Ticker

6/recent/ticker-posts

Abubuwan Da Suke Janyo Hasara a Harkokin Kirifto

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

‘A Ci Wawa A Watse’ Cikin Sigar Kirifto

Shimfiɗa

Akwai salo-salo na damfara da ake yi cikin sigar kirifto da kuɗin intanet (crypto and cryptocurrency) waɗanda suka rufe da kuɗaɗen Hausawa. Yawanci akan fito da su ta tsarin haƙo (mining) ɗin wani nau’in kirifto. Daga ƙarshe sai a buƙaci a sanya kuɗin kasuwanci a kan bulokcen (gas fee). Yayin da aka saka, sai kuma su yi ɓatar dabo, ko kuma su fito da wani farashin da ko kuɗaɗen da mutane suka saka ba za su iya fanshewa ba. Wani lokaci kuwa sukan fito da ƙa’idoji masu tsauri. Ta haka sai su yi wa mutane kora da hali wanda ya fi kora da sanda.

A waɗansu nau’o’in kirifto ɗin kuwa, akan fara hadahadar kasuwar somin-taɓi (pre-market) da farashi mai daraja. Wannan zai sa mutane masu yawa su sanya kuɗaɗensu domin sayen kififton. Yayin da aka ƙaddamar da shi (launching) kuwa, sai ya fito ba tare da wata daraja ba. Hakan zai haifar wa mutane hasara mai yawa. Akan kuma samu kirifton da bayan mutane sun raja’a a kansu, sai a cire musu ‘uwar kuɗi’[1] (liquidity). Wannan zai sa su kasance ba tare da wata daraja ba. Hasali ma, kirifto ɗin da ba shi da uwar kuɗi, ba za a iya kasuwancinsa ba.

Akwai Hausawa masu yawa da suka faɗa tarkon ire-iren waɗannan nau’o’in damfara. Wannan babin ya kawo wasu daga cikinsu tare da bayanan yadda suka kasance. Ana kyautata zaton hakan ya kasance faɗakarwa da hannunka-mai-sanda ga Hausawa. Ko da ma dai, gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

Sabubban Hasara a Harkokin Kirifto

Akwai dalilai da dama da suke janyo hasara ga waɗanda suka shiga harkar kirifto. Waɗansu daga ciki sukan zo ne kawai a matsayin yanayin kasuwa. Ma’ana sukan kasance ko dai jarrabawa daga Allah ko kuma sakamakon wani kuskure da ɗan kasuwa ya yi. Ko a nau’o’in kasuwancin duniyar zahiri akan samu hasara daga lokaci zuwa lokaci. Wasu nau’o’in kasuwanci sun fi wasu haɗarin hasara. Misali, safarar kayan lambu dangin tumatur da tattasai da attaruhu yana daga cikin kasuwancin Hausawa waɗanda suke tattare da haɗarin hasara. Wannan ne ma ya sa ake yi masa laƙabi da gwari.[2]

Hasara da ake samu a harkar kirifto sakamakon kuskure ko gangancin ɗan kasuwa takan auku yayin da ya aikata wani lamari da ya saɓa wa dokoki da ƙa’idojin kasuwanci. Ana iya samun hasara sakamakon ɗaya daga cikin waɗannan:

a. A yayin da ɗan kasuwa ya shiga harkar kirifto ba tare da neman cikakken ilimin yadda lamuran suke gudana ba.

b. A yayin da ɗan kasuwa ya ƙi karanta dokoki da ƙa’idojin kasuwanci da ake sabuntawa a kafafen cinikayyar kuɗaɗen intanet.[3]

c. A lokacin da aka ƙi bin zayyanannun dokoki da ƙa’idojin kasuwanci da aka shata, ko aka kuskure wasu matakai.

A ɓangare ɗaya kuwa, hasara a kasuwancin kuɗaɗen intanet takan auku ne a sakamakon damfara ko zamba daga mamallakan nau’in kuɗin ko kuma wasu gungun mutane. A ƙasa an kawo wasu hanyoyi da dalilai da za su iya haifar da hasara a hadahadar kirifto.

1. Riƙewa (Holding)

Riƙewa tsari ne a inda masu kirifto ko wasu gungun ‘yan kasuwa suke sayen adadi mai yawa na wani nau’in kuɗin intanet su ajiye. Hakan zai sa ya yi ƙaranci a kasuwa. Ƙarancin nasa kuma zai saka shi ya ƙara daraja da tsada. Da zarar kuɗin intanet ya yi daraja, hankalin ‘yan kasuwa musamman masu ƙarancin ilimi a fannin zai karkata gare shi. Daga nan za su yi ta sayen sa da nufin samun riba. A wannan gaɓar ne kuma masu baƙin nufin da suka ‘riƙe’ adadi mai yawan da suka saya za su sayar da shi. Za su ci riba mai yawa yayin da kai-tsaye darajarsa za ta karye a kasuwannin hadahadar kuɗaɗen intanet. Hakan yana nufin cewa duk waɗanda suka shiga daga baya za su yi hasara.

2. Cire Uwar Kuɗi (Liquidity)

Darajar kowane kuɗin intanet yana dogara sosai a kan uwar kuɗin duniyar zahiri da aka sanya masa. Kuɗin da aka sanya masa ne zai bayar da damar yin kasuwancinsa a kowane lokaci. Masu damfara ta hanyar kirifto suna iya fito da wani nau’in kuɗin intanet sannan su saka masa uwar kuɗi mai yawa. Wannan zai sa ya samu karɓuwa a tsakanin al’umma. Bayan mutane sun raja’a a kansa ta hanyar ɓata kuɗaɗe da lokacinsu, daga baya sai a cire uwar kuɗin da aka saka masa. Hakan zai sa darajarsa ta faɗi ƙasa warwas.

