Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana’a Da Kasuwanci a Bahaushiyar Al’ada

An ciro daga littafin:

BIƊA DA TANADI A DUNIYAR INTANET
(Sana’o’i, Kasuwanci, Ƙwadago)

Na

Abu-Ubaida SANI
Abdulrahman ALIYU

Bida Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana’o’i, Kasuwanci, Kwadago)
Manazartar Littafi: Sani, A-U. & Aliyu, A. (2026). Biɗa Da Tanadi a Duniyar Intanet (Sana'o'i, Kasuwanci, Ƙwadago). Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-978-62480-1-1. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.21361768

Tuntuɓa Domin Samun Littafi: 
Dr. Abu-Ubaida Sani: Imel - abuubaidasani5@gmail.com | WhatsApp - 08133529736
Dr. Abdulrahman Aliyu: WhatsApp - 08036954354

SANA’A DA KASUWANCI A BAHAUSHIYAR AL’ADA

2.0 Shimfiɗa

A babi na farko, an kawo matashiya game da biɗa da tanadi a duniyar yau. Sun shafi hanyoyin neman kuɗi da kuma na tanada su da alkinta su, domin ajiya maganin wata rana. Wannan babi na biyu kuwa ya dubi ‘sana’a’ da ‘kasuwanci’ a matsayin wasu muhimman ɓangarori kuma ginshiƙai na al’adun Hausawa. Kalmomi ne guda biyu waɗanda yawanci Hausawa suke amfani da su a madadin juna. Duk da shigar giragizai tsakanin ma’ana da bagiren amfani da su, wannan babi ya kawo bayanai dangane da kalmomin domin tabbatar da kowacce a gurbinta tare da ganin misalan wuraren da za su iya wakiltar juna.

2.1 Sana’a Da Kasuwanci a Bahaushiyar Al’ada

Kalmomin sana’a da kasuwanci ba sababbi ba ne ga kunnuwan Hausawa. Suna daga cikin kalmomin da bakuna suke furtawa, sannan kunnuwa suke ji a-kai-a-kai. Haka kuma, sun mamaye duniyar nazari da rubuce-rubucen Hausa, musamman waɗanda suka shafi al’ada.

Kalmar sana’a ararriya ce daga harshen Larabci (Jangebe a cikin Wushishi, 2011 sh. 23). Ibrahim, (2023 sh. 218) ya tabbatar da wannan inda ya bayyana cewa, asalin kalmar a Larabci tana da furucin assana’atu. A Larabci tana da ma’anar yin dabara “ta yin amfani da hikima da basira domin samar da wani abu, domin jama’a su amfana” (Ibrahim, 2023 sh. 218).

Masana da manazarta da dama sun bayyana ma’anar kalmar sana’a. Wushishi, (2011 sh. 23-26) ya yi  ƙoƙarin bitar waɗansu daga cikin ma’anonin. Wani abin lura daga cikin ma’anonin shi ne yadda ake samun shigen giragizai tsakanin sana’a da kasuwanci a cikinsu.

Dangane da ma’ana kuwa, sana’a hanya ce ta amfani da azanci da hikima na sarrafa albarkatu da ni’imomi da ɗan’adam[1] ya mallaka don buƙatun yau da kullum... Sana’a aba ce wadda ta danganci tono albarkatun ƙasa da sarafa[2] hanyoyin kimiyya da fasaha da ni’imomin da suke tattare da ɗan’adam[3] da sha’anonin kasuwanci na saye-da-sayarwa da ciniki da sauransu” (Tanko, 2000 sh. 35). Ko a cikin wannan ma’ana, za a ga cewa binciken na Tanko ya sanya kalmomin kasuwanci da saye da sayarwa da ciniki a cikin ma’anar sana’a.

A 2012 binciken Alti ya kawo ma’anar da ta yi ƙoƙarin ba wa sana’a gashin kanta. Ya bayyana cewa: “Sana’a wata hanyar rayuwa ce wadda kan ta’allaƙa da amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomi da Allah ya yi wa ɗan’adam[4] don samun abin biyan buƙatun yau da kullum (Alti, 2012 sh. 29).

Binciken Rumbun Ilimi (n.d. SL. 1) ya nazarci ayyukan masana daban-daban sannan ya bayyana cewa “Sana’a kalma ce da aka aro ta daga Larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance.” Ya ɗauki kasuwanci abu mai cin gashin kansa a matsayin hanyar saye da sayarwa.

