Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Tamkar dai ka ce mai hali ba ya
sauya halinsa, ko kuma komai aka yi da jaki sai ya ci kara. A shekarar
2024 ma an sake fito da wasu nau’o’in kasuwanci wanɗanda
suke da zubi iri ɗaya da waɗanda aka yi bayani a sama. Ana kiran su da suna 52u da
kuma Anchor. Kasancewar zuwa lokacin kammala tattara bayanan wannan littafin ba
su bayyana a matsayin kasuwancin damfara ba, za a kawo bayanansu kawai a yadda
suke. Sannan za a kawo dalilan da suka sa aka sanya su a rukunin kasuwancin
damfarar duniyar intanet. Wannan zai taimaka wa makaranta wajen ƙoƙarin
bambance kasuwanci na haƙiƙa da na damfara yayin da aka zo musu da wasu nau’o’in
kasuwancin intanet a nan gaba.
52u
An fara gudanar da shi a shekarar 2024.
Kafar intanet da suke amfani da ita: www.52u.today
Tushe (a iƙirarinsu):
Malesiya
Manufa (a iƙirarinsu):
Yaƙi da talauci da kuma bunƙasa dogaro da kai.
52u yana da tsarin yin rajista. Matakan rajistarsa guda uku.
Yayin da mutum ya yi rajista, sannan ya biya kuɗi, to 52u za su ba shi aron jari
wanda za su saka masa a akawun ɗinsa domin gudanar da kasuwanci
da shi. Yawan kuɗin da za su saka masa, ya
danganta da matakin rajista da ya yi. Matakan rajistan su ne:
a. Basic – dalar Amurka ashirin ($20)
b. Silver – dalar Amurka hamsin ($50)
c. Gold – dalar Amurka ɗari biyu da hamsin ($250)
Ga yadda abin yake nan a kan kafar intanet ɗinsu:
Hoto Na 4.3: Matakan rajista a kafar 52u
Madogara: Kafar
intanet ta 52u (https://www.52u.today/index.php)
Duk wanda ya ya yi rajistar matakin Basic, to za su
ba shi dalar amurka ɗari uku da saban’in da biyar
($375). Wannan bashi zai tsaya a akawun ɗinsa ne, ba zai iya fita ba. 52u
ne za su yi amfani da kuɗin domin yi masa kasuwanci da
su. Kasuwancin an gina shi ne a kan na’urantaccen tsari (automatic). A bisa
haka, mutum ba ya buƙatar yin
komai. Kasuwancin da kansa zai gudanar da kansa.
A kowane wata mutum zai samu ribar da ta kai kimanin dalar
Amurka sittin da bakwai ($67). Da zarar ya fara samun wannan ribar, za a riƙa cire kuɗin da aka ba shi bashi (wato $375) har zuwa lokacin da zai
biya bashin duka. Idan ya kammala biyan bashi, to nan ne kuma zai fara cire
ribar domin cin gajiyarsu. Mafi ƙarancin
abin da za a iya cirewa shi ne dalar Amurka hamsin ($50).
Shi ma yana da tsarin gayyata. Duk wanda ya gayyato wani, to
zai samu kamasho. Kada a manta, duk wani kasuwancin damfara a kan intanet yana
da tsarin gayyata. Dalili kuwa shi ne, ana jifan tsuntsu biyu da dutse guda ta amfani da wannan tsarin. Da
farko zai taimaka wajen yaɗawa da tallata kasuwancin. Na
biyu kuwa zai taimaka wajen gina yarda, wato dasa yarda a zukatan mutane. Hakan
yana faruwa ne yayin da waɗanda suke ƙoƙarin gayyato mutane suka dage wajen yi musu bayanin tabbacin
alfanun da yake tattare da harƙallar.
Anchor
Shekarar Farawa: 2024
Kafar Intanet: https://anchorit.live
Harƙallar Anchor ta haɗa
abubuwa daban-daban. Da farko dai suna da tsarin rajista mai azuzuwa biyu. Wani
abu kuma shi ne, duk rajistar da mutum ya yi, akwai wata garaɓasa
da za a ba shi. Ga yadda abin yake:
Jadawali Na 3: Tsarin Rajistar Anchor
|
Tsari |
Kuɗin Rajista |
Garaɓasa |
|
Silver |
₦6,000 |
₦6,200 |
|
Pro |
₦8,500 |
₦7,500 |
Madogara: Tattaunawa[1]
Wani abin lura shi ne, mutum ba zai iya
cire garaɓasar da za a ba shi ba. A maimakon haka, za a ajiye su ne
a cikin akawun ɗinsa, har sai sun taru. Za su taru ne ta hanyar sauran
jinga da zai riƙa gudanarwa
a kan akawun ɗin. Wanda yake Silver sai kuɗinsa
sun kai naira dubu talatin da takwas (₦38,000)
kafin ya iya fitarwa. Wanda yake Pro kuwa, sai sun kai dubu arba’in da
takwas (₦48,000).
Jingar da ake gabatarwa suna da yawa.
Sukan kasance cikin tsarin wasannin kan intanet (online games) da kuma kallon
bidiyoyi da kuma tsarawa da ɗora bidiyoyin tallata harƙallar Anchor a kan intanet. Bayan haka, akwai nau’o’in
jingar da danna kansu kawai ake buƙatar yi.
