Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kyautar Mahaifi Kafin Mutuwa

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mahaifinmu kafin ya rasu ya bai wa ɗansa kyautar fili inda ya gina gidansa. Mene ne hukuncin wannan kyautar yanzu da aka zo rabon gado?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Malamai sun nuna cewa, kyautar mahaifi irin wannan nau’i biyu ce:

1. Akwai wacce ta ke cikin babin: Al-Hibah, watau kyautar da mahaifin ya keɓance wani ɗansa da ita, ba domin wata larura ko buƙata da ta tilasta shi ya keɓance shi, ko ya fifita shi a kan sauran ’ya’yansa da hakan ba.

2. Akwai kuma wacce ta ke cikin babin An-Nafaƙah, watau kyautar da mahaifin ya keɓance ɗan da ita saboda wata buƙata wacce ta tilasta shi ya yi masa hakan, ban da sauran yayan nasa.

A kan na-farkon akwai hadisi da ya zo kai-tsaye a kansa: Al-Imaam Al-Bukhaariy da Al-Imaam Muslim sun riwaito a cikin sahihan littaffansu daga sahabi An-Nu’uman Bn Basheer (Radiyal Laahu Anhu) cewa:

أَنَّ أُمَّهُ بِنْتَ رَوَاحَةَ سَأَلَتْ أَبَاهُ بَعْضَ الْمَوْهِبَةِ مِنْ مَالِهِ لاِبْنِهَا ، فَالْتَوَى بِهَا سَنَةً ثُمَّ بَدَا لَهُ ، فَقَالَتْ : لاَ أَرْضَى حَتَّى تُشْهِدَ رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - عَلَى مَا وَهَبْتَ لاِبْنِى. فَأَخَذَ أَبِى بِيَدِى وَأَنَا يَوْمَئِذٍ غُلاَمٌ فَأَتَى رَسُولَ اللَّهِ - صلى الله عليه وسلم - فَقَالَ : يَا رَسُولَ اللَّهِ ، إِنَّ أُمَّ هَذَا بِنْتَ رَوَاحَةَ أَعْجَبَهَا أَنْ أُشْهِدَكَ عَلَى الَّذِى وَهَبْتُ لاِبْنِهَا. فَقَالَ رَسُولُ اللَّهِ : - صلى الله عليه وسلم - : « يَا بَشِيرُ أَلَكَ وَلَدٌ سِوَى هَذَا؟» قَالَ : نَعَمْ. فَقَالَ : « أَكُلَّهُمْ وَهَبْتَ لَهُ مِثْلَ هَذَا؟ » قَالَ : لاَ. قَالَ : « فَلاَ تُشْهِدْنِى إِذًا ، فَإِنِّى لاَ أَشْهَدُ عَلَى جَوْرٍ ».

Mahaifiyarsa Bint Rawaahah ce ta roƙi mahaifinsa wata kyauta daga cikin dukiyarsa saboda ɗanta, sai ya yi ta jan-ƙafa har tsawon shekara guda. Daga baya kuwa sai ya ga ya dace, (don haka sai ya ba shi kyautar). Sai ta ce: Ba zan yarda ba, har sai ka kafa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) shaida a kan abin da ka bai wa ɗana. Sai babana ya kama hannuna a lokacin ina ƙarami, ya tafi da ni wurin Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), ya ce: Ya Manzon Allaah! Mahaifiyar wannan: Bint Rawaahah ce take son in kafa ka shaida a kan kyautar da na bai wa ɗanta. Sai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce: ‘Basheer! Kana da wani ɗan ne ban da wannan?’ Ya ce: ‘E.’ Ya ce: ‘To, kowannensu ka ba shi irin kyautar wannan?’ Ya ce: A’a. Ya ce: ‘To tun da haka ne, kar ka sanya ni shaida. Domin ni kam ba na yin shaida a kan zalunci.’ (Sahih Al-Bukhaariy: 2650, Sahih Muslim: 1625).

A wata riwaya ya ce: « فَارْجِعْهُ » To, ka karɓe shi. (Sahih Al-Bukhaariy: 2586).

