An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300
Sana’o’i Masu Alaƙa Da Zogale
Kalmar
sana’a ararriya ce daga harshen Larabci. Asalin kalmar a Larabci tana da
furucin assana’atu. A Larabci tana da ma’anar yin dabara ta yin
amfani da hikima da basira domin samar da wani abu, domin jama’a su amfana. Sani
da Aliyu (2026 sh. 23) sun bayyana sana’a a matsayin “hanyar amfani da fasaha
da hikima da kayan aiki domin sarrafa wani abu, musamman dangin albarkatu domin
samar da wani abun amfani da za a iya sayarwa ko musanyawa da wani abu mai
daraja, ko kuma gyara wani abun amfani da ya lalace ko tsaftace muhalli ko
jiki, ko gudanar da ayyukan samar da warakar jiki da gamsuwar zuciya domin
samun kuɗi ko wani
abu mai dajara kwatankwacin na kuɗi.”
A babukan
wannan littafi da suka gaba an tattauna a kan zogale a
matsayin magani da kuma abinci ko ƙwalama. Wani abin burgewa
shi ne, ko bayan waɗancan amfani da zogale yake da shi, yana da kuma wani ƙarin amfani da ya shafi taka rawa a ɓangaren tattalin arziki. A
wannan gaɓa ta littafin, an kawo wasu hanyoyin neman kuɗi da suke da alaƙa da zogale.
A ƙasar Hausa akwai gonaki da lambuna masu yawa na zogale. Masu
wannan sana’a sukan shuka itatuwan zogale masu yawa. Har da rani sukan yi musu
bayin ruwa domin su ci gaba da yin tofo yadda ya kamata. Wani lokaci
sukan yi feshin maganin ƙwari idan akwai buƙatar hakan.
Mutane
sukan je ire-iren waɗannan gonakai ko lambuna domin sayen ganyen zogale. Akan samu wasu
masu lambuna da sukan fitar da zogalensu har zuwa ƙasashen ƙetare, inda suke samun riba
mai gwaɓi. A
kasuwannin duniya, man ‘ya’yan zogale da kuma garin ganyen zogale duk abubuwa
ne masu daraja, waɗanda kuma suke kawo riba sosai.
Kamar
yadda aka kawo a shafin Trade Facilitator (2026), kilogiram ɗaya (1 kg) na man ‘ya’yan
zogale a kasuwar duniya yana kai farashin dalar Amurka goma sha biyar zuwa
arba’in ($15 - $40). A kuɗin Nijeriya, ya kai kimanin dubu ashirin da biyar zuwa dubu sittin
(₦25,000
- ₦60,000).
Garin ganyen zogale ma yana da daraja a kasuwar duniya. Kilogiram na garin
zogale yakan kai dalar Amurka uku zuwa dala takwas ($3 - $8). Wannan ya kama
kusan naira dubu biyar zuwa dubu goma sha biyu (₦5,000 - ₦12,000). Haƙiƙa wannan hanyar samun kuɗi ce wadda kuma take taka rawa wajen taimaka wa tattalin arziki.
Ganye, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye
na jinsin maza. Jam’in kalmar kuwa shi ne ganyaye, ko kuma ganyayyaki a
wani ƙarin
harshen. Kalmar tana ɗauke da ma’anar: “Tohon da ke fitowa a
jikin reshen bishiya, yakan zama mai faɗi ko
siriri” (BUK, 2006: sh. 157). A wannan gaɓa ana
magana ne game da ganyen zogale.
A sama
(a ƙarƙashin 4.2.2) an nuna yadda masu gonaki ko lambunan zogale suke
sayar da ganyen ga al’umma. Ko bayan su, akwai ‘yan gwari a kasuwanni da
suke sayar da ganyen zogale. Wasu sukan haɗa su a cikin kayan gwarinsu, dangin tumatur da tattasai da albasa
da sauran ganyaye irin su yakuwa da alayyaho da sauransu. Wasu kuwa ganyen
zogalen kaɗai suke
sayarwa, wanda kuma ita ce sana’ar da suka shahara da ita. Za su sayo ganyen
sannan su zo su kasa domin samun riba.
Darajar ganyen zogale yana
da alaƙa
da ɗimbin alfanun da yake da shi a fannin magunguna.
