Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijinta Ya Rasu A Ranar Cika Iddarta

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahamatullahi wabarkatuhu Barka da safiya da fatan an tashi lafiya ina da tambaya mine ne hukuncin macen da mijin ta ya mutu, Kuma a ranar da ya rasu shi ne kwanan idda ta ya ƙare ko za ta ƙara ne? Allah ƙara lafiya da imani na gode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum salam warahamatullahi wabarkatuhu

Idan mijinta ya rasu alhalin tana cikin iddar saki mai dawowa (saki raj'iyyi) kuma rasuwar ta zo ne kafin iddar ta cika ko a daidai ranar da ake gab da cikar ta, to za ta sauya zuwa iddar mutuwa (wata huɗu da kwana goma) kuma tana da gajiyar gado a tare da shi.

Idan miji ya saki matarsa saki ɗaya ko biyu kuma tana cikin idda, a shari'ance ita ma'aikaciyar aure ce, kuma miji na da ikon mayar da ita. Idan ya rasu a wannan lokacin (koda kuwa ranar ƙarshe ce ta iddar), ta koma iddar mutuwa.

Idan har iddarta ta cika kuma ta gama lakacin da ake buƙata kafin numfashin mijin ya yanke, to auren ya riga ya mutu gaba ɗaya, kuma ba ta da iddar mutuwa ko gado.

Idan mijinta ya mutu tana da ciki, haihuwarta a ranar ko bayan rasuwarsa na nufin ta gama iddarta ke nan. Ba ta buƙatar cika watanni huɗu da kwanaki goma (iddar takaba) tunda ciki ya riga ya sauka. Haihuwa shi ne abin da ke kawo ƙarshen iddar mace mai ciki, kamar yadda aya ta 4 a cikin Suratu A-alāƙ ta nuna:

وَالّٰٓـىٴِۡ يَٮِٕسۡنَ مِنَ الۡمَحِيۡضِ مِنۡ نِّسَآٮِٕكُمۡ اِنِ ارۡتَبۡتُمۡ فَعِدَّتُهُنَّ ثَلٰثَةُ اَشۡهُرٍ وَّالّٰٓـىٴِۡ لَمۡ يَحِضۡنَ ؕ وَاُولَاتُ الۡاَحۡمَالِ اَجَلُهُنَّ اَنۡ يَّضَعۡنَ حَمۡلَهُنَّ ؕ وَمَنۡ يَّـتَّـقِ اللّٰهَ يَجۡعَلْ لَّهٗ مِنۡ اَمۡرِهٖ یُسْرًا‏

Kuma waɗanda suka yanke ɗammani daga haila daga matanku, idan kun yi shakka, to, iddarsu wata uku ce da waɗanda ba su yi haila ba. Kuma ma'abũta cikinna ajalinsu, (shi ne) cewa su haifi cikinnansu. Kuma wanda ya bi Allah da taƙawa, (Allah) zai sanya masa wani sauƙi daga al'amarinsa. (Surah: At-Talaaƙ, Ayat: 4).

Saboda haka idan mijinki ya rasu alhalin kina cikin wata tsohuwar idda ta saki kuma lokacin bai gama cika ba ko da a karshen ranar ne, wajibi ne ki soke iddar sakin ki koma ga iddar mutuwa (takaba) ta tsawon wata huɗu da kwana goma (4 months and 10 days). Kuma Wajibi ne ki yi wannan takaba a cikin gidan da kuka saba zama da shi ko wanda ya rasu ya barki a ciki.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments