Ticker

6/recent/ticker-posts

Faten Zogale Da Kwadon Zogale (Datu)

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Faten Zogale

Kalmar fate tana cikin jerin kalmomi jinsin sunaye na maza. Tana ɗauke da ma’anar: “Wani irin abinci da ake yin sa ruwa-ruwa wanda ake haɗa shi da tsaki da yakuwa (sure) ko da garafuni (garahuni) ko da albasa da wake, wani lokacin kuma har da nama, daidai da gaddama ko meye-meye, ko fate (BUK, 2006 sh. 138). Abraham (1975 sh. 260) ya bayyana cewa, ana kiran shi meye-meye a karin harshen Sakkwatanci. Ya kasance abinci mai siffar kakkaurar miya da aka yi da ganyaye, ‘ya’yan itace, gari ko tsaki da maiƙo dangin mai.

A farfajiyr ƙasar Hausa, akan yi fate ne da tsakin dawa, ko na masara, ko shinkafa, ko na alkama. Akan zuba wake da kabewa (guro, ko goji, ko kabushi). Akan sanya ganyen zogale a madadin yakuwa ko alayyaho. Masu wadata sukan saka nama ko busasshen kifi.

Ana yin wannan abincin ne a matsayin na marmari (ƙwalama). Hasali ma da rana ake yin sa. Mawadata sukan yi shi a lokacin bukukuwan suna da aure. Yakan buƙaci ganyen zogale mai yawan gaske, wadda ta fi alayyaho da yakuwa (sure) tsada da wahalar samu.

Kwaɗon Zogale (Ɗatun Zogale)

Kalmar kwaɗo tana cikin jerin kalmomin Hausa jinsin sunaye na maza. Tana ƙunshe da ma’anoni kamar haka:

a.   Haɗa daddawa ko ƙuli-ƙuli da gishiri da ɗan ruwa da dafaffen ganye a cakuɗa a ciki.

b.   Aikin wauta, daidai da soki-burutsu.

c.   Duk abincin da aka yi haɗe-haɗen abubuwa da yawa wuri guda kamar salak (BUK, 2006 sh. 260).

A karin harshen Sakkwatanci akan kira shi da lafazin ɗatu. Abubakar (2015 sh. 282) ya bayyana kwaɗo a matsayin: “Abincin da aka haɗa shi aka gauraya da daddawa, ƙuli-ƙuli, ko mai ko kuma da ganye ko wasu dakakkun ‘ya’yan itace.

Ana yin kwaɗon dafaffiyar zogale da dakakken ƙuli-ƙuli ko tunkuzar gyaɗa (labu a karin harshen Sakkwatanci). A wani karin harshen kuwa akan kira shi cakina. Za a zuba ruwa kaɗan a dama ƙuli-ƙulin ko labun, sai a zuba dafaffiyar zogale a cakuɗa. Idan ana buƙata, akan haɗa da yankakkiyar albasa da tumatur da koren tattasai.

A wasu sassan ƙasar Hausa kuwa akan haɗa zogale da ɓula ko hoce ko tuwo ko ƙanzo ko jiƙaƙƙen garin-rogo ko dafaffiyar shinkafa. Akan kuma turara zogale, a kwaɗanta da garin ƙuli-ƙuli da gishiri da sukari a ci. 

Hoton Kwaɗon Zogale

Hoton Kwaɗon Zogale

Post a Comment

0 Comments