3. Ɓatar Dabo

‘Yan damfara suna iya fito da wani nau’in kuɗin intanet wanda za a yi haƙo. Yayin da tafiya ta yi tafiya, za su buƙaci a saka kuɗin kasuwanci a kan bulokcen (gas fee). Da zarar mutane sun saka, za a nemi masu wannan kuɗin intanet a rasa. Hakan yana nufin sun damfari mutane sun gudu.

Tsokaci

A bisa bayanan da suka gabata, yana da matuƙar muhimmanci Hausawa su karanci yadda kasuwancin kuɗaɗen intanet suke gudana kafin su shiga. Wannan ya haɗa da koyon yadda ake nazartar alƙaluman da suke nuna hawa da sauƙar farashin kuɗaɗen intanet a kasuwannin duniya. Hakan zai bai wa ɗan kasuwa damar fahimtar yanayin hawa da sauƙar farashin. Yayin da yake da wannan ilimi, ko da ya ga farashin wani nau’in kuɗin intanet ya sauƙo, ba zai yi saurin saye ba da tunanin cewa farashin zai tashi daga baya. A maimakon haka, zai nazarci lamarin sosai kafin saka kuɗaɗensa.

Bugu da ƙari, ilimin kasuwancin kuɗaɗen intanet zai bai wa ɗan kasuwa damar nazartar sababbin kuɗaɗen da sukan shigo kasuwa. Zai iya amfani da alƙaluma daban-daban domin fahimtar waɗanda ya dace ya mayar da hankali a kansu da kuma waɗanda ba su da alƙibla nagartacciya.

Akwai Hausawa masu yawa da suke ƙara zurfafa ilimi a wannan fanni na kasuwancin kuɗaɗen intanet. Hasali ma, akwai Hausawa waɗanda suka buɗe makarantun koyar da wannan nau’in kasuwanci. Wasu masu yawa kuma suna koyarwa ko fitar da bayanai cikin bidiyoyi da rubuce-rubuce a shafukansu na sada zumunta da sauran kafafen intanet.

Sunusi Danjuma Ali tasha yake da ita a kan YouTube mai suna SunusiCryptoTV. Ya zuwa 10 ga watan Octobar shekarar 2024, kimanin mutane dubu ashirin da huɗu da ɗari ɗaya (24,100) ne suke bibiyar wannan tashar tasa. A duba hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 5.1: Tashar Koyar Da Hadahadar Kuɗin Intanet a Kan YouTube

Abubuwan Da Suke Janyo Hasara a Harkokin Kirifto

Madogara: https://www.youtube.com/@SunusiCryptoTV/videos

Ya zuwa ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2025, wannan adadi ya haura zuwa kimanin dubu arba’in da bakwai da ɗari bakwai (47,700). Wannan yana nuni ga yadda mutane suke ƙara bibiyar abubuwan da yake ɗorawa a wannan kafar tasa. A duba hoton da yake ƙasa:

Hoto Na 5.2: Bunƙasar Tashar Koyar Da Hadahadar Kuɗin Intanet a Kan YouTube

Abubuwan Da Suke Janyo Hasara a Harkokin Kirifto

Madogara: https://www.youtube.com/@SunusiCryptoTV/videos

Ƙarin misalai na Hausawa da suke koyarwa ko gabatar da laccoci na musamman game da kuɗin intanet sun haɗa da:

a. Abdul Kabo: Yana koyar da abubuwa daban-daban da suka shafi kasuwancin duniyar intanet. Sunan Tasharsa a YouTube Abdulkabo Tech (https://www.youtube.com/@Abdulkabo__tech)

b. Aminu Sirajo: Sunan Tasharsa a YouTube Aminu Tech (https://www.youtube.com/@aminutech)

c. Injiniya Mujahid Muhammad Manga: Ya shahara wurin gabatar da laccoci a shafinsa da yake kan kafar TikTok. An fi sanin sa da suna Abumaher.

d. Umar Isma'il Muhammad: Shi ne yake da tashar Umar Top TV YouTube (https://www.youtube.com/@umartoptv).

e. Yusufuddee. A. Yusuf: Shi ne yake da tashar YDEEN a YouTube (https://www.youtube.com/@iam_ydeen/videos).

Makarantun Hausawa na koyar da hadahadar kuɗaɗen intanet waɗanda suke azuzuwa a duniyar zahiri sun haɗa da:

a. Arewa Trading Academy[4]

b. HydarFX Academy Kano[5]

c. SMT Academy Kaduna[6]

Hoto Na 5.3: Wasu Ɗalibai a Ajin Koyon Hadahadar Kuɗin Intanet a Makarantar Arewa Trading Academy

Abubuwan Da Suke Janyo Hasara a Harkokin Kirifto

Madogara: https://www.tiktok.com/@yahaya_crypto




[1] Uwar kuɗi (liquidity) shi ne kuɗaɗe ko hannayen jari da ake sakawa a harƙallar wani kirifto. Yayin da kirifto yake da uwar kuɗi mai yawa, hakan ne zai sa ya kasance mai daraja a kasuwannin duniya na hadahadar kirifto.

[2] Akan yi masa kirari da “gwari ba kuɗi ba sai an sai da.”

[3] Harkar kasuwancin kuɗin intanet ba ta rago ba ne. Dole mutum ya kasance yana biyar bayanai da ake sabuntawa, sannan yana karanta su tiryan-tirya.

[4] Za a iya duba su a https://www.tiktok.com/@yahaya_crypto.

[5] Za a iya duba su a https://www.tiktok.com/@hydarfx.

[6] Kafar intanet ɗinsu ita ce: https://smtacademy.org/index.html.

Manazarta: 

Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments