Ticker

6/recent/ticker-posts

Turancin Ungulu Sai Sarkin Fawa: Tsokaci a Kan Waƙoƙin Tsokana a Tunanin Yara

NA

MU’AZU SA’ADU MUHAMMAD

SATUMBA, 2023

Ø Ma’anar Tsokana

Ø Ma’anar Tunani

Ø Ma’anar Waƙoƙi (Waƙa)

Ø Ma’anar Yara

Ø Dalilan Tsokana

Ø Ire-iren Tsokana

Ø Waɗanda Ake Tsokana

Ø Masuyin Tsokana

Ø Wuraren Tsokana

Ø Lokutan Yin Tsokana

Ø Amfanin Tsokana

Ø Sakamakon Tsokana

TURANCIN UNGULU SAI SARKIN FAWA: TSOKACI A KAN WAƘOƘIN TSOKANA A TUNANIN YARA

DALILAN YIN TSOKANA

Daga cikin dalilan yin tsokana akwai tunzura mutum (wanda ake tsokana), sannan tsokana tana sa nishaɗi (wato ana tsokana don neman nishaɗi), da kuma motsa jiki.

IRE-IREN TSOKANA

1. A kwai tsokana ta magana: Akan kwaikwaiyi mutum idan yana wata irin magana misali; ana-ana, ko tsamin baki, ko gura-gura, ko kuma anta-anta.

2. Akan kwaikwaiyi mutum ta dalilin tafiyarsa ko kuma irin tufafin da ya sanya, ko da kuwa tufafin na yayi ne misali; Hula dara. Yara kan tsokani mutumin da ya sanya hula dara da faɗin, “Idan naga mai dara sai na ja da baya nace da shi kuturu ba kuturu ba ne ‘yan alewane suka ce da shi kuturu”, ko kuma “Mai dara sa mana wellecome” ko ” mai dara mayene, mai zanna-bukar angon jaka, mai auwalawo shegen kenan” duk waɗannan wasu waƙoƙi ne da ake yinsu domin a tunzura wanda ya sanya hula dara.

Hakanan tufafin da ake yayinsa shi ma yara suna shirya masa waƙa domin su tsokanin mutumin da ya sanya shi misali;

“Mai akwamiri warin damuna take yi,

Mai akwamuri warin bunsuru take yi,

Akwai wata atanfa da aka yi yayi wacce ake kira da MAI ƊAWISU da MAI IGIYAR SHANYA waɗannan atamfofi su ma yara sun ƙirƙiro waƙoƙi da suke yi wa wanda ya sanyasu. Misali; “Baki da gata ne aka sai miki mai igiyar shanya”. Yara sukan yi wannan tsokanane ta dalilin nishaɗi, a yayin yin wannan waƙoƙine suna rawa suna tsalle-tsalle suna kuma motsa jiki.

3. A kwai suna: Yaro musamman idan yaga mai suna Balaraba, sai ya fara waƙar tsokana yana cewa,

“Larai-larai Laraba,

Tana tafe kashi yana zuba”

Kanan suna yin wata waƙar tsokana da suke cewa,

Ɗanladi na malam ladi,

Ya lashe gadon mai jego,

Ya ce mata wayyo Allah.”

Hanan suna cewa.

“Asabebe Asaberuwa,

Kaza ba ta san Alhamduba,

Sai ta ji wuƙa a maƙogaro.”

Suna wannan ne domin su tunzura mai wannan sunan ne.

4. A kwai kuma mutanan da yara suke kallon siffarsu su yi musu tsokana misali kamar doga. Suna cewa,

“Dogo raƙom-raƙom,

Dogo zauren yinwa.”

Irin wannan tsokana ita ma suna yi ne dominsu tunzura mutumin da yake da wannan suffa.

A kwai ta aiki

A kwai tsokanar da ake yi a dalilin tufafi wadda mutum ya sa, ko a dalilin sunansa ko kuma wata siffa da yake da ita.

