An ciro daga littafin:
BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)
Na
Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU
1.4 Biɗa
da Tanadi a Faifan Zamani
Zamani ya yi tasiri matuƙa a kan ɓangarorin rayuwar Hausawa, ciki har da abin da
ya shafi biɗa da tanadinsu. Akwai sana’o’in da “aka samu sakamakon cuɗanya
tsakanin Hausawa da wasu baƙin al’ummu, kama sana’ar
kanikanci da kafinta da ɗinkin keke da mesin da dai sauransu” (Sallau, 2009).
Cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Larabawa da Turawa da kuma sauyawan
zamani sun samar da sauye-sauye da dama a fannin biɗa da tanadin Hausawa.[1] Haka kuma, a har kullum Hausawa suna ƙara samun wayewa ta fuskar kasuwanci tare da faɗaɗawa da
bunƙasa sana’o’insu da kuma hanyoyin tanadinsu.
Bunƙasar kasuwancin Hausawa yana kasancewa cikin manyan sigogi guda biyu
kamar haka:
1. Bunƙasar Kasuwanci: Bunƙasar kasuwanci yana faruwa ne yayin da ribar da ɗan
kasuwa yake samu a cikin wani ayyanannen lokaci (misali wata guda) ta ƙaru. Wannan yana iya kasancewa sakamakon ɗaya daga cikin
abubuwan da aka zayyano a ƙasa:
a. Faɗaɗar kasuwanci
b. Ɗaukakuwar darajar kasuwanci
c. Raguwar kuɗaɗen da ake kashewa a kan sana’a[2]
2. Faɗaɗar Kasuwanci: Kasuwanci yana samun faɗaɗa
ne yayin da kayayyakin da yake samarwa suke isa hannun adadin mutane sama da
yadda abin yake a baya. Wannan ma yana
iya kasancewa ta fuskokin da suka haɗa da:
a. Faɗaɗar kasuwanci na cikin gida[3]
b. Faɗaɗar kasuwanci na waje[4]
Yana da kyau a lura da cewa, dukkannin
matakan biyu (bunƙasa da faɗaɗar kasuwanci) suna samuwa
sakamakon tasirin zamani. Dalilan samuwarsu sun haɗa da (i) sauƙaƙar hanyoyin sufuri da (ii)
bunƙasar hanyoyin sadarwa da (iii) sababbin
matakan sarrafawa da makamantansu.
Ana iya kallon tasirin zamani kan kasuwancin
Hausawa ta fuskoki daban-daban kamar haka:
i. Ƙare-Ƙare
ii. Ƙirƙire-Ƙirƙire
iii. Hulɗayya
Kamar yadda masu iya magana suke cewa, “ruwa
ba ya tsami banza,” akwai dalilai daban-daban da suke samar da waɗannan
sauye-sauye a sha’anin kasuwancin Hausawa. Idan aka ce “tasirin zamani,” dunƙulallen zance ne da yake tattare da abubuwa mabambanta.
Yayin da aka banƙaɗa cikinsa, za a tarar da ɗaiɗaikun dalilan
da suka haɗa da:
a. Ɗaukar Hannu: Wannan ya shafi kwaikwayo
daga fasahohin waɗansu al’ummu na daban. Misali, a yau maƙeran Hausawa suna samar da kayayyaki daban-daban ta
hanyar ɗaukar hannu daga ƙere-ƙeren ƙasashen ƙetare. Haka ma kafintoci Hausawa suke ƙera sababbin nau’o’in abubuwan amfani ta hanyar ɗaukar
hannu. Babban misali shi ne bodin babbar mota (roka) da ake amfani da katakai da ƙarafa wajen ƙerawa.
b. Yanayi/Tilasci: Sauyin yanayi da ya shafi
rayuwa ko muhalli na kai ga an samar da sababbin kasuwanci tare da sauye-sauye
a waɗanda ake da su. Kasuwancin sayar da datar intanet da ta POS da Hausawa
suka runguma a yau, duk misalai ne na sababbin nau’o’in kasuwanci da suka samu
a sakamakon tasirin yanayi. Haka kuma awara/wara/ƙwai-da-ƙwai da take ƙara mamaye ƙasar Hausa tana da alaƙa da yanayin yunwa da talauci da Hausawa suke ciki (R.B.
Adamu, keɓantacciyar tattaunawa, 8 ga watan Disamba 2023). A lokacin annobar
korona kuwa (2019-2022), Hausawa da dama sun tara kuɗi ta hanyar kasuwancin
takunkumin fuska (face mask).[5]
c. Yayi: Akan samu lokutan da yayi
na wani nau’in kaya yake sauyawa. Sannu a hankali sai a sake shi a koma kan
wani abu sabo. Irin wannan sauyi yana kasancewa cikin yanayin da abu ne mai
wuya a iya bayanin mene ne haƙiƙanin dalilin da ya sa aka saki tsohuwar al’adar. Sau da
dama sai dai a ce an samu sauyi ne sakamakon “wayewar zamani.”[6]
A ɗaya ɓangaren kuwa, an samu sauye-sauye
game da hanyoyin tanadin Hausawa. Kamar yadda aka tattauna matakan tanadin
Hausawa a ƙarƙashin 1.3, a yau an samu
sauye-sauye da ƙare-ƙare masu tarin yawa. Ɗaya daga cikin misalan waɗannan sauye-sauye shi ne salon
adashen zamani (‘Yar kati).[7]
A ɓangaren turkan dabbobi ma an samu
sauye-sauye da suka haɗa da amfani da allurai da magunguna da sauran dabarun
zamani da suke sa dabbobi girma da wuri tare da kare su daga waɗansu cututtuka.
