"Ya ci maza jikan mashasha,
Gogarma raba kaya
Shehu na Sarkin Rwahi na malan Atto".
Wannan amshin wata waƙa ce da Makaɗa Sa'idu Faru (1916-1987) ya rarewa marigayi maigirma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji, Barista Hwanarabul Usman Usman Kure Bunguɗu da aka fi sani da Alh. Usman Ɗangwaggo Bunguɗu (1928-2008).
A sharhin mu na yau zamu duba alaƙar
marigayi Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu
da Sarkin Rwahi /Sarkin Rafi da kuma malan Atto/Malam Attahiru ne da yake
danganta shi dasu a cikin wannan waƙa "Shehu na Sarkin Rwahi na malan
Atto".
Duk da yake bamu samu
tabbataciyar magana ba akan kowane Sarkin Rafi ba ne a lokacin da aka yi wannan
waƙar
a cikin 1970s amma mun haƙiƙance cewa laƙabin sarautar Sarkin Rafi a gundumar
Bunguɗu (a lokacin da
aka yi waƙar)
wato masarautar Bunguɗu
ta yau dake Jihar Zamfara har ya zuwa yau a garin da ake kira
"Kwaikwai" ne ake yin ta.
Malam Abdulƙadir ɗan Sarkin Fulanin Bunguɗu na 4 wato Muhammadu
Lawali ɗan Sarkin
Fulanin Bunguɗu na 2
wato Ibrahim I(Maigari) ɗan
Sarkin Fulanin Bunguɗu
na farko wato Muhammadu Zundumi ne ya haifi Sarkin Rafin Kwaikwai na farko da
ake kira Sarkin Rafi Huta. Ya zuwa yau zuriyarsa ne(shi Huta) ke sarautar
wannan gari da ya zama hedikwatar gundumar Kwaikwai da wannan laƙabi na
Sarkin Rafi.
Maigirma Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu ɗan Sarkin Fulanin Bunguɗu na 10 ne wato Sarki Usman
Kure da yayi sarauta daga shekarar 1932 zuwa 1944 shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 6 ne
wato Sarki Ibrahim II da yayi mulki daga 1891-1913, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 4 ne
wato Muhammadu Lawali da ya yi sarauta daga 1841- 1879, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 2 ne,
Ibrahim I(Maigari) da ya yi mulki daga 1785-1825 shi kuma ɗan Sarkin Fulanin Bunguɗu na farko ne wato
Muhammadu Zundumi wanda ya yi sarauta daga shekarar 1740 zuwa 1785.
Kenan da Sarkin Rafin Kwaikwai
wanda Makaɗa Sa'idu
Faru ya danganta da shi Ɗanmadamin Sakkwato Alhaji Usman Ɗangwaggo Bunguɗu duka daga gidan Sarkin Fulanin Bunguɗu na 4 wato Muhammadu
Lawali ɗan Ibrahim
I(Maigari) ɗan
Muhammadu Zundumi suka fito. Ashe kiran sa da "Na Sarkin Rwahi/Sarkin
Rafi" babu za'ida.
To shi Malam Atto fa? Ta ina
Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu ya zama nashi?
Malam Attahiru ko Malam Atto
kamar yadda aka fi sanin sa ɗan
Sarkin Fulanin Bunguɗu
na 7 ne wato Sarkin Fulani Mahe wanda ya yi sarauta daga 1913-125, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 6 ne
wato Sarki Ibrahim II da ya yi mulki daga 1891 - 1913, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 4 ne
wato Sarki Muhammadu Lawali da ya yi sarauta daga 1841-1879, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na 2 ne,
wato Sarki Ibrahim I(Maigari) da ya yi mulki daga 1785-1825, shi kuma ɗan Sarkin Fulani na farko
ne wato Sarki Muhammadu Zundumi wanda ya yi sarauta daga shekarar 1740 zuwa
1785.
Kenan shi ma Malan Attahiru
/Malam Atto tsatson Sarkin Fulani na 4 ne wato Sarki Muhammadu Lawali ɗan Sarki Ibrahim I(Maigari)
ɗan Sarki Muhammadu
Zundumi kamar yadda Sarkin Rafin Kwaikwai da Ɗanmadamin Sakkwato Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu suke.
Da wannan muna iya cewa dangata
waɗannan mashahuran
mutane da marigayi maigirma Ɗanmadamin Sakkwato, Alhaji Usman Ɗangwaggo
Bunguɗu da Makaɗa Sa'idu Faru ya yi a cikin
wannan waƙa
"Shehu na Sarkin Rwahi na Malan Atto" daidai ne saboda yan uwa ne na
jini.
Abin lura anan shi ne shi Malan
Atto/Malam Attahiru ɗan
Sarki Mahe ɗan Sarki
Ibrahim II ɗan
Muhammadu Lawali ɗan
Ibrahim I(Maigari) ɗan
Muhammadu Zundumi wanda ya taɓa
zama wakili a majalisar wakilai ta Tarayyar Nijeriya a Jamhuriya ta farko
(1960s) shi ne mahaifin mai martaba Sarkin Fulanin Bunguɗu na yanzu wanda kuma shi ne Sarki na 14 a
wannan masarauta mai daraja ta ɗaya,
Alhaji Hassan Attahiru MFR. Allah SWT ya ƙarawa mai martaba Sarki lafiya da nisan
kwana mai albarka ya jiƙan dukan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da
imani Alfarmar Sahibul Qiblataini Rasulallahi Sallallahu Alaihim Wasallam, amin
ya rabbal alamin.
A wannan hoto marigayi Malam
Attahiru /Malam Atto Bunguɗu
ne.
Daga Taskar:
Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin
Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.
01/08 /2026.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.