Ticker

6/recent/ticker-posts

Sayar Da Sassan Zogale a Matsayin Mahadin Magani

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

Sayar Da Sassan Zogale a Matsayin Mahaɗin Magani

Wata hanyar samun kuɗi da zogale ita ce sayar da sassan itaciyar. Yawanci akan sayi waɗannan sassa domin sarrafa su wajen haɗa magunguna daban-daban. A babi na biyu na wannan littafin, an tattauna zogale a matsayin magani. A ƙarƙashin babin, an nuna nau’ukan magunguna daban-daban da ake iya haɗawa ta hanyar amfani da sassan zogale. Wannan ne kuma ya sa sassan suka kasance masu matuƙar daraja da har ake samun kuɗi ta hanyar sayar da su. Daga cikinsu akwai:

a. Furen zogale

b. Kwasfar zogale

c. Garin zogale (dakakke)

d. Ƙwayar zogale (‘ya’yan zogale)

e. Man ‘ya’yan zogale

f. Sassaƙen zogale

g. Ƙaron zogale

h. Saiwar zogale (jijiyar zogale)

A ƙasa an tattauna a kan amfanin wasu daga cikin waɗannan.

1. Furen Zogale

Ana sayar da furen zogale saboda amfanin da yake da shi a fannin magunguna. Fure, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin maza. Jam’in kalmar kuwa shi ne furanni. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Hudar bishiya ko wani tsiro kafin ‘ya’ya”. A wani karin harshe kuwa, ana kiran sa da lafazin hure, kamar yadda BUK (2006: sh. 144) suka nuna.

Ga ‘yan misalai na magununan da ake haɗawa da furen zogale:

a. Inganta Nono: Ana dafa furen zogale a rinƙa shan ruwan. Yin haka yana ƙara ingancin nono tare da samar da wadataccen ruwan mama ga mata masu shayarwa.

b. Maganin Rashin Yin Fitsari: Shan ruwan dafaffen fure yana da matuƙar muhimmanci wajen kawar da matsalar rashin yin fitsari, saboda shan ruwan yana sanya mutum ya yi fitsari cikin sauƙi.

c. Maganin Sanyi: A ƙasar Haiti, mutanen ƙauyuka suna tafasa furen zogale suna shan ruwan domin maganin sanyi (Rajangam, 2001).

2. Kwasfar Zogale

Kwasfa, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin mata. Kalmar tana ɗauke da ma’anar: “Ɓawo ko kwamɓori ko kwalfa”, kamar yadda BUK (2006: sh. 267) suka nuna. Kwasfar zogale a nan ana nufin abin da ake ɓarewa daga jikin ‘ya’yan zogale.

Cin ɗanyar kwasfar zogale yana magance matsalar ciwon zuciya, saifa, tare da ciwon gaɓoɓin jiki, kamar yadda Ramachandran da wasu (1980) suka nuna.

3. Ƙwayar Zogale (‘Ya’yan Zogale)

Ƙwaya, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin mata. Jam’in kalmar kuwa shi ne ƙwayoyii ko ƙwayayaki. Kalmar tana ɗauke da ma’anar ƙanƙanen abu mai nau’in hatsi, kamar su gero, wake, dawa, masara, ko makamantansu. A wannan fagen kuwa, ƙwayar zogale fara ce. Girmanta kuma ya kai na wake. Idan aka sami zangarniyar zogale aka ɓare ta, za a tarar da ‘ya’yan zogale a ciki; yayin da aka ɓare su ne za a sami ƙwaya ƙarama wadda ake bayani a kanta. Ita ma tana da nata muhimmancin a fagen magani kamar haka:

a. Kashe Ƙwayoyin Cuta: Ana amfani da ita wajen kashe ƙwayoyin cuta da suke haifar da lahani a cikin jikin ɗan’adam. Wato, tana matsayin makashiyar ƙwayoyin cuta (antibiotic). Hasali ma, tana maganin kumburi.