A wata kuma ya ce:

« اتَّقُوا اللَّهَ وَاعْدِلُوا فِى أَوْلاَدِكُمْ ». فَرَجَعَ أَبِى فَرَدَّ تِلْكَ الصَّدَقَةَ.

‘Ku ji tsoron Allaah! Ku yi adalci a tsakanin ’ya’yanku.’ Sai babana ya dawo ya karɓe wannan sadakar (kyautar). (Sahih Muslim: 1623).

Game da fiƙhun wannan hadisin, Al-Imaam Ibn Ƙudaamah (Rahimahul Laah) ya ce:

وَهُوَ دَلِيلٌ عَلَى التَّحْرِيمِ لِأَنَّهُ سَمَّاهُ جَوْرًا ، وَأَمَرَ بِرَدِّهِ ، وَامْتَنَعَ مِنَ الشَّهَادَةِ عَلَيْهِ ، وَالْجَوْرُ حَرَامٌ ، وَالْأَمْرُ يَقْتَضِي الْوُجُوبَ ، وَلِأَنَّ تَفْضِيلَ بَعْضِهِمْ يُورِثُ بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ وَقَطِيعَةَ الرَّحِمِ ، فَمَنَعَ مِنْهُ ، كَتَزْوِيجِ الْمَرْأَةِ عَلَى عَمَّتِهَا أَوْ خَالَتِهَا

Wannan hadisi dalili ne a kan haramci, saboda ya kira shi: Zalunci, kuma ya yi umurni a warware shi, kuma ya ki yarda ya yi shaida a kansa. Shi kuma zalunci haram ne, kuma umurnin yana hukunta cewa shi wajibi ne. Kuma domin fifita sashensu yana aukar da gaba da kiyayya da yanke zumunci, don haka ya hana yin shi, kamar dai hada auren mace da goggonta ko innarta. (Al-Mughnee: 6/298).

Al-Imaam As-Shawkaaniy (Rahimahul Laah) ya ce:

وَهَذِهِ الْأَحَادِيثُ تَدُلُّ عَلَى وُجُوبِ التَّسْوِيَةِ ، وَأَنَّ التَّفْضِيلَ بَاطِلٌ جَوْرٌ ، يَجِبُ عَلَى فَاعِلِهِ اسْتِرْجَاعُهُ. وَبِهِ قَالَ طَاوُسُ وَالثَّوْرِىُّ وَأَحْمَدُ وَإِسَحَاقُ وَبَعْضُ الْمَالِكِيَّةِ.

Waɗannan hadisan suna nuna wajibcin daidaitawa a tsakanin ’ya’ya, kuma cewa fifitawa ɓataccen abu ne, zalunci ne. Wajibi ne ga mai aikata shi ya koma ya karɓe shi. Wannan kuma ita ce maganar Taawus da At-Thawriy da Ahmad da Is’haaƙ da waɗansu malaman Maalikiyyah. (Ad-Daraarul Mudiyyah sharh Durarul Bahiyyah: 2/304).

Kuma a cikin littafin As-Sunan na Sa’eed Bn Mansuur ya riwaito da isnadinsa har zuwa ga Abu-Saalih cewa:

أَنَّ سَعْدَ بْنَ عُبَادَةَ قَسَمَ مَالًا بَيْنَ وَلَدِهِ وَخَرَجَ إِلَى الشَّامِ ، فَوُلِدَ لَهُ ابْنٌ بَعْدَهُ ، فَمَاتَ ، فَجَاءَ أَبُو بَكْرٍ وَعُمَرُ إِلَى قَيْسِ بْنِ سَعْدٍ فَقَالَا : " إِنَّ سَعْدًا قَسَمَ بَيْنَ وَلَدِهِ وَمَا يَدْرِي مَا هُوَ كَائِنٌ ، وَإِنَّا نَرَى أَنْ تَرُدَّ عَلَى هَذَا الْغُلَامِ ، فَقَالَ قَيْسٌ : مَا أَنَا بِرَادٍّ شَيْئًا فَعَلَهُ سَعْدٌ ، وَلَكِنَّ نَصِيبِي لَهُ "

Sa’ad Bn Ubaadah ya raba dukiya a tsakanin ’ya’yansa, kuma sai ya fita tafiya zuwa Shaam. Sai kuwa aka haifa masa jariri a bayansa, shi kuma ya rasu. Shi ne Abubakar da Umar suka je wurin Ƙays Bn Sa’ad suka ce: ‘Sa’ad ya raba dukiya a tsakanin ’ya’yansa alhali bai san abin da zai auku ba, don haka muna ganin ka warware wannan kyautar saboda wannan jaririn.’ Sai Ƙays ya ce: ‘Ba zan warware abin da Sa’ad ya yi ba, amma dai na bar wa jaririn nawa rabon.’ (Sunan Sa’eed Bn Mansuur: 291).