WAƊANDA AKE TSOKANA

Akan tsokani mahaukaci domin a tunzura shi, ba ma mahaukaci ba, hatta lafiyayyen mutum yara kan tsokane su shi ta hanyar shirya wata waƙa domin su tunzura su. Daga cikin manyan mutane yara suna tunzura mai saurin fushi, ko juya, ko bakarare, ko mai ido ɗaya, ko mai harara-garke, ko kuma mai kanne, da yawa yara su kan yi amfani da wannan wajen tsokana domin su tunzura mai irin wannan halitta.

Baya da wanan, yara yasu-yasu, idan suka rasa wanda zasu tsokana, sukan ƙirƙiri tsokana su sawa junansu. Misali:

Malam mai duka,

Ya ci tuwan afu,

Alaramma,

Ko gyara babu,

Alaramma.

Shi kuma yaron da ake tsokana sai ya ɗauki bulala yana bin sauran yara da gudu domin ya duke su.

Ko kuma su rinƙa cewa,

Mahaukaciyar kasuwa,

Tana warin daddawa,.

Haka zasu rinƙa bin juna suna motsa jiki.

Suma yara maza ba a ƙalesu ba. Misali a cikin yara idan aka ga mace tana wasa a cikin maza, ana ce mata,

Mai wasa da maza,

Karya,

Tun da na ganta,

Na renata.

Idan wasa ake, saai kaga ta tsahi ta karkaɗe hannunta ta bar wajen.

Idan kuma namiji ne, shi kuma akan ce masa,

Namata-namata,

Kyankyaso,

Na cikin masai,

Kyankyaso,

Mai watsalniya,

Kyankyaso.

Baya da wannan kuma ana cewa,

Na mata ɗauki lefe,

Banda karya mazare.

To, anan wannan waƙa ko tsokana tana raba gwamutsuwa (Cakuɗuwar) maza da mata tun suna yara.

Sannan yara suna tskanar dabba ko dabbobi. Misali yara suna tsokanar raƙumi, suna waƙa suna cewa,

Raƙumi-raƙumi,

Zololo,

Ɗan akuya ya fika ɗuwawu.

***

Raƙumi uwaka ta mutu,

Yanka ƙuda ka yi sadaka.

***

Raƙumi maida gabanka zuwar Adar,

Adar, ta tafi ta barka.

Sai kaga yaro ya dannan da gudu ya shiga gida.

Hakanan ma, tsuntsaye yara suna tsokanarsu ta hanyar waƙa. Misali yara idan sunga kurciya suna tsakanarta da cewa,

Mai kurtun ciki. (Wato suna kyakkwayon kukanta)

Haka nan, suna tskanar talo-talo da cewa,

Talo-talo,

Yimin tusa in ba ka rumbun wake.

Kulu-kulu kulu-kulu kulu-kulu.

Yara suna tsokanar mai naƙasa misali; Gurgu, za ka ji suna cewa,

Tashi ɗangalau gurgun mage,

Tashi ɗangalau gurgun mage,

Ashe kananan ban sami ba.

Misali kaga duk wannan suna cikin masu naƙasa.

Sannan idan sunga mutum mai ƙusumbi suna cewa,

Mai ƙusumbi-ƙusumbi,

Doro,

Mai ƙusumbin baya,

Doro.

Mai ƙusumbin wasa,

Don haka komi haƙurin mutum sai sun tunzura shi.

Sannan idan sunga mai ido ɗaya suna cewa,

Mai ido ɗaya,

Ƙyallin masifa,

Mai Ido ɗaya ƙyalla mu gani.

WURAREN YIN TSOKANA

Yara ssun kangudanar da tsokana a gida, ko a ƙofar gida, haka nan akan yi tsokana a kan hanya ko a makaranta yara yasu-yasu, ko kuma a kasuwamusamman idan aka ga baƙon mahaukaci, yara suna tsokanarsa a kasuwa.