Idan aka so bayar da ma’anar sana’a a keɓance, ana iya cewa sana’a ita ce hanyar amfani da fasaha da hikima da kayan aiki domin sarrafa wani abu, musamman dangin albarkatu domin samar da wani abin amfani da za a iya sayarwa ko musanyawa da wani abu mai daraja, ko kuma gyara wani abin amfani da ya lalace ko tsaftace muhalli ko jiki, ko gudanar da ayyukan samar da warakar jiki da gamsuwar zuciya domin samun kuɗi ko wani abu mai dajara kwatankwacin na kuɗi.

A ɓangare guda kuwa, ma’anonin kasuwanci da dama da ayyuka suka zo da su suna da nason sana’o’i a cikinsu. Sukan kasance tamkar dai yadda aka ga nason kasuwanci a cikin ma’anar sana’a wacce (Tanko, 2000 sh. 35) ya bayar kamar yadda aka kawo a baya. Binciken Buhari (2021) ya bayyana ma’anar kasuwanci da cewa:

Kasuwanci dai yana nufin saye da sayarwa na wani abu ko kuma haja wanda abun nan yana iya kasancewa wanda ake gani ne ko kuma wanda ba a gani ne kamar mutum ya yi wani aiki a biya shi to duka suna ɗaukar ma’anar kasuwanci. (Buhari, 2021 SL. 3)

Lura da waɗannan bayanai, ana iya cewa kasuwanci fasaha ne na saye da sayarwa ko musanyen abubuwa masu daraja domin samun riba, ta hanyar bin matakai da dabarun da suka haɗa da gano wurin ɗauko kaya cikin sauƙin farashi da amfani da dabarun talla da jan hankali da tarairayar abokan hulɗa da fikirar daɗin baki a zantukan cinikayya.

2.2 Shigar Giragizai Tsakanin Kasuwanci Da Sana’a

Sana’a da kasuwanci kalmomi ne masu alaƙa da juna. Duk da cewa akwai rubuce-rubucen da suka yi ƙoƙarin bambance tsakaninsu (kamar yadda aka kawo a ƙarƙashin 2.1), sau da dama akan kawo su cikin shigar giragizai. Akwai ma nazarce-nazarcen da suka kawo su a matsayin abu guda.

Gummi, (2014) bai rarrabe  tsakanin sana’o’i da kasuwanci ba. Yayin bayani game da yankunan Sakkwato da Kebbi da Zamfara, ya bayyana cewa: “Daga cikin sana’o’in da ake gudanarwa a wannan yankin akwai noma da kiwo da su da kasuwanci da dai sauransu” (Gummi, 2014 sh. 77). A nan ya kawo kasuwanci a matsayin wani ɓangare na sana’o’i.

Binciken Alti, (2012) ma bai ware ba tsakanin sana’o’i da kasuwanci. Ya kawo su a haɗe a shafi na 32, ciki har da waɗanda suka shafi cinikayya da waɗanda suka shafi ƙere-ƙere da sarrafe-sarrafe. Yadda manazarta suke kallon kasuwanci da sana’a a matsayin abu guda cikin rubuce-rubucensu abu ne mai jan hankali da yake buƙatar zurfafa nazarin ƙwaƙƙwafi.

A shekarar 2018 ma an samu nazarin da ya ginu a kan irin wannan ra’ayi. Abdullahi (2018 sh. 22) ya nazarci ma’anonin ƙamusu na kasuwanci da ƙwadago da fatauci. Daga ƙarshe ya bayyana cewa, duk da bambancin da yake tsakaninsu ta fuskar ma’ana da yanayi da sigar aiwatarwa, Hausawa suna ɗaukar su ne a matsayin abu guda. Ma’ana a nan ita ce, binciken Abdullahi (2018) na da fahimtar cewa, Hausawa sukan ɗauki sana’o’i ko nau’o’in kasuwanci a matsayin abu guda.

Binciken Abdullahi, (2021) ma ya kawo sana’a da kasuwanci a matsayin abu guda. Da yake ba da ma’anar sana’a, ya bayyana cewa tana nufin “... amfani da hikima da kaikawo da juriya da sarrafa albarkatun da suke kewaye da ɗan’adam[5] wala’alla a binne suke a cikin ƙasa ko a sarari, domin biya wa kai buƙatu na yau da kullum” (Abdullahi, 2021 sh. 2). A nan ma za a iya lura da cewa, binciken Abdullahi ya haɗe sana’a da kasuwanci a wuri ɗaya. Dalili kuwa shi ne “sarrafa albarkatu” shi ne abin da ya fi kama da sana’a. Saye da sayar da shi kuma, shi ya fi kama da kasuwanci.