Shi ma Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahul Laah) ya faɗa a cikin Al-Ikhtiyaaraatul Ilmiyyah ta sa cewa:

وَالصَّحِيحُ مِنْ قَوْلِ الْعُلَمَاءِ ، أَنَّ هَذَا وَاَلَّذِي خَصَّ بَنَاتِهِ بِالْعَطِيَّةِ دُونَ حَمْلِهِ يَجِبُ عَلَيْهِ أَنْ يَرُدَّ ذَلِكَ فِي حَيَاتِهِ ، كَمَا أَمَرَ النَّبِيُّ. وَإِنْ مَاتَ وَلَمْ يَرُدَّهُ رُدَّ بَعْدَ مَوْتِهِ عَلَى أَصَحِّ الْقَوْلَيْنِ أَيْضًا ، طَاعَةً لِلَّهِ وَلِرَسُولِهِ ، وَاتِّبَاعًا لِلْعَدْلِ الَّذِي أُمِرَ بِهِ ، وَاقْتِدَاءً بِأَبِي بَكْرٍ وَعُمَرَ ، وَلَا يَحِلُّ لِلَّذِي فَضَّلَ أَنْ يَأْخُذَ الْفَضْلَ ، بَلْ عَلَيْهِ أَنْ يُقَاسِمَ إخْوَتَهُ فِي جَمِيعِ الْمَالِ بِالْعَدْلِ الَّذِي أَمَرَ اللَّهُ بِهِ ، وَاَللَّهُ سُبْحَانَهُ وَتَعَالَى أَعْلَمُ.

Ingantacciyar maganar malamai dai ita ce: A kan wannan da kuma wanda ya fifita ’ya’yansa mata da kyauta ya bar jaririn da ke cikin ciki, ya wajaba gare shi ya warware wannan kyautar a halin rayuwarsa kamar yadda Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi umurni. Idan kuma ya rasu alhali bai warware shi ba, to sai a mayar da shi daidai a bayan rasuwarsa, a mafi ingancin maganganu biyu na malamai. Wannan domin biyayya ga Allaah da Manzonsa, kuma domin yin adalcin da aka yi umurni da shi, kuma domin yin koyi da Abubakar da Umar. Kuma bai halatta ga shi wanda aka fifita da kyautar ya cigaba da riƙe wannan kyautar ba. Abin dai da yake wajibinsa shi ne: Ya yi raba-daidai da yan uwansa a cikin dukkan dukiyar a bisa adalcin da Allaah ya yi umurni da shi. Kuma Allaah Mai Tsarki da Ɗaukaka shi ne Masani. (Al-Fataawal Kubraa: 4/184-185).

Sannan babban malamin Fiƙhu a wannan zamanin As-Shaikh Muhammad Bn Saalih Al-Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya ce:

وَالصَّوَابُ : أَنَّهُ إِذَا مَاتَ وَجَبَ عَلَى الْمُفَضَّلِ أَنْ يَرُدَّ مَا فُضِّلَ بِهِ فِي التَّرِكَةِ ، فَإِنْ لَمْ يَفْعَلْ خُصِمَ مِنْ نَصِيبِهِ إِنْ كَانَ لَهُ نَصِيبٌ ؛ لِأَنَّهُ لَمَّا وَجَبَ عَلَى الْأَبِ الَّذِي مَاتَ أَنْ يَسْوِيَ ، فَمَاتَ قَبْلَ أَنْ يَفْعَلَ صَارَ كَالْمَدِينِ ، وَالدَّيْنُ يَجِبُ أَنْ يُؤَدَّى ، وَعَلَى هَذَا نَقُولُ لِلْمُفَضَّلِ : إِنْ كُنْتَ تُرِيدُ بَرَّ وِالِدِكَ فَرُدَّ مَا أَعْطَاكَ فِي التَّرِكَةِ.