Sai kuma kan hanya: Hanya ta iyu yaran suka zo wucewa, suka ga baƙon mahaukaci, ko kuma suka ga wani daga cikin waɗancen mutanan marassan haƙuri, ko kuma su masu larurarar suka zo wucewa taw ajen da yaran suke wasa a kan hanya a nan ma akan gwamutsa.

LOKACIN YIN TSOKANA

Ko wanne lokaci yaro ya sami dama ba zai bari ba, ba ma da rana ko dare ba, ko da wanne irin lokaci yaro yana iya yin tsokana. Misali. A lokacin Azumi da Asuba yara za su ɗauki ganguna, suna zagaya gari suna cewa,

Gwauro! Gwauro!,

Gwauro,

Mai azumin jemage,

Gwauro,

Tashi gari ya waye,

Gwauro,

Mai sawur da alewa,

Gwauro,

Mai sawur da ƙarago.

AMFANIN YIN TSOKANA

Tskana tana da amfani domin a wajen yara ta za maabin wasa, kumaabin tsinka jini, kuma abin nishaɗi. Domin idan su ka ga wanda suke tono (tskana), har tsalle za a ga suna yi, suna kuma ƙara gayyato yara abokan tsokana. Shi ne yasa ake cewa, “Abokin wasan yaro, wanda ya kula shi”.

Sannan kuma baya da wannan za a ga suna kaiwa goron tsokana, za ka ji suna cewa,

“Kai ga wani cen”

“Ga wani baƙon mutum bai son ka ce ma sa “Sannu”

Misali. Abin da ya faru a wannan shekara ta dubu biyu da ashirin da uku (2023). An yi wani baƙon mahaukaci a gain Kudan. Yara da yawa sun taru suna tsokanarsa shi kuma yaƙi kula kowa, amma da aka sami wata taƙadara ta ce basa “bodari” shikenan ya tunzura ya bisu da gudu yana zage-zage, daga nan buƙatarsu ta biya.

SAKAMAKON TSOKANA

Dama ana yin tsokana ne domin a harzuƙa wanda ake tsokana, sannan ayi guje-guje. To, wani zubin idan an yi guje-gujen nan ana samun matsloli, domin ya kan jawo faɗuwa, ko kuma a sanya mahaukaci ya shiga jefe-jefe, ko kuma a samu sauni, amma dai nishaɗi yana ɗaya daga cikin buƙata ko kuma sakamakon da yaro yake samu a wurin tsokana ko mai lafiya ko mahaukaci, haka kuma baya da nishaɗi ana samun annushuwa.

DABARUN YIN TSOKANA

Yaro Allah ya ba shi shikima wajen tsogalo abin da zai sa mutum ya yi fushi, don haka yara suke amfani da wani sauti, ko wata ƙara kamar; fito, ko dariya, ko ihu domin a tunzura wanda ake tsokana, ko kuma ayi amfani da wata kalma a ƙirƙireta. Misali;

Ayya!

An gama da shi.

Tashi a nan.

Ga abu kaza nan.

Ko kuma ayi kukan akuya, duk wannan dabarun tsokana ne. Misali. Kamar wani mahaukaci da aka taɓa samun labarin shi, ana kiransa da Tsage (Tsage wani kifi ne da ake samunsa a ruwa) To, idan ka ambaci Tsagen nan muddin ya ji, to fa sai kunyi tsiya.

Daga dabarun tsokana akwai aiki Misali; daƙuwa, ko gwalo, ko rawa da sauran makamantansu, haka nan ana kwaikwayon shi wanda ake son a tsokana ko kuma arinƙa hasashe ko ‘yar cinkr-cinke har sai an faɗi abin da baya so.

MASU YIN TSOKANA

Masu yin tsokana su ne yara maza da mata, idan suka taru, kuma a bisa yadda tsari yake yaro ɗaya ke fara tsayawa a wajen mahaukaci. Tsokana daga kallo ake farawa sai aje ga tambaya “Malam yau ka zo nan?”, “Malam wannan kayanka ne?”, “Meye sunanka?” “Sannu” daga nan sai tsiyata ta shi.

Hausa Post

Post a Comment

0 Comments