Ticker

6/recent/ticker-posts

Zogale Da Kimiyyar Zamani

An Ciro Daga: Bakura, A.R., & Sani, A-U. (2026). Zogale a ƙasar Hausa: Magani, abinci, tattalin arziki. SAS Publishers. ISBN: 978-978-63958-1-4. https://doi.org/10.5281/zenodo.22682300

 Na

Adamu Rabi’u Bakura

Da

Abu-Ubaida Sani

Zogale a Kasar Hausa: Magani, Abinci, Tattalin Arziki

1.4 Zogale Da Kimiyyar Zamani

Kamar yadda zogale take da suna nau’i-nau’i a harshen Hausa dangane da yanayin bambancin muhalli da kuma karin harshe, haka take da sunaye daban-daban da ake ambaton ta da su., t Akwai sunayen a harshen Latin da Faransanci da Girkanci da Indiyanci da sauransu. Wannan ne ya haifar da wanzuwar sunaye daban-daban da aka kira ta da su a kundaye da ƙasidun binciken da aka aiwatar game da zogale. Misali ana kiran ta Moringa Tree, Moringa Oleifera. Akan kuma kira ta da suna: Drustick Tree, Horseradish Tree. Tana ɗaya daga cikin jerin itatuwan da Allah ya albarkace ta da baiwa ta musamman wajen ƙara lafiyar jiki tare da kasancewa garkuwar jiki don hana shigar cuta a cikinsa.

Binciken masana kimiyyar zamani ya tabbatar da kasancewar zogale rumbun sinadarai masu yawan alfanu wajen kiwon lafiyar al’umma, wanda yake da sauƙin mallaka har ga matalauta. Ita ce mafi armashin zama kafar samar da sinadarin gina jiki da ƙara kuzari. A kimiyyance an tabbatar tana kwantar da cututtuka kamar: Saukar da hawan jini tare da taimakawa wajen samun isasshen barci. Wani aikin da zogale za ta iya aiwatarwa ya haɗa da tace ruwa tare da tsabtace su. Kuma tana daskarar da abubuwa masu illa (lahani) a cikin jikin ɗan’adam.

Yayin da al’ummomi suka cigaba da amfani da zogale a matsayin abinci don maganin yunwa da cuta a bisa al’adu mabambanta a sassa daban-daban na duniya. Haka kuma Romawa da Girkawa da Misirawa sukan tatsi (fidda) mai (oil) daga ‘ya’yanta wanda sukan sarrafa shi wajen yin turare da man shafawa. A ƙarni na 19 gandayen zogale da suke yammacin ƙasar Indiya sun fitar da man zogale zuwa ƙasashen Turai don sarrafa shi wajen yin turare da giris don amfanin na’urori. An tabbatar da irin fa’idojin da suke ƙunshe a cikin zogale ta hanyar binciken masana kimiyyar zamani. Ganyen zogale tun fil-azal Allah ya halicce shi yana ƙunshe da ninkin sinadarai nau’i-nau’i kamar haka:

a.  Sinadarin bitamin “SI” (c) ninki bakwai (7) fiye da wanda yake cikin lemo.

b.  Sinadarin kalsiyam ninki huɗu (4) fiye da wanda yake cikin madara.

c.  Sinadarin bitamin “E” (A) ninki huɗu (4) fiye da wanda yake cikin karas.

d.  Sinadarin kanwa ninki uku (3) fiye da wanda yake cikin ayaba.

e.  Sinadarin furotin ninki biyu (2) fiye da wanda yake cikin kindirmo.

Dr. Mercola ya bayyana cewa, zogale tana ƙunshe da bitamin da ma’adanan gina jiki da muhimman tsamin amino, antioxidants da sauran su. Bincikensa ya tabbatar zogale tana maganin ciwon suga (diyabitis) da na kumburi, Cholesterol-lowering, sannan tana kare jiki daga cututtuka. ‘Ya’yan zogale kuwa za a iya amfani da su wajen tsabtace ruwan sha fiye da wasu sinadiran zamani da ake amfani da su. Ya kuma nuna cewa, ganyen zogale yana tattare da sinadirai masu gina jiki, kamar furatainin da alli da beta da carotene da bitamin “SI”(c ) da potassium. Ana amfani da ita a matsayin abinci da magani fiye da shekara 4000 da suka shuɗe. Binciken nasa ya nuna zogale yana tattare da abubuwa kamar haka:

a.  Sinadarin gina jiki ninki tara (9) fiye da wanda yake ƙunshe a cikin kindirmo (yoghut).

b.  Sinadarin bitamin “E” (A) ninki goma (10) fiye da wanda yake cikin karas.

c.  Sinadarin potassium ninki goma sha biyar (15) fiye da wanda yake cikin ayaba.

d.  Sinadarin kalsiyam (calcium) ninki goma sha bakwai (17) fiye da wanda yake cikin madara.

e.  Sinadarin bitamin “SI” (c) ninki goma sha biyu (12) fiye da wanda yake cikin lemo.

f.  Sinadarin iron ninki ishirin da biyar (25) fiye da wanda yake cikin alayyaho.