b. Ciwon Gaɓoɓi da Cututtukan Jima'i: Ana amfani da ita wajen maganin amosanin gaɓa, ƙaban ƙashi, ciwon burdu, sandarewar gaɓa (wanda a wani karin harshe ake kira muƙyuyaciya), da sauran cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima’i. Za a soya ƙwayoyin irin zogalen ne, a kirɓa su tare da man kwakwa, sannan a rinƙa shafawa a wajen da yake ciwo.

c. Maganin Farfaɗiya da Fitsari: Cin soyayyar ƙwayar irin zogale da shan manta yana taimakawa wajen magance matsalar rashin yin fitsari. Haka kuma, yana magance ciwon farfaɗiya cikin ikon Allah.

d. Cututtukan Fata: Niƙaƙƙiyar ƙwayar zogale ana amfani da ita wajen maganin ƙazuwa da sauran cututtukan fatar jiki. (Gopalan da wasu, 1989)

4. Saiwa Da Sassaƙe Da Ƙaron Zogale

Saiwa, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin mata. Jam’in kalmar kuwa shi ne saiwowi ko saiwu ko kuma saiwoyi a wani ƙarin harshen. Haka kuma, ana kiran ta da lafazin tushe ko gindi ko jijiya. Kalmar tana ɗauke da ma’anar: “Sashen tsiro yawanci mai rarrabuwa da kuma gashi da ke binne a ƙasa, wanda ke nemo da kuma tsotso wa tsiro abinci domin toho, girma, da ci gaba da rayuwa” (Abubakar, 2015: sh. 422).

Yayin da aka dawo kan kalmar sassaƙe kuwa, kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin maza, jam’inta kuwa shi ne saƙe-saƙi ko sassaƙe-sassaƙe. Kalmar tana ƙunshe da ma’anar: “Ɓawon itace”, musamman wanda ake yin magani da shi (BUK, 2006: sh. 393). Duk da haka, sassaƙen itaciya bai tsaya ga ɓawonta kawai ba. Yayin da ake sassaƙa, ana iya ɗauko har da jikin nata. A wasu lokuta ma ba ɓawon ake buƙata ba. Ana buƙatar a sassaƙo asalin jikin nata ne.

Ƙaro kuwa kalma ce ta Hausa da take cikin rukunin sunaye na jinsin maza. Kalmar tana ɗauke da ma’anar: “Wata ɗarɓa mai ɗanƙo wadda take fitowa a jikin bishiya ta daskare.” A wani karin harshen kuwa, ana kira ta da lafazin jirai (BUK, 2006: sh. 277).

Waɗannan sassan jikin na zogale suna taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin rashin lafiyar da suke addabar ɗan’adam. Ga ‘yan misalai:

a. Maganin Ciwon Zuciya da Kumburi: Ana amfani da saiwar zogale da sassaƙenta wajen maganin ciwon zuciya, matsalolin zagayawar jini, da kuma kawar da kumburi.

b. Ciwon Gaɓoɓi da Ƙaɓar Ƙashi: A ƙasashen Senegal da Indiya, ana saɓa saiwar zogale tare da gishiri ana shafawa domin maganin ƙaɓar ƙashi da ciwon gaɓoɓin jiki.

c. Ciwon Kwankwaso da Ƙoda: A ƙasar Senegal, suna amfani da saiwa da sassaƙen zogale wajen maganin ciwon kwankwaso da na ƙoda.

d. Maganin Fuka (Asma): Shi kuwa ƙaron zogale, ana amfani da shi ne wajen maganin ciwon fuka (asma) (Fahey, 2005; Olson & Carlquist, 2001; Ramachandran da wasu, 1980).

Naɗewa

A ƙasar Hausa ana kallon bishiyar zogale tamkar “nagge daɗi goma.” Kusan komai na zogale abin amfani ne. Ya kasance abin moriya ta fannonin rayuwa daban-daban kamar dai yadda aka kawo a cikin babukan wannan littafin. Lura da ɗimbin alfanun itacen zogale, yana da kyau mutane su himmatu wajen shukawa a gidaje da gonakansu da sauran wuraren da suka dace. Abu ne mai sauƙi, kasancewar itacen ba ya cin wuri mai yawa, sannan yana da sauƙin shukawa da kuma saurin girma.

Post a Comment

0 Comments