Wanda yake Silver dole ne ya hau ya danna da kansa. Wanda yake Pro kuma,
kwamfuta za ta riƙa danna
masa. Sauran ɓangarorin da ake samun kuɗi
daga gare su sun haɗa da barin kuɗi masu yawa
a akawun ba tare da an cire ba, da shiga gasa da sauransu.
Bayan waɗannan,
akwai tsarin gayyata daraja-daraja. Idan mai darajar Silver ya yi gayyata, za a
ba shi naira dubu biyar da ɗari biyu (₦5,200). Idan Pro ne kuma, za a ba shi naira dubu bakwai
da ɗari biyu (₦7,200). Garaɓasar gayyata ana cire su ne a ranakun Litinin da Alhamis
daga ƙarfe tara zuwa goma sha ɗaya
na safe (9:00am – 11:00am). Mafi ƙarancin kuɗin
da mutum zai iya cirewa shi ne dubu goma (₦10,000).
Hannunka Mai Sanda
Akwai muhimman abubuwa da ya kamata a
lura da su dangane da 52u da kuma Anchor. Yana da kyau a lura da cewa, 52u da Anchor suna
da zubi da tsari ne irin na kasuwancin kan intanet na damfara da suka gudu da
kuɗaɗen
Hausawa a baya. Za a iya lura da cewa, duk nau’o’in kasuwancin kan intanet na
damfara suna ƙoƙarin yin amfani da “yarda” wajen
yaudarar mutane. Tsarin gayyata shi ne babban makamin gina yarda da suke amfani da shi.
An lura da cewa, kafafen intanet ɗinsu ba sa ɗauke da bayanan da ya kamata
kasuwancin gaskiya ya ɗauka. Kafar 52u (https://www.52u.today) kallonta kaɗai zai saka shakku a zuciyar
wanda ya san kasuwannin duniyar intanet. Kafar ba ta tsaru ba, ta yadda har
hoton shafin farko (homepage background image) ya ɓoye ƙunshiyar
kafar (menu bar).
Hoto Na 4.4: Hoton shafin farko na kafar 52u
ya ɓoye ƙunshiya (menu)
Madogara: Kafar
52u (https://www.52u.today)
Duka kafafen biyu ba su da bayanan tuntuɓa. Ko Anchor (https://anchorit.live) da ya kawo shafin, lambobin
WhatsApp kawai aka sanya guda biyu. A duba hotunan da suke ƙasa:
Hoto Na 4.5: A kafar 52u babu shafin tuntuɓa
Madogara: Kafar
intanet ta 52u (https://www.52u.today)
A wannan hoto da yake sama, za a iya lura da cewa wannan
kafar ba ta ɗauke da shafin tuntuɓa. Abin da suka gabatar kawai shi ne liƙau ɗin da zai kai mutane zuwa zaurensu da yake kan kafar sada
zumunta ta Telegiram. Wannan kuwa ba tsari ba ne na amintattun ‘yan kasuwa.
Amintattun ‘yan kasuwa na kan intanet suna bayyana cikakkun bayanan tuntuɓa, ciki har da imel da lambar wayar kamfani. Sukan kuma
sanya adireshinsu, wato inda za a iya tarar da su yayin da buƙatar hakan ta taso.
Hoto Na 4.6: Babu bayanan tuntuɓa a kafar Anchor
Madogara: Shafin
tuntuɓa a kafar intanet ɗin Anchor (https://anchorit.live/post/contact-us)
A wannan shafin tuntuɓa, za a iya lura da cewa ba a
gabatar da wuri takamaimai da za a iya samun jami’an wannan kasuwanci ba. Dangane da bayanan tuntuɓa, sun bayar da lambobin WhatsApp ne kawai. Layin waya kuwa
abu ne wanda za a iya jefar da shi a duk lokacin da aka ga dama.
Wani ƙarin
abin shi ne, duka kasuwancin biyu an tsara su bisa wani salon da ɗorewarsu zai yi wahala. Dalili kuwa shi ne, suna da riba mai
yawa wadda ba za a iya gamsasshen bayanin tushensu da ɗorewarsu ba.
Naɗewa
Wayewar zamani da ilimin da aka samu
dangane da wasu nau’o’in damfarar da aka yi a baya sun sa a yanzu ba a iya yin
nasara ta amfani da hanyoyin damfara na gargajiya ba. Duk da haka, ‘yan damfara a
kullum idanunsu a buɗe suke. A koyaushe sukan fito da
sababbin hanyoyin damfara, tamkar dai su ce wa al’umma “in kun iya ruwa, ba ku
iya taɓo ba.” Sannan
kuma a kusan kullum sukan samu sababbin shiga a cikin harkar intanet, ko dai
yara matasa ko kuma mutanen karkara da ilimin harƙallolin
intanet bai je musu da wuri ba, ko kuma marasa wayo da dabarun rayuwa da kuma
uwa-uba ‘yan son banza, waɗanda ake iya saran su kuma a cuce su, amma ba sa daddara.
Ya rage wa Hausawa su yi karatun
ta-nitsu dangane da duk wani sabon al’amari da zamani ya kawo wanda yake
da alamun tambaya. Wannan kuwa ko kaɗan bai
kamata ya zama dalilin gujewa duk wani cigaban da zamani ya kawo ba. Abin da ya kamata kawai shi ne a
yi bincike dangane da duk wani sabon ilimi domin wani zomon a sabara ake
barin sa.
[1] S. Muhammad (keɓantacciyar tattaunawa, 24 ga watan Nuwamba 2024)
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.