A ƙasa an
kawo taƙaitattun
misalai:
a. Ciwon Kai: Idan
ana ciwon kai, za a iya tsigo ɗanyen
ganyen zogale a murtsika shi, sannan a shafa a goshi. Cikin yardar Ubangiji, za
a sami sauƙin ciwon
kan.
b. Olsa da Zawo (Gudawa): Tafasa ganyen zogale domin yin shayi a sha yana taimakawa
wajen magance ciwon olsa da kuma zawo.
c. Ƙarancin Jini: Ana amfani da ganyen zogale domin magance ƙarancin jini, musamman a ƙasar Philippines. A can, ana dafa ganyen ne a
ci, sannan kuma a sha ruwan da aka dafa shi da shi.
d. Gudawa: A ƙasar Malawi kuwa, suna amfani da busasshen
ganyen zogale ne wajen maganin gudawa.
e. Tsayar da
Jinin Rauni: Yayin da wani sashe
na jikin mutum ya samu rauni, har aka samu zubar jini, sai a tsigo ɗanyen ganyen zogale a murza
shi sosai, sannan a matsa ruwan a wajen raunin. Da izinin Allah, jinin zai
daina zuba. (Fahey, 2005)
A ɓangare ɗaya kuwa, mata daga cikin
gida sukan ɗora wa yara tallar ganyen zogale. Za a kasa shi kashi-kashi a bisa
tire ko cikin tasa ko baho. Mai tallar za ta riƙa bi
gida-gida tana talla da furucin:
Mai
Talla: Assalamu alaikum, ga
talla/talle.
Masu
Gida: Wa’alaikumussalam, tallan
me (tallen me)?
Mai
Talla: Tallan zogale
Wani
lokaci kuma mai tallan za ta gabatar da furuci kamar haka: “Assalamu alaikum ga
tallan zogale.” Masu gidan za su kira mai tallar idan suna buƙata. Idan ba sa buƙata kuwa za su sallame ta
domin ta yi gaba. Akan kira ta da furucin: “Kawo mu gani”, ko “Kawo
mu saya.” Ida kuwa ba a buƙata, akan sanar da ita da
furucin: “Allah ya ba da sa’a,” ko kuma “Ba za mu saya
ba.” Haƙiƙa wannan ma hanya ce ta samun kuɗi ga masu sana’ar.
Akan dafa
zogale sannan a riƙa sayar da dafaffen ganyen. Wannan yana daga cikin misalan ƙananan jaura da Hausawa suke gudanarwa. Yayin sayarwa, akan yi
masa haɗi
da ƙuli/ƙarago da albasa, wani lokaci har da kayan almbu dangin su tattasai
da tumatur. Rukunonin mutanen da suke cin gajiyar wannan sana’a sun haɗa da:
1. Mata
sukan dafa a gida sannan su ɗora wa yara talla. Yaran sukan bi gida-gida ko titi-titi ko
wuraren zaman jama’a domin talla.
2. ‘Yanmata
sukan yi irin wannan jaura da kansu. Sukan sayo ganyen zogale, su gyara, su
dafa, sannan su fita domin sayarwa.
3. Akan samu
maza masu irin wannan talla na ganyen zogale inda wani lokaci sukan tura a
cikin baro. Duk wanda ya saya za su saka masa kayan haɗi domin ci.
4. Wasu kuwa
sukan dafa ne sannan su zauna nan cikin gidajensu. Da ma sun yi fice a wannan
jaura. Masu buƙata za su riƙa zuwa ko su aiko domin a
saya musu.
5. Akwai
kuma waɗanda suke
buɗe wurare
na musamman domin sayar da zogale, ko kuma su saka shi a matsayin ɗaya daga cikin nau’ukan
abinci da ake sayarwa a gidan abincin.
6. Mata
tsofaffi ma sukan dafa zogale tare da kaiwa kasuwa domin sayarwa. A kasuwannin
wasu garuruwa na ƙasar Hausa kamar Sakkwato
da Zamfara, akwai wurare na musamman da suka kasance fitattu inda ake samun
dafaffen zogale na sayarwa.
Za a iya
tuna wata fitacciyar waƙar da Dauda Adamu Kahutu Rarara ya yi wa wata mai irin wannan sana’a na sayar da
zogale. Ga tsakure daga cikin waƙar:
Bayarwa: Fatima mai zogale!
Amshi: Fati, Fatima, Fati adon gari.
Bayarwa: Kin wuce ai daƙile.
Amshi: Fati, Fatima, Fati adon gari.
Bayarwa: Kin yi kamar labule, a’ah.
Amshi: Fati, Fatima, Fati adon gari.
Bayarwa: Sa mini in dangwale.
Amshi: Fati, Fatima, Fati adon gari.
(Dauda Adamu Kahutu Rarara: Fatima Mai Zogale)
Wata hanyar samun kuɗi da take da alaƙa da zogale ita ce sayar da busasshen ganyen zogale. A kasuwannin garuruwan ƙasar Hausa akan samu busasshen ganyen zogale. Akan saya a gyara
sannan a yi miya da shi ko a kwaɗa (ɗatu) domin a ci.
Wannan yana nuni da cewa, yayin da aka ciro ganyen zogale, to ba zai zama hasara ba. Ko da ba a samu damar amfani da shi ko sayar da shi ba, to za a iya shanyawa domin ya bushe. Haka kuma, za a iya amfani da busasshen ko a sayar da shi domin samun kuɗi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.