Ticker

6/recent/ticker-posts

Dambun Zogale

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Zogale a Mahaɗin Ƙwalama Da Abinci

Zogale a farfajiyar ƙasar Hausa ya kasance wani muhimmin mahaɗi na abinci da ƙwalama. A ƙarnukan da suka shuɗe, zogale ta kasance abin ƙwalama a ƙauyuka da birane. Hasali ma, ta zamanto tushen inganta tattalin arzikin al’ummar da suke noma ta a fadamunsu. Hakan yakan ba su damar dafa ta, su kai garuruwa da biranen da suke kusa da su domin sayarwa. Mazauna garuruwa sukan saye ta ne domin ci a matsayin abin marmari a wani ƙayyadajjen lokaci. Sauyawar zamani ya wanzar da har ana sayar da ɗanyen ganyen zogale a fadamun da aka shuka ta a matsayin danga da aka zagaye gonakin fadamar da ita, domin kariya daga ɓarnar dabbobi.

Akan sarrafa zogale ta mabambantan hanyoyi domin marmari (ƙwalama) ko kuma abinci a sassan ƙasar Hausa. Yadda ake sarrafawar shi ma ya sha bamban dangane da zarafin al’ummar. Ana yin abubuwa da dama da ita da suka haɗa da:

a.  Dambun zogale

b.  Faten zogale

c.  Kwaɗon zogale

d.  Miyar zogale da dai sauran abubuwan marmari (ƙwalama).

Dambun Zogale

Kalmar dambu tana cikin jerin kalmomin Hausa jinsin sunayen maza. Kalmar tana ƙunshe da ma’anoni kamar:

(i)  Abincin da ake yi ta hanyar turara garin hatsi a haɗa shi da ganyen rama ko zogale da albasa da sauransu.

(ii) Duk abinci mai kama da wannan, kamar:

·  Dambun kifi

·  Dambun nama (BUK, 2006 sh. 93).

A nan an nuna cewa, ana aiwatar da dambu ne ta amfani da hatsi a cukuɗa shi da ganye. Ke nan wannan manuniya ce da take ishara da cewa al’ummar Hausawa suna yin dambu da rama tun kafin bayyanar zogale a farfajiyar ƙasar Hausa.

Shi kuwa Abubakar (2015 sh. 92) ya bayyana shi da: “Abincin turararren gari ko tsaki, hautsine da ganyaye da albasa da kuma mai. A ma’anar Garba (1990 sh. 35) da Abraham (1975 sh. 181) sun bayyana shi da cewa: “ Gari da albasa da yakuwa da aka dafa gaba ɗaya. Ba abin mamaki ba ne, a ji sun bayyana dafawa a madadin turarawa saboda rashin zaman su Hausawa. Wannan ne ya sa suka kasa bambantawa tsakanin turarawa da dafawa.

A al’adar ƙasar Hausa ana yin dambu ne da tsakin dawa ko ɓarzajjen gero ko masara ko shinkafa. Abin la’akari a nan shi ne, kafin yawaitar masara da shinkafa a tsakanin shekarun 1970 har zuwa 1975 manoman ƙasar Hausa ba su mayar da hankalinsu ga noman masara ba. In ma an noma, an yi ne domin cin marmari. Ita ma shinkafar ba ta yawaita ba sai da aka soma shigowa da ita daga ƙasashen waje. A bisa wannan dalili, ɓarzajjen gero da tsakin dawa ne aka fi amfani da su. Hasali ma na gero ya fi garɗi da sa lafiyar jiki.

Yadda Ake Dambun Zogale

Yayin da ake buƙatar yin dambun zogale, za a ɗora madambaci a turara tsakin da aka tanada. Daga nan za a samu ganyen zogale mai yawa da zai isa a yi dambu da shi, tare da gyaɗa ɗanya da kayan ƙamshi idan da hali, da albasa gwargwadon buƙata da zarafi da gishiri da magi.

Lokacin da aka ga tsakin ya turaru, sai a juye a wani wuri mai kyau da tsabta, a yayyafa ruwa domin ya yi wara-wara (wasar). Daga wannan matakin ne za a zuba zogale da gyaɗa ɗanya da kayan ƙamshi, da albasa da gishiri da magi, a hautsine su sosai. Za a sake mayarwa cikin madambacin a sake turarawa a karo na biyu. Da zarar ya nuna shi zai nuna alama, ta hanyar tashin ƙamshinsa. Daga nan za a zuba toyayyen/soyayyen man shanu ko man gyaɗa. Ana yin sa ne domin cin marmari da rana (Bayero, 2007 sh. 216-7) da (Umar, 1985 sh. 56). 

Post a Comment

0 Comments