3 Farfajiyar Bincike: Dangane da muhallin bincike, shi ne, ɓarna da matsainta a al’adar Baaushe a da’irar Ƙasar Hausa. Maƙalar zata kawo bayanai tare da fito da rawar da ɓarna take takawa a yanayin rayuwar Bahaushe.

1.4 Ra’in Bincike: Na ɗora nazarin bisa Ra’in bincike a kan ra’in Morau na Emith Durkheim (1858-1917) wanda da Turanci ake kira Functionalism Theory of Culture, saboda bincike ya kawo irin yadda al’adar Bahaushe ta ɗauki ɓarna da muninta, da sakamakonta,

2.0 Ma’anar Ɓarna: Ayuba (2015:67) ɓarnace-ɓarnace, Lalata abu da gangan, ta’adi, ɓata abu da yara kan yi wajen wasa ko ƙiriniya, ɓatawa mutum rai. Lalata abu a sababin ruwan iska, wuta.

Ƙamusun CNHN (2006:64) ta’adi, faɗa tsakanin dangi, kuskure wajen karatu musamman karatun ƙur’ani, lalata. Birai sun yi ɓarna, wuta ta yi ɓarna a gona. Bargery, G. (1993:89) Lalata, ko ta’adi, ko ribar da fada tsakanin dangi, almubazzaranci.[1]Encater Dictionary sata ko lalata, ko gusar da ingancin, ko amfanin abu, ko gurbata wani abu. [2] Newman (2020:109) ɓata, ko lalata, ko matsala, ko rauni. [3]

Bisa la’akari da bayanai daga wasu masana kai tsaye ana iya cewa: Ɓarna na nufin lalata ko ɓata wani abu daga matsayinsa na daidai zuwa matsayinsa na rashin daidai. Ko illata wani abin amfani, bisa kuskure ko kuma da gangar wato ana sane don mugunta.inda zai zama sai dai a zubar ko a rasa shi gaba ɗaya.

2.1. Faɗaɗa Ma’anar Ɓarna: Bahaushe kan ɗauki Kalmar ɓarna ya faɗaɗa ma’anarta daga asalin ma’anarta ta farko zuwa sabuwar ma’ana, a inda an san cewar ɓarna a aikace take, in an yi ta, ana ganinta a zahiri. Kuma a mafi yawa, abu mai rai kan yi ɓarna, amma sai Bahaushe ya faɗaɗa ma’anar ɓarna ga wasu abubuwa marasa rai, da waɗanda ba a iya gani. Kamar, iska, da ruwa, da wuta, da zamani, akan samu ɓarna a aiki, da kuma magana.

2.2 Ire-Iren Ɓarna: 1.Ɓarna ta gajeren lokaci, ita ake kira “Ƙaɗa’an”, ko “Zubar-kago”.

2. Ɓarna ta dogon lokaci. 3. Ɓarna kwatsam, sai dai haƙuri (Ɓarin miya a yashi). 4. Ɓ Ɓarna tura haushi.

Amadu Doka Kaduna Mai Kukuma a waƙar komai zakai ka rinƙa Tunani yana cewa:

 Jagora : Ita dai ɓarna iri-iri ce,

Kaga dabbobi iri-iri ne,

Masu ɓarna ma iri-iri ne,

Komai zaka yi rinƙa yin Tunani.

Kaga dai ɓera ya zon ya sata,

Haka yanyanwa ta zo ta sata,

ta ɗiba ta kai wa ‘ya’yanta,

Kun ga jauji ya zo ɗiba ,

Komai zaka yi rinƙa yin Tunani.

Makwarwa ita ma ta zo ta tona,

ta tsinta ta kai wa ya’yanta,

To anan kun ga sun taru sun yi ɓarna,

 Sun bar babban biri shi da mai gona.

2.3 Ɓarna a Magana: Akan samu ɓarin baki ko suɓul da baka, ko zagi ko zargi, ko gori ko tsegumi ko gulma da sauransu. Dukkan waɗannan abubuwa suna iya ɓata yanayin zamantakewa.

Alhaji Adamu Ɗan maraya Jos a waƙar magulmaci yana cewa:

Allahu ya wahidun mai ni,

Raba mu da sharrin magulmaci,

Sannunka Ɗan uwan Shaiɗan,

Mai ɓata halin zaman yanzu,

mai ɓata halin zaman da can.

Har ‘yan uwa sai ya ɓata kaf.

3.0 Dalilan Da Kan Jawo Ɓarna: A Bahaushen tunani, an yi imanin cewa, komai ba ya rasa sanadi. Kamar yadda Ɗangoma mai Garaya yake cewa:

 “Ba zan ƙi dalili ba, Dalilin Aure tsarance”.

Bisa wannan dalili, ya sa al’adar Bahaushe ta rarrabe dalilan ko ayyukan da kan yi sanadin aikata ɓarna. 1. Karambani. 2.Wauta. 3. Gaggawa. 4.Ganganci. 5. Fushi. 6.Gardama (Jayayya). 7. Kuskure. 8. Tsautsayi. 9. Ƙyuiya. 10. Son ganin Ƙwaƙwaf.

3.1. Karambani: A wani lokaci karambani kan haifar da ɓarna, mutum bai iya abu ba, ko bai san kan shi ba, ko ba a sa shi ba, saboda karambani sai ya aikata wani abu, sai ya zama ɓarna. Shiyasa Bahaushe ya ce, “Karambani gajere, kowa ya taɓa shi zai yi tsawo. An fi irin wannan a wajen Yara.

3.2. Wauta: A wani lokaci, wauta kan jawo ɓarna, sai a aikata ɓarna saboda ƙarancin hankali.

3.3 Gaggawa: Gauƙa ko ci-da-zuci tare da ƙosawar saurin samun sakamako, kan sanya a aikata ɓarna.

3.4. Ganganci: Akwai ɓarnar da kan faru wajen yin abu da gangan, an san abin ba zai yiwu ba, amma sai a ce, “bari mu gwada mu gani”, sai ta ɓaci kuma a zo ana nadama.

3.5. Fushi: Aiki cikin fushi ko magana cikin fushi kan yi sanadiyar a aikata ɓarna.

Bisa mahanga ta addini fushi yana da illa, don haka Annabi (S.A.W) ya yi hani da yin fushi, a wani Hadisi ya ce: “La tagadab” (Kar kai fushi) har sau uku.

Haka kuma wani Hadisin Annabi (S.A.W) da ya tambayi Sahabbai cewa wane ne mai ƙarfi? Sahabbai suka ce wanda aka yi kokuwa ya yi kaye. Sai Annabi (S.A.W) yace: a’a, mai ƙarfi shi ne wanda fushinsa ya taso, amma ya danne zuciyarsa.

Duk wanda ya yi fushi aka ce ya yi haƙuri matuƙar dai ya yi, to Allah zai taimakeshi, in kuma ya ƙi to zai ga abin ƙi. Kamar yadda ya zo a Suratul Luƙman aya ta 17. Inda aka nunawa mumini ya tsai da sallah, ya yi umarni da aikin alheri, kuma ya yi hani da mummunan aiki, kuma ya yi haƙuri.”

Bisa al’ada mutum mai saurin fushi, Bahaushe na kiransa da kububuwa. Ba duka harkoki ake yi da shi ba. Domin ana kallon sa mai murɗaɗɗen hali. Misali idan miji da mata suka samu saɓani sai aka ga ana basu haƙuri suna ƙi, da zarar ɓarna ta auku (saki), sai kuma a koma nadama.

A al’adance idan aka yanke wa mutum hukuncin kisa in rage kwana sai a tafi da shi kasuwa, to duk abincin da ya gani kamar tsire ko waina, sai ya fizga ya ci. Duk saboda fushin za a kashe shi.

A kimiyyance, wani Likitan ƙwaƙƙwalwa Paul (2004) a Jami’ar New York Amurka ya ce: “Halaye huɗu kan sanya a yi haukan wucin gadi: 1.Fushi (anger). 2.Tsoro (phobia). 3. Sha’awa (desire). 4. Zaƙuwa (anxiety)”.

3.6. Gardama (Jayayya): Duk inda aka samu mutum biyu (2) ko fiye da haka suka yi jayayya a kan wani al’amari, to matuƙar ba a samu daidaito ba, aka yi aikin, to ana iya samun ɓarna. Kamar yadda Alhaji Musa Ɗanƙwairo ke cewa:

Jagora: Gardama ma-tsirar sababi,

 An bar gama ta ran wani bai ɓaci ba”.

3.7. Kuskure: Rashin iya abu ko manta yadda ake yin shi, ko kauce wa wani umarni. Shi ma irin wannan kan sa a aikata ɓarna.

3. 8. Tsautsayi: Akwai ɓarnar da kan faru a dalilin tsautsayi, mutum ya saba yin abu, kuma ya ƙware, ya san kan shi, amma sai a samu tsautsayi. Haka kuma, wata ɓarnar ta faru, amma ba ta bayyana ba, sai wani na taɓawa sai ta bayyana. Sai a ce wane ne, to a nan ya taka sawun ɓarawo.

4.0 Masu Yin Ɓarna: Babu shakka, aiki ba ya yin kan shi sai ga mai yin shi. Haƙiƙa akwai masu aikata ɓarna kamar yadda al’adar Bahaushe ta keɓe su, sun haɗa da:

1.      Mutane.

2.      Dabbobi.

3.      Ƙwari / Tsutsotsi.

4.      Tsuntsaye.

5.      Wasu abubuwa.

Bisa wannan zai sa mu lura cewar, abubuwan da kan aikata ɓarna akwai masu rai da marasa rai.

4.1. Mutane: Ta fuskar mutane, akwai Yara. Shi ne a kan ce, “Hannun Biri ba ka zama kurum”. An danganta birin da yaro, saboda wasu ɗabi’u, kamar karambani, da kwaikwayo, wanda kan sa su aikata ɓarna. Wani abin ya ga manya na yi, amma saboda ya kwaikwaye su sai ya aikata ɓarna, kamar abin da ya shafi Abinci ko na kayan aiki, da magana.Yaro, da mahaukaci, da mata.

4.2. Yaro Da Ɓarna: Ɓarna na nufin lalata, la'anta, ko ɓata wani abu da hannu ko ƙafa ko wani ƙarfe. Tana iya yiwuwa a fasa ko huda ko yaga ko kuma a rusa da sauransu. Bahaushe na alaƙanta ɓarna da yaro ne, saboda wasu dalilai kamar haka: -1. Ƙarancin hankali da tunani 2. Son ganin ƙwa-ƙwaf. 3. Kwaikwayo. 4. Karambani. 5. Tsautsayi. Muhammad (2019)

1. Ƙarancin Hankali Da Tunani: Bahaushe ya yi imani cewar lallai yaro fama da qaranci ko kuma raunin hankali da na tunani, kuma ba ya tunanin abin da zai je ya dawo. Bisa wannan dalili ne ya sa bahaushe kan ce yaro mai varnar rashin dalili. Haka kuma da zarar tunanin da zuciyar ta riya masa sai ya aikata. Zai iya ɗaukar abu komai amfaninsa ya fasa.

2. Son Ganin Ƙwa-ƙwaf: Hujjoji marasa iyaka da suka tabbatar da haka, cewar yaro akwai shi da son ganin ƙwaƙwaf, wannan ya sa komai yaro ya ji ko ya gani, sai ya tambaya ko ya tava, balle kuma aka ce babu wani babba da zai tsawatar masa. Mafi yawa yara kan so su san mene ne wannan? Da me aka yi? Mene ne a ciki? da sauransu. A wani lokaci ɓarnar yaro kan tafi tare da wayau ko shekarunsa. Wani yaron idan ya yi ɓarna ya kan gudu, ko ya voye saboda kar a yi masa faɗa, akwai inda yaro bai gudu kuma bai ɓoyewa, yana iya faɗa cewar shi ne ya yi kaza, saboda bai san daraja da amfanin abin ba, shi dai ya ga abin da aka haɗa aka yi.

3. Kwaikwayo: Al'adar Bahaushe ta jingina ɓarna ga yaro, bisa dalilan kwaikwayo. Allah Ya yi yaro da son kwaikwayon abin da ya ga ana aikatawa.Yaro da biri akwai su da kwaikwayo. A wani lokaci yaro ganin an yi aiki ko Magana zai fara kwaikwayon abin da ya ga ana yi, wannan kan ja shi zuwa ga ɓarna, kamar ɗaukar wani abin aiki garin ya kwatanta abin da wani yayi, sai abin ya fashe ko ya karye. A wasu lokutta yaro kan cutar da kansa a dalilin yin ɓarna, misali wajen aikata wani abu da ya ga wani ya aikata.

4. Karambani: Kowa ya san yara iyayen karambani ne, wannan dalili ne ya sanya ake alaƙanta ɓarnar yaro da karambani. Akwai wata karin magana mai cewa: “hannun biri baka zama kurum” wannan magana ba da biri ake yi kai tsaye ba a'a, da yaro ake yi, saboda zai yi wuya a ajiye wani abu a gaban yaro, ko kuma ya tarar an ajiye bai taɓa ba. A wani lokaci daga tavawar ne sai varnar ta auku. A kan ɗorawa yaro ɓarna ne ko da ba shi ya yi ba, saboda an san shi da karambani har akan ce: “yaro taɓa ba a saka ba” ko “karambana ko ka ga dokin sarki”.

5. Tsautsayi: Tsautsayi na nufin, wani abu ya faru da mutum bisa kuskure ba tare da ya yi niyyar aikata abin ba. Bahaushe na ganin cewa wani lokaci wata ɓarnar na aukuwa ne bisa tsautsayi, ma'ana yaro ba da gangar ya yi ba. Ko da yake ba a cika amincewa da wannan dalili ba, bisa dogaro da sanin waɗancan dalilai na karambani ko kwaikwayo, amma kuma wani lokaci a kan karɓi uzurin. A ƙarshe ana iya cewa ɓarnar yaro na faruwa ne bisa waɗannan dalilai da suka gabata da ma wasu da ba a kawo ba. Muhammad (2019)

4.3 Mahaukaci: Shi kuma Mahaukaci, a kasancewarsa ba shi da hankali, kan sa ya aikata ɓarna. Wannan ya sa ake kauda kai da ɓarnar da ƙaramin Yaro ko Mahaukaci ya yi, amma idan Mahaukaci ya je yana ba da labarin ɓarnar da ya yi, to sai danginsa su biya wannan ɓarnar.