Abin da yake daidai shi ne: Idan shi (mahaifin) ya rasu, to ya wajaba a kan wanda aka fifita ɗin ya mayar da abin da aka fifita shi da shi a cikin kayan gado. Idan kuma bai yi hakan ba, to sai a rage wannan abin daga cikin gadonsa idan yana da rabo a cikin gadon. Domin tun da dai ya wajaba a kan mahaifin da ya rasu cewa ya daidaita a tsakanin ’ya’yansa sai kuma ya rasu ba tare da ya yi hakan ba, to shi ya zama kamar wanda ake bin sa bashi ke nan. Shi kuwa bashi wajibi ne a biya shi. A ƙarƙashin wannan ne, muke faɗa wa wannan da aka fifita cewa: Idan dai har kai mai biyayya da neman alheri ne ga mahaifinka, to sai ka mayar da abin da ya ba ka a cikin kayan gado. (As-Sharhul Mumti’ Alaa Zaadil Mustaƙni’: 11/85).

Har dai zuwa inda ya ce:

فَإِنْ قَالَ قَائِلٌ : إِذَا كَانَ أَحَدُهُمْ يَحْتَاجُ إِلَى سَيَّارَةٍ وَالْآخَرُونَ لَا يَحْتَاجُونَ؛ لِأَنَّ الْأَوَّلَ مَدْرَسَتُهُ بَعِيدةٌ وَالْآخَرُونَ مَدْرَسَتُهُمْ قَرِيبَةٌ ، فَهَلْ يَجُوزُ أَنْ يَشْتَرِيَ لِلَّذِي يَحْتَاجُ السَّيَّارَةَ سَيَّارَةً ؛ لِأَنَّهُ يَحْتَاجُهَا؟

Idan kuma wani ya ce: Idan ɗaya daga cikin yaran ya buƙaci mota sauran kuma ba su da wannan buƙatar, domin na-farkon wataƙila yana zuwa makaranta a nesa, sauran kuma suna zuwa na-kusa, ko zai yiwu ya saya wa wanda yake da buƙatar, domin ya buƙatu ga motar?

Sai ya amsa da cewa:

لَا يَجُوزُ؛ لِأَنَّهُ إِنَّمَا يَحْتَاجُ لِلنَّفْعِ فَقَطْ ، وَهُوِ رُكُوبُهَا إِلَى الْمَدْرَسَةِ وَرُجُوعِهِ ، وَهَذَا يَحْصِلُ بِأَنْ تُكْتَبَ السَّيَّارَةُ بِاسْمِ الْوَالِدِ ، وَيَبْقَى الاِنْتِفَاعُ لِلْوَلَدِ ، بِحَيْثُ إِذَا مَاتَ الْوَالِدُ تَرْجِعُ هَذِهِ السَّيَّارَةُ فِي التَّرِكَةِ ، وَلَا يَجُوزُ لِلْإِنْسَانِ أَنْ يُمَلِّكَ الْوَلَدَ السَّيَّارَةَ ؛ لِأّنَّ الْمَقْصُودَ دَفْعُ الْحَاجَةِ ، وَدَفْعُ الْحَاجَةِ يَحْصِلُ بِدُونِ تَمْلِيكٍ ؛ لِأَنَّهُ رُبَّمَا يُعْطِيهِ السَّيَّارَةَ بِسِتِّينَ ألْفاً الْيَوْمَ وَيَمُوتُ الْأبُ غَداً.

Bai halatta ba. Domin amfani da ita kawai yake buƙata, watau ya riƙa hawa zuwa makaranta da komowa. Wannan kuwa zai samu idan aka sayi motar da sunan mahaifin, yaron kuma yana amfana da ita. Idan kuma ya rasu sai motar ta dawo a saka ta a cikin kayan gado. Bai halatta ba mutum ya mallaka wa ɗansa motar, domin maƙasudi dai shi ne a kawar da buƙatar da damuwar kawai. Wannan kuwa tana samuwa ba tare da mallakawa ba. Domin zai iya mallaka masa motar riyal dubu sittin a yau kuma gobe mahaifin ya kwanta ya mutu!