Nasir, (2021) ya nazarci ayyukan masana da manazarta daban-daban. Daga ƙarshe ya kai ga yanke hukuncin cewa, idan aka yi la’akari da ƙunshiyar ma’anonin da suka bayar game da sana’a, “za a fahimci suna da dangantaka da kasuwanci da saye da sayarwa” (Nasir, 2021 sh. 14). Ko ba komai, aikin Aliyu (2018) kacokan ya kira gwanjo da “sana’a”, alhali abu ne da ya shafi saye da sayarwa.

La’akari da bayanan da wannan bincike ya tattara daga rubuce-rubucen da suka gabata, da kuma lura da dukkannin alƙaluman da suke ƙunshe cikin ayyukan, an fahimci waɗansu ‘yan bambance-bambance tsakanin sana’a da kasuwanci. An kawo su cikin jadawali na ɗaya (1) da yake ƙasa.

Jadawali Na 1: Bambance-Bambance Tsakanin Sana’a Da Kasuwanci

Fanni

Sana’a

Kasuwanci

Ma’ana

Sana’a ta fi shafar aikin da za a aiwatar da hannu ta amfani da kayan aiki. Ta shafi sarrafa ma’adanai domin samar da kayan amfani.

Kasuwanci ya fi shafar saye da sayar da kayayyaki domin samun riba.

Fasali

Ta fi shafar aikin da mutum guda yake aiwatarwa da hannaye da basirarsa domin sarrafa wani abu ya samar da wani abu.

Ya shafi sayen abu ko abubuwa daga hannun wani mutum ko waɗansu mutane da sayar da shi ga wani mutum ko waɗansu mutane.

Haɗarin Faɗuwa

Yawanci babu haɗarin faɗuwa. Ko da akwai, yakan kasance kaɗan. Abin da mai sana’a ya samar, shi zai sayar.

Yawanci lamari ne da ya shafi riba da faɗuwa. Ɗankasuwa kullum yana kan lissafin yadda zai kauce wa faɗuwa da yadda zai ci riba sosai.

Yanke Hukunci

Yanke hukunci kamar na abin da ya shafi farashi abu ne da mai sana’a zai iya yi nan take, musamman idan ba ta shafi sayen kayayyaki da za a sarrafa ba.[6] Misali, mai sana’ar yankan farce, ko nawa ya karɓa bai yi hasara ba sakamakon bai sanya waɗansu kuɗaɗe masu yawa ba wajen tanadar kayan aikinsa.

Yanke hukunci game da farashi na buƙatar matuƙar taka-tsantsan don gudun hasara.

Kadada

Yawanci takan kasance taƙaitacciya da ta ƙunshi mutum guda ko mutane kaɗan.

Yana iya kasancewa mai girma da faɗi. Yana iya haɗawa da ma’aikata masu yawa.

Masu Gudanarwa

‘Yan gado da koyo ta hanyar barantaka sun fi yawa.

Akan samu ‘yan haye sosai.

Koyo

Yawanci akan ɗauki lokaci mai tsawo kafin hannu ya iya jiki ya saba.

Akan samu masu faɗawa dare ɗaya idan dai suna da jari.

Madogara: Ɗaukar hannu daga ayyukan  Sallau (2000) da Mika’il (2017) da Rambo (2018) da Buhari (2021)

Yayin da aka nazarci bambance-bambancen da aka kawo a jadawali na ɗaya da yake sama, ana iya ƙoƙarin ware sana’o’i daga kasuwanci. An bayyana hakan a cikin jadawali na biyu (2) da yake ƙasa.

Jadawali Na 2: Waɗansu Sana’o’i da Kasuwancin Hausawa

 

Sana’o’i

 

Kasuwanci

1.                   

Dakau

1.                   

Dillanci

2.                   

Dukanci 

2.                   

Fatauci

3.                   

Jima 

3.                   

Gwanjo

4.                   

Ƙira 

4.

Sakai

5.                   

Kiwo 

 

 

6.                   

Noma 

 

 

7.                   

Rini 

 

 

8.                   

Saƙa 

 

 

9.                   

Sassaƙa 

 

 

10.               

Su (kamun kifi)

 

 

11.               

Wanzanci 

 

 

Madogara: Sallau, (2009 sh. 37-45); Rambo, (2018 sh. 179-190)

A fahimtar wannan littafin, tattauna kasuwanci a kadadar al’adun Hausawa ba zai kammala ba har sai an haɗa shi da sana’o’in Hausawa. Hasali ma a bagire da dama suna iya wakiltar juna. Aikin Muhammad (2020 sh. 224) ya bayyana ma’anar sana’a a matsayin “hanyoyin da ake gudanar da saye da sayarwa." Kai tsaye za a iya cewa wannan ma’ana tana bayani ne a kan kasuwanci. Ta yiwu cuɗeɗeniyar da take tsakanin sana’a da kasuwanci ne ya ja hankalin manazarcin wajen ba da wannan ma’ana.

Ko Rumbun Ilimi (n.d. SL. 1) da (Buhari (2021 SL. 3) da suka rarrabe tsakanin kasuwanci da sana’a, akwai wuraren da bayanansu suke nuna ba a iya rabe su. Misali, Buhari ya kawo “noma” da “kiwo” da “ɗinki” a cikin misalan kasuwanci. Ya yi hakan ne a ƙoƙarin nuna yadda Hausawa suke samun kuɗi da su. Idan aka ɗora su a kan ma’anonin kasuwanci da sana’a, za a tarar da cewa sun fi dacewa da su zauna a ƙarƙashin rukunin sana’o’i.

Ko ba komai, za a tarar da cewa duk sana’ar da za a gudanar (misali kaɗi ko ƙira ko saƙa ko wanzanci da sauransu) to sai kasuwanci ya shiga ciki (ciniki, talla, da sauransu). Haka kuma duk kasuwancin da za a gudanar, to ana yi ne ta amfani da kayayyakin da aka samu sakamakon sana’o’i. Mai aiwatar da sana’a yana iya kasuwancin sayar da kayayyakin sana’arsa (misali masassaƙi ya sayar da turame da taɓare da sauran kayan sassaƙe-sassaƙensa). Haka kuma, ɗan kasuwa mai zaman kansa yana iya gudanar da kasuwancin sayen kaya daga masu sana’o’i domin sayar da su (misali, sakai na iya sayen hatsi daga manoma don ya sayar ya samu riba).

Bugu da ƙari kuma, a koyaushe al’ummar da take da harshe ita take ba wa kalmominta ma’anonin da ta ga dama. Zamani ko yanayi yana iya tasiri ta yadda har zai kai ga al’umma ta sauya  waɗansu kalmomin da take da su, ko ta faɗaɗa ma’anoninsu. A yau, Hausawa da dama sun mayar da kasuwanci zuwa wani matsayin reshe na sana’a, ko dai bisa niyya da fahimtar hakan, ko kuma ba tare da tunaninsu ya kai kan hakan ba. Za a iya kafa hujjar wannan iƙirari da al’adar tambayar da ta kasance sababbiya ga harsunan Hausawa sannan ‘yar gida ga kunnuwansu. Wannan tambaya tana zuwa cikin sigogi mabambanta kamar haka:

Wace sana’a yake yi?

Mece ce sana’arsa?

Yana da sana’a?

A taƙaice ke nan, Hausawa suna amfani da kalmar sana’a wajen wakiltar sana’a da kasuwanci. Amsar misalan tambayoyin da aka kawo a sama na iya kasancewa ɗaya daga cikin misalan kasuwanci da aka bayar a baya. Ko a daɗaɗɗun rubuce-rubuce an samu inda aka kawo kasuwanci a matsayin wani nau’i na sana’a. Yayin lissafo jerin sana’o’in da ake gudanarwa a Talata Mafara, Cibiyar Binciken Tarihin Talata Mafara ta kawo kasuwanci a mataki na tara (9) cikin goma sha huɗu (14) da ta lissafo.[7]



[1] haka

[2] Haka

[3] Haka

[4] Haka

[5] Haka

[6] Akwai sana’o’in da suke buƙatar a sayi kayayyakin gudanar da su. Misali, mai sana’ar rini a zamanance da ya sayi launuka, dole ne kuɗin da zai karɓa ya haura jimillar kuɗin launuka da ya saya. Saɓananin haka, to babu riba sai faɗuwa.

[7] A duba (Cibiyar Binciken Tarihin Talata Mafara, 2007 sh. 73-121).

Post a Comment

0 Comments