Dr. Mercola, ya ƙara da cewa, zogale tana maganin ciwon suga saboda irin muhimman sinadaran da suke ƙunshe a cikin ganyenta waɗanda suka haɗa da, isothiocyanates. Ya kuma bayyana cewa, duk matar da ta rinƙa shan garin ganyen zogale mai nauyin giram bakwai (7grm) a duk rana har tsawon wata uku, sukarin jikinta zai ragu da kashi goma sha uku da rabi (13. 5) daga cikin ɗari (13. 5%). Haka zuba garin ganyen zogale mai nauyin giram hamsin (50grm) a cikin abinci, ga masu fama da ciwon suga, yana rage yawan sukarin da kashi ashirin da ɗaya bisa ɗari (21%).

Ya kuma nuna ganyen zogale da kwasfarta da ‘ya’yanta suna ƙunshe da isothiocyanates, flavonoids da kuma tsamin phenolic. Wannan ne ya ba su damar mallakar sinadaran da suke magance kumburi. Sakamakon haka ne a gargajiyance ake amfani da zogale wajen maganin gyambon ciki (stomach ulcet). Manta yana maganin ciwon hanta domin yana kare ta daga kumburin sha-ma-jika. Hasali ma mai ne da babu kamarsa. Ana sarrafa shi wajen kare abinci daga lalacewa da kuma ta fuskar toye-toye da haɗa salad. Yana maganin amosanin gaɓɓai da hana bushewar fatar jiki.

A cikin Duniyar Intanet a shafin Madina Islamic Medicine, an bayyana zogale da cewa, itaciya ce mai ban al’ajabi wadda Allah ya sanya albarka da waraka a cikinta. Ita abinci ce mai romon sinadaran da suke ƙara lafiya a jiki. Don haka ne aka kira ta da suna Itaciyar Rayuwa (The Tree of Life). Ganyen zogale yana ƙunshe da romon sinadari mai tarin yawa na bitamin “E” (A) wanda yake ƙara wa idanun ɗan’adam lafiya da gani fiye da bitamin “E” (A) da yake cikin karas har ninki huɗu (4). Sun kuma nuna cewa, zogale yana tattare da sinadarai masu yawan gaske kamar:

a.  Sinadarin calcium mai sanya ƙashi da haƙoran ɗan’adam ƙwari da lafiya ninki huɗu (4) fiye da wanda yake cikin madara.

b.  Sinadarin bitamin SI (c) wanda yake ƙarfafa garkuwar jikin ɗan’adam don yaƙi da cututtuka masu kai farmaki ga lafiyar jiki, ninki bakwai (7) fiye da wanda yake cikin lemo.

c.  Sinadarin bitamin “I” (E) da ke kyautata fata da lafiyar jiki.

Binciken masana ilimin kimiyya game da itaciyar zogale ya bayyana zogale na:

a.  Daidaita sukarin da yake cikin jiki.

b.  Rage hawan jini.

c.  Ƙara wa mace mai shayarwa ruwan mama (nono).

d.  Kashe ƙwayoyin cutar bakteriyal.

e.  Wanke ciki, idan aka ci kafin a ci wani abinci.

f.  Kare lafiyar hanta da ƙoda.

g.  Ƙara kuzarin jiki.

h.  Rage ƙiba.

i.  Gyara ƙwaƙwalwa da sauran su.

1.5 Naɗewa

Haƙiƙa itaciyar zogale tana da muhimmanci da daraja a duniya. Ɗimbin amfaninta ya sa masana da manazarta a fannonin ilimi daban-daban suke ci gaba da rubuce-rubuce dangane da ita. Sun haɗa da masana a ɓangaren kiwon lafiya da ilimin halittu da na tsirrai har ma da masana a fannonin da suka shafi al’adu da tarihi. A wannan babi, an ga yadda al’ummomi suka riƙe zogale da muhimmanci, har itaciyar ta yaɗu zuwa sassan duniya, cikinsu kuwa har da ƙasar Hausa.

Post a Comment

0 Comments