4.4 Mata: Ana danganta ɓarnar Mace bisa waɗansu dalilai kamar haka: 1.Kuskure. 2.Tsautsayi. 3.Ganganci.

1. Ta Kuskure: Shi ne ta iya abin, sai mantuwa ta sa ta yi kuskure.

2. Ta Tsautsayi: Wannan shi ne , ta iya abin kuma ba ta manta ba, sai a samu wata ƙaddara ta gitta a aikata ɓarna bisa tsautsayi. Ana cewa, “Rugum kwaram ɓarin mai ɗaki, in ka ji shiru ita ta yi abinta”. Haka kuma ana cewa: “Kwaram haɗa kaya”.

3. Ganganci: Akwai ɓarnar da kan faru, wadda mace ta yi cikin ganganci, musamman idan ta yi aiki cikin fushi, kamar lokacin da baƙonta (Jini) zai zo, ko kuma tana wanki (al’ada). Ko tana da yaron ciki, ko ta yi faɗa da mijinta, ko an yi, ko za a yi mata kishiya. Kamar wata Waƙar Dandali ko Gaɗa, inda ‘Yanmata ke cewa:

Amshi: Iye

Mai waƙa: An yi mata kishiya tana watsi da hatsin tuwo

Amshi: Iye

4.5. Dabbobi: Dabbobi, halittu ne masu ƙafafu huɗu na gida da na daji”[4] “dabbobi, dukkan halitta mai ƙafa huɗu”.[5] “ wasu, halittu ne masu ƙafafuwa huɗu jikinsu lulluɓe da gashi”.[6] ‘dabba’ muna nufin dukkan abu mai rai ne in ka ɗebe tsire-tsire, watau ba nufi muke dabbobin gida da daji kaɗai ba, amma har tsuntsaye da su macizai da kwaɗI da kifaye.[7]

Babu shakka al’adar Bahaushe ta danganta ɓarna ga wasu dabbobi na gida da na dawa, manya da ƙanana. Su ma ɓarnarsu tana iya faruwa a dalilai kamar haka: 1. Faɗa a tsakaninsu. 2. Dalilin neman abinci ko abin sha. 3. Dalilin gyara muhallinsu. 4. Ko Barbara a tsakaninsu.

1.Faɗa: Rigima da tashin hankali tsakanin mutum biyu ko fiye. Gwabzawa jiki da jiki don rikici, ko yaƙi da makami tsakanin mutane. Faɗa na nufin saɓani ko rashin jituwa, wanda kan jawo husuma har zage zage a wani lokaci har da doke- doke a tsakanin mutane ‘yan adam. To su ma dabbobi akan samu irin haka a tsakaninsu, duk da yake ba sa magana ana ji a asarari. Dabbobi su ma sukan yi faɗa, wannan kuwa na faruwa ne bisa wasu dalilai. Kamar yadda Bahaushe ke cewa ko tsakanin harshe da haƙori ma akan saɓa. To haka yake su ma dabbobi ba su tsira ba. Wannan kuwa na faruwa ko da a jinsi ɗaya ne yasu-yasu, ko da bare na wani jinsi baƙo ko da Ɗan adam. Muhammad (2015)

2.Barbara: Bahaushe na da wani tunani, game da rayuwar dabbobi da alaƙarsu da barbara. Bahaushe na ganin dabbobi kan yi barbara ne a wurare daban-daban, kuma a lokuta daban-daban, sannan bisa dalilin hakan sukan yi ɓarna. Dabbobi kan yi faɗa ne, a wani lokaci a wurin kiwo don cin abinci, ko shan ruwa, ko a wurin kwana, watau muhalli ko kuma a wurin hutawa.Imam (1969). Babban dalilin da kan sanya su faɗa, shi ne don kare ƙananan ‘ya’yansu, wanda kan iya jawo ɓarna. Duk a ƙarshe faɗa kan yi sanadin ɓarna.

3.Neman abinci: Tabbas kiwo, ko ruwa kan sanya wasu dabbobin faɗa a tsakaninsu, ko da wani baƙon jinsi da ya yi kutse. Wannan kuwa ya haɗa dabbobin gida da na daji. Misali tumaki da awaki sukan yi faɗa a wurin cin dusa a wurin cin abinci. Haka su ma na daji, kamar zaki, ko damusa, ko kura da sauransu. Wasu dabbobi yunwa ce kan sanya su zama mafaɗata don su samu abinci. Dangane da Dabbobin dawa da Bahaushe ke alaƙanta su da ɓarna, sun haɗa da Biri da Kurege da Jauji da Gyazbi da Yanyawa da Kura da Dila da kuma Giwa. Kowanne daga cikinsu su kan yi ɓarna bisa waɗancan dalilai. Amma Biri shi ne jagoran maɓarnata a dabbobi, kamar yadda Amadu Doka Kaduna mai Kukuma yake cewa:

 Jagora: Kun ga fa ɓarna iri iri ce,

Kun ga Yanyawa ta zo ta tona,

Ta tsinta ta kai wa ‘ya’yanta,

Sannan Kurege ya zo ya sata,

Ya ɗiba ya kai ga raminsa,

Shi kuma Jauji ya zo ya ɗiba,

Ya ɗiba ya kai shi raminsa,

To kun ga sun taru sun yi ɓarna.

Amma an bar babban Biri da shi da mai gona,

 

 Amshi: Komai za ka yi ringa yin tunani.

Haka kuma Alhaji Musa Ɗanƙwairo yana cewa:

 Jagora: A zuba ɓarna, jan Biri bai ɗara bika ba,

Tsula na nan, ɗan ƙaraminsu,

To shi ma yana da ƙarya gero.

 

 Amshi: Babban Jigo Na yari,

 Uban shamaki, tura haushi.

Akwai Karin Magana mai cewa:

Laifin ba na yanzu ba ne, wai an jefi biri da rani.

Hannun biri baka zama kurum.

Giwa ki ci mai gona na nan,

Giwa kin wuce kora da kara.

4.6 Biri: Biri ya zama kamar shugaba a wannan fuskar, saboda biri ne kawai aka sani da ɓarna ta ban haushi da mamaki da rainin wayo. Bahaushe ya nazarci wannan halin biri, sai ya yi masa kirari da cewa; biri mai ɓarnar a faɗa, sannan ya lura da yanayin ɓarnar da biri kan yi, idan ya shiga wurare daban-daban.

A wata hira da Malam Ashana Ɗankama Kano, cewa ya yi:

Biri a Gonar Auduga: Bahaushe ya lura da cewa idan biri ya shiga gonar auduga, musamman wadda ta fara yin gululu. Wai sai biri ya ce ko ba za’a ci ba, bari a tsinke ko a ba da haushi, sai kawai ya fara tsinke gululun audugar nan yana zubarwa.

Gonar Dawa: Idan biri ya shiga gonar dawa musamman in ta fara yin ciki(gululu), wai sai ya ce wannan wane ne take yiwa fushi, sai ya rinƙa kakkaryewa yana zubarwa, har sai ya gaji.

Gonar Gero: Idan biri ya shiga gonar gero, musamman wanda ya fara zare kai amma bai yi ido ba, wai sai biri ya ce ‘bari mu ji ko da zaƙi?, sai kawai ya fara karye kan geron ta wajen sullen karan, yana yi taunawa yana jefarwa har sai ya gaji ko ya ji motsin wani mutum.

