𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam ni sunana Binta. Wanda mahaifina ya sanya mun Amma sai na ji wasu malamai suna cewa ba suna ba ne. Shin malan yaya abun yake?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikis salam wa
rahmatullahi wa barakatuhu.
Sunan BINTA na nufin
«Diya» ko «Yarinya» a harshen Hausa, kuma ya samo asali ne daga kalmar Larabci
«BINT» (بنت) da ke nufin ɗiya ko 'ya.
Hausawa suna yin
inkiyar sunan ne ga 'ya'yansu masu suna 'FATIMAH" wato FATIMA BINTU RASUL
(Fatima 'yar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam). To daga nan ne sai
hausawan suke yin wani kirari ga duk masu suna Fatimah, suna cewa "Fadima
Binta". To daga nan kuma sai sukan kirata da suna "BINTA".
Sunan
"BINTA" a asali ba sunan da aka tsara ya zama cikakken suna ba ne. Wato
ba sunan yanka ba ne mai zaman kansa a harshen Larabci, amma ya zama suna mai
zaman kansa a al'adance musamman a wurin Hausawa. Saboda sun saba da sunan, har
suna sanya wa 'yayansu kai tsaye a matsayin cikakken suna mai zaman kansa, kuma
babu laifi a sanya shi tunda yana da kyakykyawan ma'ana a harshen Larabci da
al'ada. Ba a sami wani hani ko haramci daga malaman Musulunci game da sanya wa
yara wannan suna ba, domin yana nufin 'ya ko kuma yana da nasaba da sunayen
gidan Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Ana iya chanza miki
sunan BINTA zuwa FATIMAH. Ya halatta a chanza wa mutum suna ko kuma shi da
kansa ya chanza sunan idan ya zamanto akwai wata matsala tare da sunan. Kamar
yadda Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yi chanjin suna ga wasu daga cikin
sahabbansa masu yawa, bayan sun musulunta. Kuma kamar yadda Sayyiduna Umar (ra)
ya taɓa chanza wa matarsa
sunanta daga "AASIYAH" (عاصية) zuwa JAMILAH.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.