Asusu kuwa a yau ya koma kan bankuna daban-daban da kuma adana kuɗi ko kadara
cikin nau’o’in kuɗaɗen intanet mabambanta.
Waɗannan bayanai duk sun shafi lamuran biɗa
da tanadin Hausawa ne a zamanance. La’akari da waɗannan sauye-sauye, akwai buƙatar a yi bitar rabe-raben kasuwancin Hausawa. Hakan zai
ba da damar ganin ko an samu ƙarin nau’o’in kasuwanci?
1.5
Naɗewa
Intanet ya kasance tamkar wata duniya mai
zaman kanta, wadda ta cika kuma ta tumbatsa. Da a ce duniyar intanet za ta
bayyana a gan ta ciki da waje, tabbas da za a tarar tana ƙunshe da duk wani abin da ake da shi a duniyar zahiri. An
bar Hausawa a baya ta fuskar shiga a dama da su cikin harkokin biɗa da tanadi a
duniyar intanet. Akwai ƙarancin ingantancen wakilci
na al’adun Hausawa a wannan duniya ta intanet, duk kuwa da hoɓɓasa da ake samu
daga wasu Hausawa a shekarun baya-bayan nan. Hakan kuwa ba ƙaramin ƙalubale ba ne ga Hausa da
Hausawa a idon duniya. Wannan littafi zai kasance jagora wajen haska ɓangarori
daban-daban da Hausawa za su iya sake mayar da hankali domin cin gajiyar
duniyar intanet.
[1] Wannan littafi yana da ra’ayin cewa, ko da
Hausawa ba su yi cuɗanya da kowace al’umma ba, za su samu sauye-sauye da
cigaban zamani a harkokin rayuwarsu. A har kullum halin rayuwa yana tilasta wa
ɗan’adam amfani da fikira wajen sama wa kansa sauƙi da mafita daga ƙalubalen da yake dabaibaiye
da matakan rayuwarsa. Sakamakon haka, yadda kullum yanayin duniya yake sauyawa
tare da ɓullo da sababbin ƙalubale da ɗan’adam bai
taɓa cin karo da su ba, haka yake ƙara ƙirƙiro hanyoyin fuskantar
matsalolin. Waɗannan su ne suke haɗuwa su samar da cigaban zamani. Domin samun ƙarin bayani game da wannan mahangar falsafa, ana iya duba
Cropley (2019).
[2] Ana iya samun raguwar kuɗaɗen da ake kashewa
wurin gudanar da sana’a ta hanyoyin da suka haɗa samun kayayyakin gudanar da
ita mafiya sauƙi ko samun sauƙaƙan hanyoyin jigilar
kayayyakinta zuwa wurin sarrafa su, da dai makamantansu.
[3] Wannan yana faruwa yayin da aka samu ƙarin mutane a muhalli ko maƙwabta ko cikin al’ummar mai sana da suka fara amfani da
kayayyakin da mai sana’ar yake samarwa.
[4] Wannan na faruwa yayin da waɗansu al’ummu na
nesa suka fara amfani da kayayyakin da mai sana’a yake samarwa.
[5] A matakin duniya, bincike ya nuna cewa,
annobar korona ta sa an yi cinikin takunkumin fuska da ya kai na dala biliyan
saba’in da huɗu da miliyan ɗari tara ($74.90bn) a watanni huɗun farko na
shekarar 2021 kawai. A duba Olaoluwa (2021) domin samun ƙarin bayani.
[6] Babban misalin wannan shi ne yadda matasan
Hausawa suka riƙi babban wando (fantalo) a matsayin kwalliya
(tsukakken wando kuma ya kasance ƙauyanci), har zuwa wajajen
shekarar 2008. Daga baya kuma sai yayi ya sauya, inda aka ɗauki fantalo a
matsayin ƙauyanci, shi kuwa tsukakken wando ya koma
wayewa. Duk lokacin da irin haka ya faru, masu kasuwancin wandunan dole su
sauya domin samar da abubuwan da mutane za su saya ba waɗanda za su yi kwantai
ba.
[7] Adashe ‘yar kati wani nau’in adashe ne ko ajiyar kuɗi mai kama da tsarin banki. Babu wani taƙamaiman lokacin zubawa da lokacin ɗiba. Bayan haka, kowane mai zubawa yana cin gashin kansa ne, koma bayan na gargajiya da ake tarawa a ba wa mutum guda (mai ɗiba). Ana amfani da kati wajen adana bayanan zubawa da ɗiba da kuɗin mai ajiya. R. Muhammad, (keɓantacciyar tattaunawa, 6 ga watan Maris 2024).
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.