Gonar Yalo :Idan biri ya shiga gonar yalo, sai fara da yin tsalle, sannan sai yace’da manya muke harka ba ruwan mu da taratsagutsa, shi ma mara zaƙi jifa mukai da shiya. wannan dalili ne yasa biri ɓarna a gonar yalo fiye da ko’ina.[8]

Wannan ya sa ko an yi mutummutumi an sa a gona, sai dai ya hana wasu dabbobin ɓarna, amma ban da biri. Wannan yasa Musa Ɗanƙwairo a wata waƙa mai suna:Bello shiri nai yai kyau bai ya da gudun Arna ba, yake cewa:

 Jagora: Mutummutumi mutumin banza,

 Ko ka yi shi ka kai gona,

 ba za ya tsare komai ba,

 Ɓarnar da akai sai an yi,

 Don ba za ya tsare komai ba.

 Gindi:Bello shiri nai yai kyau ,

 Bai ya da gudun Arna ba.

Ɗan waƙa da ya gabata ya nuna cewa mutum-mutumi kamar shigar burtu ne da ake yi wa wasu dabbobi, saboda a hana su yin ɓarna a gona. Biri shi kuwa, sanya wannan alamar ta mutum-mutumi a gona ba ya hana shi yin ɓarna. Dabarar da biri yake yi kuwa, ita ce, da ya shiga gona wadda aka sa mutum-mutumi, sai ya gwada ya ga mutum ne ko a’a ?. Da zarar ya gwada ya ga bai yi motsi ba, sai kawai ya cigaba da ɓarnarsa.

4.7 Dabbobin Gida: Babu shakka al’adar Bahaushe ta danganta ɓarna daga wasu dabbobin gida, manya da ƙanana. Akwai Akuya, da Mazuru, da Ɓera, da Gafiya, da dai sauransu. A dangane da Dabbobin Gida babu kamar waɗannan da aka lissafa dangane da abin da ya shafi abinci da muhalli, ɓarnarsu a bayyane take barna da rana, Su ma ɓarnarsu tana iya faruwa a dalilai kamar haka:

Akuya: Bahaushe ya ɗora wannan hali na ɓarna ga akuya, wannan yasa har ya yi mata kirari da cewa: 1.Taɓa ƙofa mai asirin sata. 2. Jar akuya mai kai ga yara ɓarnar.

Haka kuma Bahaushe ya lura da yanayin ɓarnar da akuya kan yi, sannan kuma ya rarraba ta kamar haka: Idan akuya ta tarar da dannin kara (shinge), wanda aka yi shi a tsaye, sai ta sanya ƙahonta ta huda don ta shiga. Haka kuma, idan dannin a kwance a ka yi shi,sai ta yi rimi (miƙe ƙafafun gabanta sama), a inda ta kan tsaya bisa ƙafafunta na baya, saboda ta yi ɓarna, sai ta danna ƙafafunta na gaba don ta shiga ta yi ɓarnawannan ya haifar da Karin maganganu kamar haka: Jar Akuya mai kai ga yara ɓarna. Taɓa ƙofa mai abincin sata.

Akwai wata maganar azanci da Bahause ke cewa: Idan akuya ta je ma’auna a cikin kasuwa wai ita laya take gwadawa shi yasa sai bayan ta sanya bakinta a kwandon hatsi ta dumbuza ta cika baki sannan ake ganinta a koreta. Saɓanin tunkiya ita kuma sa’a take gwadawa si yasa ita kuma ko an ganta an yi mata tsawa bai hanata cin hatsin har sai an haɗa da duka.

Akwai wata waƙar dandali ta yara da ake cewa:

 Waƙa: Ɗan akuyana,

 Amshi: damushere,

Waƙa: ya shiga rumbu,

Amshi: damushere,

Waƙa: Don yayi ɓarna,

Amshi: damushere,

Waƙa: za a bugeshi,

Amshi: damushere,

Waƙa: Nan da takobi,

Amshi: Damushere,

Waƙa: nan da su adda,

Amshi: damushere.

Dangane da haka ne Alhaji Musa Ɗanƙwairo ke cewa:

 Jagora: Da Burgu da Zomo da Kurege,

Kowanne hali ya kai bambam,

Burgu shi ka rami cikin ƙunƙu,

Zomo shi ka rami gaton kalgo

Kurege shi ya ranar gaba,

Ya yi ɓullo nai can da ban,

In an ragaɗa in fice wa ta.

 Amshi: Gagarau mai jiran daga, Ali Namagaji ci fansa.

Ya ƙara da cewa a wata Waƙar Sani Bello:

 Jagora: Ga wanga mai yi ma gyara,

ga wanga mai yi ma ɓarna,

In ance ka zo ka zaɓa,

Duk wanda ka fis so cikin ranka,

wanga mai yi min gyara,

 shi naf fi so cikin raina,

Ban yarda da mai yi min ɓarna

Ni kam ban yarda da mai yi min ɓarna.

 Jagora: Mage kin wahal da mata,

Suna ta jere kina ta rusawa,

Mage farauta ta kai cikin ƙorai,

Mage ja’ira shege kan nan kama da ɗan ƙoƙo.

 Amshi: Sani Bello Shiryayye kake ka wuce a raina ma.

Akwai misali a wani rubutaccen zube da aka samu jirwayen ɓarnar akuya a ciki, kamar haka:

Labarin Nahana Sarkin Rowa.

“A wani gari wai shi Tanga,an yi wani mai rowa, sunansa Na-hana. Wanda ba taɓa ganin ya ba wani ko ruwan sha in ya bi ta gidansa ba. Da anininsa ya ɓace masa,gwamma ka mare shi sau biyu.Yana da awaki da tumakai ƙwarai da gaske ko shi ma bai san iyakarsu ba. Ran nan ya dawo daga kiwo, sai wata akuyasa ta sa kanta cikin tukunya kai ya ƙi fita. Na-hana ya yi ya yi, ya kasa jawowa. Ga shi kuwa ba ya iya fasa tukunyar, don yana ganin ɓarnar kuɗi ne. Bisa dole ya kira Mahauta suka yi cinikin akuya ya sayar, yace su yanka su cire kan su ba shi tukunyarsa. Mahauta yanka akuya amma suka kasa cire kan akuyar daga tukunya. A maimakon haka sai tukunya ta fashe Na-hana ya yi baƙin ciki ƙwarai. Ga sayar da akuya da arha ga asarar tukunya ta fashe, sai da ya yi kuka har da hawaye. Tun daga ran nan bai ƙara ajiye a ƙasa ba, kullum sai bisa inda awaki ba su kaiwa saboda ɓarna.” [9]

Mazuru: shi ma gwani ne kuma ya yi fice a fagen ɓarna a wata fuskar kuma kwaɗayi, ko a maganganun yau da kullum da akan ce:

1. Mazuru cinye kaji.

2. Tuban muzuru, amma ga kaza a baki. Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a waƙarsa ta Sarkin Yawuri Mamman Tukur Mai martaba, cewa ya yi:

Jagora: Babban mazuru can haka,

 Sai tumbiɗar kaji yakai,

 Shi ba shi jin tsoro haƙo.

 Sarkin Tukur Baban Hassan

Gindi: Mamman Tukur Mai martaba,

Dangane da ɓera da kurege da gafiya, su ma suna da ɗabi’ar ɓarna a wurin Bahaushe, amma su a matsayin tsumi da tanaji yake. Don kuwa in har suka samu kayan abinci sun dinga ɗiba ke nan har sai inda ƙarfinsu ya ƙare. Musamman gafiya idan ta samu buhun gyaɗa ko kalwa, ɓata na ɓatawa ta ɗebi ɗiba zuwa a matsayin tana tattalin abinci.

Gafiya: Tana iya kwana tana ɗibar kayan abinci tana tarawa, a wani wuri na musamman da ake kira “horonhoromi”, wani rami ne wanda ya yi kama da rumbu ko sito. Akwai wasu maganganun azanci masu cewa:1.Tarin gafiya tarin banza. 2. Gafiya tara ba don ki ci ba,

3. Gafiya ta tsira da na bakin ta. 4. Gafiya ki kwana tari da asuba a buge ki.

5.0Tsuntsaye: Abraham, (1947) cewa ya yi; Tsuntsaye, Halittu ne masu ƙafafu biyu da fukafukai na gida da na daji. Ƙamusun Hausa (2006) ya ce; tsuntsaye, halitta mai ƙafa biyu da fukafukai, da sukan haihu ta hanyar saka ƙwai da ƙyanƙyaƙeshewa. Bargery, (1993) cewa ya yi, tsuntsaye wasu, Halittu ne masu ƙafafuwa biyu da fukafukai biyu, jikinsu lulluɓe da gashi.

Bisa dogaro da bayanai da suka gabata, muna iya cewa; Wannan kalma ta tsuntsaye, wasu halittu ne waɗanda Allah Ya halitta suna da ƙafafu biyu da fukafukai biyu, sannan akwai masu yawo a sararin samaniya, ta hanyar tashi da fuka-fukai, tsuntsaye su ma akwai na gida da na daji, Dangane da tsuntsaye kuwa akwai irin su kaza, da zabo, da makwarwa, da shaya, da jan baki, da sauransu. Tsuntsayen gida kan yi ɓarna a kayan abinci, misali idan an yi shanya, haka su ma tsuntsayen daji sukan yi ɓarna ne a kayan amfanin gona, tun daga shuka har zuwa girbi.

6.0 Ƙwari Da Tsutsotsi: Bahaushe na danganta ɓarna da wasu ƙwari da tsutsotsi. Wannan ɓarna kan shafi gidainda Bahaushe kan zauna, da kuma Gona inda yake yin noma, ko rumbu gun adana abincinsa.

Ɗabi’un Ƙwari A Tunanin Bahaushe: Bisa la’akari da yadda ƙwari ke gudanar da rayuwarsu, sai Bahaushe ya alaƙanta wasu ɗabi’u na mutum ga ƙwari. Akwai ƙwarin da Bahaushe ya alaƙantasu da mugunta ko cutarwa, su ne kamar cinnaka da sauro da barbaje da rina da ƙwarƙwata da kuɗin cizo. Haka kuma, akwai waɗanda suka danganta da kwaɗayi, su ne kamar ƙuda da shazumamu da kwarkwasa da kyankyaso da tsatso. Bayan haka, akwai waɗanda ake alaƙantasu da kishin mace da sha’awa musamman gamaɗiɗi (ƙwaron rimi). Ban da wannan kuma akwai waɗanda ake dangantasu da kiyashi, gizo-gizo da zanzaro. Akwai masu zumunci da haɗin kai da biyayya ga shugaba, su ne kamar zuma da tururuwa da gwano da zago da sauransu. Akwai jarumai masu jan hali, su ne gwano da zago kiyashi da zirnaƙo. Akwai masu alaƙa da ƙazanta, su ne kamar ƙuda da kyankyaso da ƙwarƙwata da kuɗin cizo da bi-tsami da dai sauransu.

7.0 Wasu Abubuwa: Akwai wasu abubuwa marasa rai waɗanda Allah Ya halicci ɗan Adam ya rayu tare da su. Duk da yake suna da matuƙar amfani a gareshi, to amma duk inda aka samu kuskure ko ɓacin rana, sai su yi wa mutum mummunar ɓarna inda sukan yi sanadin asarar dukiya da na rayuka. Waɗannan abubuwa kuwa sun haɗa da: ruwa, da iska, da wuta, da jahilci, da talauci, da zamani, da Annoba, da yaƙi.

7.1 Ruwa: Idan aka samu ruwan sama da damuna mai yawa wanda har koguna da fadamu suka cika suka tumɓatsa, har aka samu ambaliya. Ambaliya ɓarnar da ruwa yakan yi a inda akan yi asarar rayuka da na dukiya, da gidaje, da kayan amfanin gona, da dabbobi su salwanta. Alhaji Mai daji Sabon Birni yake cewa:

Jagora: Gwamma ruwa da ɓarnar fari,

 In ko sun tashi kaftu mukai.

Amshi: Isah Ɗan Sanda mai duniya.

7.2 Iska: Iska ita ma takan yi ɓarna har ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi, idan da damuna ne a kira ta da iskar hadari, idan kuma da kaka ne a ce iskar kaka, idan kuma da bazara ne a ce guguwa.

 Babba Ƙawa: Guguwa, guguwa ta taso.

Guguwa, guguwa ta taso.

Uwar miji guguwa ta taso.

 Ƙawaye: Guguwa ta wuce da amarya

Uban miji guguwa ta taso,

Guguwa, guguwa ta taso.

7.3 Wuta.wuta kan yi ɓarna, idan aka samu kuskure ko ɓacin rana ta hanyar ƙone gidaje ko gonaki ko daji, sai a kirata gobara. Idan kuma wuta ta ƙone daji sai a kirata da wautar daji.

7.4 Jahilci, Haƙiƙa shi ma jahilci kan yi ɓarna a harkar gudanar da rayuwa ta fuskar gamuwa da cikas a inda hakan takan jawo asarar rayuka da dukiyoyi, yakan hana al’ummar Ƙasa ci-gaba. Kamar yadda Salmai Albasu a waƙar Soriyo take cewa:

 Zabiya: Mu kai yara makaranta,

Su san ilmi mu ji daɗi,

Musan Jahilci babu kyau,

 iya ɓarna a cikin Ƙasa.

Mu’azu Haɗeja a waƙar Ilmin Zamani yana cewa:

Da tsiya da talauci duk suna,

Gun da jahilci yai sansani.

7.5 Wadata: Bahaushe na da tunanin cewa samun wadata na dukiya ko abinci ko tufafi. A wani lokaci Bahaushe kan yi ɓarnar abinci idan akwai wadata a gidan ana iya ganin shaida ko a wajen wanke wanke ko a rariya ko juji inda za a samu an zubar da abinci. Haka kuma Idan kaka ta yi bayan an yi girbin kayan gona akan shirya bukukuwa kamar dafuwar ɓarna. Ko kalankuwa. Akwai bikin ɓacin kaka na abinci da tufafi. Ko bayan an kammala bikin aure amarya takan yi girki da ake cewa dahuwar ɓarna, ta hanyar amfani da kayan gara da aka kawo mata.

7.6 Talauci : Abubakar A.Y.(2015:475) Tsananin rashin wadata, 2. Tsananin tsiya. (2015:135) Fatara: rashin kuɗi na ɗan lokaci. CNHN (2006:423) Rashin Wadata,Tsiyata, Fatara, ƙarancin Ko Rashin Kuɗi na Wani Lokaci . Newman (2020:246) tsiya, ko tsananin rashi.

Illar Talauci A Mahangar Al’ada: Bahaushe kan yiwa talauci kirari da cewa: “Talau-talau mugun tsoho, ƙadagi ƙanin mutuwa, lalata mutum da sauran ransa”. Wannan kirari na talauci gaskiya ne, saboda talauci kan yi tasiri ga rayuwar Ɗan adam, ta kowacce fuska. Rayuwar ma gaba ɗaya takan samu dabaibayi ko tarnaƙi a kasa sukuni da walwala a cikin al’umma. Talauci kan yi tasiri matuƙar aka ce ya shafi mutum, to sai kuwa an ga alama. A kan wannan hujja ce ya sanya duk mutumin da ya tsinci kansa a cikin talauci ko kuma ya faɗa masa, yake shiga wani hali na gaba damusa baya siyaki. Mafi yawa mutane matalauta ke galabaita fiye da tsararrakinsu da suke da wadata. Wannan kuwa na bayyana ne tun daga ɗabi’unsu, da tunaninsu, da kamannunsu, kai hatta yanayin fatar jikinsu kan bambanta da sauran jama’a. Almubazzaranci na nufin ɓarnatar da kudi ko wani abin amfani ta hanar kashewa ko lalatawa ko banzatarwa da nuna halin ko-in-ka ko rikon sakainar kasha yayin amfani da shi, wanda hakan ka iya sa ya lalace ko ya ƙare cikin ƙanƙanin lokaci, koma bayan yadda zai yi ƙarko ko auki idan aka bi da shi cikin taka tsantsan.

7.7 Yunwa.To in muka tsaya, muka dubi yadda Bahaushe yake zargin yunwa da yin illa ga dukkan rai ba mutum kaɗai ba. Zamu ga cewa wahalar da yunwa ta yi sanadin ta, tafi komai illa. Misali wasu kirari da karin maganganu da Bahaushe ya yi da suke cewa:

“Yunwa ta bahuwa mai mahurin ƙarfe”,

 “Yunwa ba’a yi maki lahaula

da rubutu gara kwaɗon rogo

ko ko tsari wanki fari”,

 “Yunwa sa dogo doro sa gajere faɗin ƙirji”.

Bisa dogaro da waɗannan bayanai, sai muce yunwa na taimakwa matuƙa, wajen sauyawa mutum kamannu ya koma tsohon tilas. Ana iya cewa akwai unwa ta annoba, kamar ‘yar Gusau, da ‘Yar balange, Ƙwaƙuduba da sauransu.

7.8 Annoba:Korona, Maibaushe((kwalara ko amai da gudawa), Baƙon dauro(Ƙyanda), ‘Yanrani, Agana, Sanƙarau, da sauransu. Idan annoba ta faɗawa gari akan yi asarar rayuka da na dukiya. A dalilin ɓarnar da annoba ke yi yasa Bahaushe ke cewa: haifi-haifi ka ga kamarka haihuwa na maganin annoba.

7.9 Tsufa. Tsufa kan faɗawa ko kama mutum, a mafi yawan mutane daga shekara sittin zuwa saba’in (60-70).Komai daular da mutum yake ciki, sai an ga wasu alamu.waɗanda tsufa kan aiko a matsayin ‘yan saƙo.Kamar irin su furfura (farin gashi), jemewar ido gefen yayi fari kwal, billen gara wani lotsawa da fuska kan yi dai-dai ƙasa da tayani muni (kunduki), raunin jiki, da sauyawar ɗabi’a.

Bugu da ƙari, shi tsufa da irin yadda yake zuwa ga kowa. Akan samu saɓani tsakanin mutum zuwa mutum, kamar yadda wani tsohon zai rikice ko takwarkwashe, sai a samu wani ya kai waɗannan shekaru, amma bai rikice ko takwarkwashe ba. Haka kuma a kan saɓa tsakanin jinsi zuwa jinsi, kamar tsufan mace, wasu matan sukan fi maza ruɗewa, hakanan ko a maza wani kan fi wani, ko kuma wata ta kan fi wata.

Rayuwar tsufa kan fara kama mutum ne a wani tsari na mataki-mataki, ko a hankali. Ana iya cewa tsufa ba ya faɗawa ko kama mutum a lokaci guda ko dare ɗaya. Abin da yake faruwa shi ne, tsufa kan fara turo wakilai ko alamu, kaɗan daga cikin alamun sun haɗa da furfura (farin gashi), da faɗuwar haƙora, da ƙorafi ko mita ,da yawan faɗa,da laulayi,da raunin gaɓoɓi da sauransu.In aka koma ta fannin shekaru, mafi rinjaye ana ganin daga shekara sittin (60). Daga kuma waɗannan shekaru har zuwa 70-80-100. Idan mutum ya kai shekaru 90-100 akan ce tsoho tukuf.

Bisa lura da irin yadda rayuwar mutum ke sauyawa sannu a hankali ko kuma a ce yau da gobe. Wannan ya bayar da damar gano wasu sauye-sauye da ke faruwa a ɗabi’unsa, saɓanin waɗanda aka san shi da su a da. Waɗannan baƙin ɗabi’u su ne Bahaushe ya kira alamun tsufa.

 Ire-Iren Tsufa.Kamar yadda bayani ya gabata, babu abin da Bahaushe ya ƙyale shi haka kurum, sai da ya nazarce shi, don tantancewa tare da karkasashi zuwa mataki-mataki gwargwadon matsayinsa. Dangane da harkar rayuwar tsufa ma, bata tsira ba, don kuwa Bahaushe saida ya rarraba ta zuwa kashi huɗu kamar haka: - 1.Tsufan Shekaru. 2. Tsufan Wahala. 3.Tsufan Halitta. 4.Tsufan Jawowa kai.

7.10 Wahala.Wahala kowace iri ce bata da daɗi, kamar yadda ake cewa: “Wuya ko da magani ba daɗi”, “Maganin wuya a gudu”, “Wahala ke sanya mutum ya lalace”. Waɗannan karin maganganu sun nuna matsayin da wahala take da shi,da kuma irin yadda take yiwa rayuwar mutum illa ko tasiri.

Alhaji AAdamu Ɗanmaraa Jos a waƙar Lebura yake cewa:

Wahala mai sa a lalace.

Yunwa mai kai maza kwance,

Ta kashe ba sai da aibu ba.

7.11 Zamani: Zamani, abin da agogo, da kwanaki, da watanni, da shekaru suke aunawa don kintatar faruwar abu, ko halin da yake ciki, ko yadda zai kasance a nan gaba.[10]lokaci ko sa’i, yi mulki na ƙayyadadden lokaci na shekara huɗu, ya zauna har na ajalin wata uku, lokaci-lokaci, ko loto-loto , ko jiƙo-jiƙo.[11] Loto ; sa’a; sa’i; sa’ili; wokaci; yayi; zamani.[12]

Bisa la’akari da bayanai daga masana, muna iya cewa lokaci na nufin daga hudowar rana zuwa faɗuwarta, sannan kuma daga faɗuwarta zuwa hudowarta, to shi ya haɗa dare da rana, wuni da kwana. Tabbas, zamani ya iske Bahaushe da wasu kyawawan ɗabi’u, kuma na-san barka waɗanda tilas ne mutum ya yaba dasu. Kash! Sai dai kuma zamanin ya yi wa wasu daga cikin ɗabi’u korar kare saboda tasirin boko ko rayuwar Turawa. Ga wasu guda goma waɗanda zamani ya kora, ko bai kore su duka ba, a yau masu aikatasu sun yi ɗaranci matuƙa. Waɗannan ɗabi’u kuwa, su ne: - 1 . Ciyayya. 2. Kawo ƙwarya. 3. Marka-marka. 4. Ɗauki. 5. Riƙo ko goyo. 6. Zumunci. 7. Ziyara. 8. Gudummuwa. 9. Aikin gayya. 10. Zaman gandu.

7.12 Mulkin Mallaka (Colonial Rule) 1900-1960; Turawan kamfani su ne suka share wa Turawan mulkin mallaka hanya, (colonialist). Tabbas Turawan kamfani sun e suka fara rusa ko karya Daulolin mu (kingdoms and empires) kamar Daular Oyo, Benin, Etsekiri a kudu. A nan arewa kuma Daular Sokoto (Sokoto Caliphate). Bayan Turawan kamfani sun gama yin irin nasu zagon ƙasa, musamman kamfanin Royal Niger Company .Su kuma Turawan mulkin mallaka suka zo suka ƙarasa ruguza mu. Bayan sun rusa Daulolin kudu, sai suka dawo Arewa kan Daular Sokoto. A inda suka rinƙa yi masu ɗauki- ɗai-ɗai, daga shekarar 1900 suka dirarwa Bidda, da Kwantagora, da Keffi, sai Zariya 1902, Kano 1903 a ƙarshe Sakkwato 1903.

Bayan sun ci galabar mu, sai suka kafa wani mulki mai kama da baba –na ɗaka- gemu- na- waje ko kuma cinka –nan –kashin-can. Ma’ana Sarauniyar Ingila ita ce take mulki daga can Turai, amma kuma wakilinta ke aiwatar da umarnin ta. A shekarar 1914, sai aka ƙulla wani auren zobe (amalgamation), inda aka haɗe sashin kudu (Southern Protectrate) da sashin arewa (Northern Protectrate) a ƙarƙashin jagorancin Pedrict Lord Lurgard. Bayan ya haɗesu (kudu da arewa) sai matarsa Florence lurgard ta raɗawa Ƙasar sunan Nijeriya wanda ya samo asali daga kogin Kwara (River Niger).

Turawan Birtaniya sun gudanar da mulkin Nijeriya, ta hanyar tsarin mulkin mai shamaki (indirect rule). A inda yake a sama Turawa ne, a tsakiya zuwa ƙasa sarakunan gargajya. Kamar haka: gwamna janar, mai binsa Resdan daga shi sai D.O (District Officer).Dukkan waɗannan Turawa ne, daga baya aka ƙara D.D.O (Deputy Director Officer) wanda ake kira baƙin Bature. Bayan su sai kuma sarakunan mu kamar haka:

Sarkin yanka (Emir), Hakimi (District Head), sai Dagaci (Village Head) a ƙarshe Mai Unguwa (Ward Head). Haka wannan tsari ya gudana na tsawon shekara 60 ko fiye da haka.

Zama Da Maɗaukin Kanwa; Wannan irin dogon zama da aka yi, na shekaru masu yawa.Shi ne ya haifar da abubuwa da yawa da suka yi tasiri a kan rayuwar Bahaushe gaba ɗaya. Shi wannan irin tasirin kuwa, zamu iya karkasa shi zuwa kashi huɗu ko kuma su mutanen kamar haka:

1. Akwai mutanen da tasiri ya yi masu jirwaye suka yi dabbare- dabbar.

2. Akwai mutane da suka yi rabi da rabi kamar ragon uda ko akuya mai gefe rabi fari rabi baƙi.

3. Akwai mutane da suka yi baƙi-baƙi.

4. Akwai mutanen da suka rikiɗe gaba ɗaya sun yi baƙiƙƙirin. Sun ƙuna ba su gudun ƙauri.

Kowane daga cikinsu baya rasa dalili da ya sanya shi zama hakan;

i.                    Rukunin mutane na farko su basu yi boko ba, amma sun fi ‘yan bokon zaƙewa.

ii.                  Rukunin mutane na biyu, ana iya samun ‘yan boko zalla watau waɗanda suka yi karatun zamani kuma suka ɗauki ra’ayin boko, amma kuma suna gaurayawa da al’adunsu.

iii.               Rukunin na uku ,sune boko sana’a, suna cin moriyar ta amma ba su dulmiya ba.

iv.               Rukunin mutane na huɗu su ake kira boko aƙida, kuma tunanin su yafi na Bature, tun da su rayuwarsu ta yi ban –tafin- makafi da rayuwar Bahaushe da kuma musulmi.

A inda suturarsu da harshensu ba su ɗauke su da muhimmanci ba.Kai har da addini, al’ada da tunani, babu wani abu muhimmi, sai wanda Bature ya yi, ko ya faɗa. Ga masu irin wannan tunani na Nasara , maganarsu , rayuwarsu da tunaninsu duk na Bature ne.Farko dai, matarsu 1, ‘ya’ya 2-3,ga baƙar rowa kamar yaro ɗan yaye, ƙin zumunci kamar ɗan tsako, kare yafi ɗan uwa, farkarsa tafi matar aure.Ya san tarihin turai, bai san danginsa ba ko na Ƙasarsa. Ƙyale dala’ ilu ka ɗauki jarida. Jikinka na Kano zuciyarka a London, shi da makwabcinsa kuwa ba ruwan wani da wani(mahaukaci ya yi baƙo), jikinka baƙi zuciya ta Nasara. To wannan shi ne baƙin Bature, ɗan boko ne ko ba ɗan boko ba.

7.13 Yaƙi: Bahaushe na cewa yyaƙI mai ta da gidan gona. Tabbasa yaƙi kan yi sanadiyyar ɓarna ko asarar rayuka da na duukiya masu yawa. Manyan misalai su ne kamar yaƙin Duniya na ɗaya 1914 zuwa 1918, da yaƙin Duniya na biyu 1938 zuwa 1945, a nan gida kuma Nijeriya akwai yaƙin basasa 1966 zuwa 1970. Ɓarnar da waɗannan yaƙoƙi suka haifar ba kaɗan bane.

 8.0 Hanyoyin Riga-Kafin Ɓarna

Bisa nazarin bayanai da suka gabata ana iya cewa akwai wasu hanyoyin da za a iya yin riga-kafin aukuwar ɓarna. Da farko akan yi amfani da tsawatarwa ta hanyar yin Magana ga yara ko kuma faɗakarwa da gargaɗi ga manya. A wasu lokuta akan tanaji kwalbatoci, da magudanar ruwa don riga-kafin ɓarnar ruwa ko ambaliya. Akan tanaji abubuwan kashe gobara na gargajiya(addu’o’i da kafi ko kan gida) da na zamani, misali

 Alhaji Sani Aliyu Ɗandawo a waƙar Sarkin Maƙeran Yawuri yana cewa:

 Jagora:Sarkin Maƙeran Tukur,

 Gadagadan Alhaji.

Lawan mai maganin wuta,

kai ko gobara a kai,

Lawan bai zo ba,

In ya aiko macewa takai.

Akan yi dashen itatuwa don rage ƙarfin iska, haka kuma akan gyara rufin ɗakuna da bazara kafin faɗuwar damuna, saboda riga kafin ɓarnar iska.

Akan shirya ƙwanda a gona don hana ɓarnar yara.

Akan shirya mutum-mutumi a kai shi gona saboda riga-kafin ɓarnar dabbobi a gonaki.

9.0 Sakamakon Bincike:

Barna wata tsohuwar ɗabi’a ce da ta yi tasiri a al’ada Bahaushe da kowa ya yarda cewa kowa ya tarar ana gudanar da ita a Ƙasar Hausa. Duk da yake ba a son a aikata kuma ba a son mai aikatawar, har yanzu ana samun masu yin ɓarna. Saboda daɗewarta babu wanda zai ce ga wanda ya fara yenta, ko kuma a zamani kaza aka fara, wannan ya nuna cewa ɗabi’a ce a Ƙasar Hausa da ake gudanar da ita. Ba kuma a Ƙasar Hausa kaɗai aka yin ta ba, har da sauran sassan duniya. Duk da daɗewar da aka yi ana gudanar da ita, har yanzu ba’a daina ba. Wani abin mamaki kuma shi ne, ɓarna takan haifar da gaggarumar illa ga harkokin rayuwar Bahaushe da ma. Ga ɗan abin da bincike ya hararo akwai:

1. Tabbacin cewa, ɓarna kan auku bisa dalilai mabambanta, da kuma lokuta da wuraren da akan yi. Ɓarna ta zama ƙarfen ƙafa, wannan yasa Bahaushe ya kasa daƙile wannan harkar, saboda an zama tsumma da ƙwarƙwata ko kuma a ce mutu ka raba takalmin kaza.

2. Kasancewar barna tsohuwar al’ada ce ta gargajiya, ko kuma wata ɗabi’a da aka halicci ɗan Adam da ita, sannan kuma babu wanda ya san lokaci da mutumin da ya assasata, shi ya har yanzu ake samun jirwaye ko nasonsu a dukkan rassan adabin Bahaushe.

3. Bahaushe na cewa, tun ran gini, tun zane, ma’ana dai ɓarnar da harkokin rayuwa a Ƙasar Hausa gaba ɗaya, har ƙasa ta naɗe ba za a daina ba.

10.0 Shawarwari.

Dangane da shawarwari waɗanda ya kamata mu ɗauka su ne:

Bisa lura da bayanai da suka gabata, ana iya cewa an gani kuma an gamsu. Ɓarna wani aiki ne ko ɗabi’a mai matuƙar tasiri ga rayuwar Hausawa, saboda haka akwai buƙatar masana su ɗauki matakin fito tare da bayyana matsayinta a al’ada.

 Ya dace masana masu koyar da wannan Harshe na Hausa mu bai wa juna shawarar neman mafita. Musamman a kan irin waɗannan abubuwa da ake da ƙarancin bayanai game da su.

Akwai wasu abubuwa da yawa da suke buƙatar a fito da su don al’umma su ƙaru, kuma al’umma masu zuwa zasu yi alfari.

Akwai buƙatar yaƙar zuciya, da kuma cire ƙyuya mu zurfafa nazari a kan abubuwan da suka shafi al’adar Bahaushe. Mu daina raina ƙanƙantar abin da za a riƙa yin bincike akansa, ɗan abin da Allah Ya sa ka fito da shi, sai wani ya faɗaɗa tare da zurfafawa.

11.0 Kammalawa:

Ƙarshen tika-tika tik, komai yai farko, dole ne yai ƙarshe, don haka wannan tsokaci dangane da bayanai da suka gabata bisa ga nazarin ɓarna matsayinta, da tasirinta a rayuwar Bahaushe. Haƙiƙa an kawo bayanai masu dama da ka yi ƙarin haske tare da fito da irin kallon da ake yi wa ɓarna tare da nuna matsayinta a yanayin zamankewar Bahaushe. Da farko an kawo ma’anar ɓarna tare da ire-irenta, da fagagen da ake yinta, sannan da dalilan yinta, da lokutan aukuwarta ko aikatata, da wuraren faruwarta da kuma masu yinta. Tun daga mutane, da dabbobi, da tsuntsaye, da ƙwari da tsutsotsi da kuma wasu abubuwa marasa rai. Haka kuma an hararo irin yadda Bahaushe ya ɗauki ɓarna, muninta da kuma sakamakonta, tare matsayin masu yinta,

Bisa wannan dalili ne, yasa muka ɗan tsakuro wani abu daga cikin fage na al’adar Hausa, saboda ko ba a shafa ba maruru ya ɗara kaluluwa. Dukkan bayanan da muka yi, to ya zo ne a matsayin fitila abin haskawa da kuma jagora. Bahaushe dai yace; lomar hasafi tafi kaɓakin tsiya, ƙaramin goro yafi babban dutse, sai a yi haƙuri da abin da samu. Alhamdu lillahi.

Manazarta

Ayuba A.B (2015), Ƙamusun HausaNorthern Nigerian Publication Company,

 Zaria.

Bargery, G. F. (1993) A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary.Zaria: Amadu Bello University Press.

Bunza A.M.(2006) Gadon feɗe al’ada. Tiwel Nigeria Limited Surulere, Lagos.

 Ɗangambo A. (1984) Rabe-Raben adabin Hausa da Muhimmancinsa ga rayuwar Hausawa.Triunph Publication Kano.

Ɗangambo A.(1983) Kitsen Rogo. Triumph Publication Kano..

Ɗahiru B (2007) Tafsirin Watan Ramadan. Rediyo Najeriya Kaduna.

Imam A.(1937) Magana Jar ice na 1, da 2, da 3.Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Ƙamusun Hausa(2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano:Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

Madauci I.(1963)Al’adun Hausawa.Northern Nigerian Publication Company,

 Zaria.

Bello A.(1980)The Hausa Dialect Northern Nigerian Publication Company, Zaria.

Yahaya Y.I.(1988)Hausa A Rubuce;Tarihin Rubuce-Rubuce cikin Hausa.

Northern Nigerian Publication Company Zaria.

Ingawa A (1970) Iliya Ɗan Maiƙarfi. Northern Nigerian Publication Company,Zaria

Daura S A (1970) Tauraruwar Hamada. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Katsina D.U (1980) Kulɓa na Ɓarna. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ladan Y. (1980) Zaman Duniya Iyawa ne. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Ɗangogo (1970) Tabarmar Kunya. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Katsina M.S (1960) Uwar Gulma. Northern Nigerian Publication Company,Zaria.

Yahaya Y.I (1980) Tatsuniyoyi. Longman Press Ibadan

 




[1]Dubi Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabularyna Bargery, G. P. (1993) Ahmadu Bello University Zaria.Shf 89

[2] Encater Dictionary

[3]Newman (2020:109)

[4]Abraham, R. C. (1947)Dictionary of the Hausa Language,

[5] Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006),

[6]Bargery, G. P. (1934) a Hausa-English Dictionary & English Vocabulary London Oxford University Press.

[7]East da Imam (1949) a littafin Ikon Allah, Northern Nigeria Publication Company Zaria

[8] Hira da Malam Ashana Ɗankama Kano a Rediyon Jihar Kano 23/5/1998

[9] Dubi littafin Ka yi ta karatu na 4 (1972) Muhammadu Ingawa da Jean Boyd shf—37-38.

[10]. Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero (2006),

[11]Roxana MaNewman (1997) An English Hausa Dictionary.

[12]Bargery G.P.(1993)Ahmadu Bello University Press LTD.

 

Hausa Post

Post a Comment

0 Comments