Ya cigaba da cewa:

فَلِذَلِكَ نَقُولُ : هَذِهِ مَسْأَلَةٌ يَجِبُ التَّفَطُّنُ لَهَا ، إِذَا كَانَ أَحَدُ الْأَبْنَاءِ يَحْتَاجُ إِلَى سَيَّارَةٍ وَالْآخَرُونَ لَا يَحْتَاجُونَ ، فَإِنَّنَا لَا نُعْطِي الْمُحْتَاجَ سَيَّارَةً بِاسْمِهِ ، وَلَكِنْ تَكُونُ السَّيَّارَةُ بِاسْمِ الْأَبِ ، وَهَذَا يَدْفَعُ حَاجَتَهُ بِانْتِفَاعِهِ بِهَا ، وَإِذَا مَاتَ الْأَبُ ترْجِعُ فِي التَّرِكَةِ. إِذاً الْقَوْلَ الرَّاجِحُ : أَنَّهُ إِذَا مَاتَ فَإِنَّهَا لَا تَثْبُتُ الْعَطْيَّةُ ، وَيَجِبُ رَدُّهَا فِي التَّرِكَةِ.

Shiyasa a nan muke cewa: Wannan mas’alar wajibi ne a faɗaku game da ita sosai. Idan wani daga cikin ’ya’ya yana buƙatar mota, sauran kuma ba su da buƙata, mu ba za mu sayo wa mai buƙatar motar da sunansa ba. Sai dai mu sayi motar da sunan mahaifin. Wannan zai kawar da damuwarsa ta hanyar amfaninsa da ita. Idan mahaifin ta rasu kuma sai motar ta komo cikin kayan gado. Don haka, maganar da ta fi rinjaye ita ce: Idan ya rasu kyautar da ya yi ba za ta tabbata ba, wajibi a mayar da ita a cikin kayan gado. (As-Sharhul Mumti’ Alaa Zaadil Mustaƙni’: 11/86).

Wannan a nau’in kyauta na farko ke nan.

A kan nau’in kyauta na-biyu mai alaƙa da babin Nafaƙah kuma akwai atharin Abubakar As-Siddeeƙ (Radiyal Laahu Anhu).

Al-Imaam Al-Baihaƙiy ya riwaito da isnadi sahihi har zuwa ga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) cewa:

إِنَّ أَبَا بَكْرٍ الصِّدِّيقَ - رَضِىَ اللَّهُ عَنْهُ - نَحَلَهَا جِدَادُ عِشْرِينَ وَسْقًا مِنْ مَالٍ بِالْغَابَةِ ، فَلَمَّا حَضَرَتْهُ الْوَفَاةُ قَالَ : وَاللَّهِ يَا بُنَيَّةُ مَا مِنَ النَّاسِ أَحَدٌ أَحَبَّ إِلَىَّ غِنًى بَعْدِى مِنْكِ ، وَلاَ أَعَزَّ عَلَىَّ فَقْرًا بَعْدِى مِنْكِ ، وَإِنِّى كُنْتُ نَحَلْتُكِ مِنْ مَالِى جِدَادَ عِشْرِينَ وَسْقًا ، فَلَوْ كُنْتِ جَدَدْتِيهِ وَاحْتَزْتِيهِ كَانَ لَكِ ذَلِكَ ، وَإِنَّمَا هُوَ مَالُ الْوَارِثِ ، وَإِنَّمَا هُوَ أَخَوَاكِ وَأُخْتَاكِ ، فَاقْتَسِمُوهُ عَلَى كِتَابِ اللَّهِ.

Mahaifinta Abubakar As-Siddeeƙ (Radiyal Laahu Anhu) ya ba ta kyautar ausuƙ ashirin na nonon dabino daga dukiyarsa da ta ke Al-Ghaabah, amma lokacin da ajalinsa ya zo sai ya ce: ’Yata, wallahi a cikin mutane babu wanda na fi son shi da wadata a bayana fiye da ke, kuma babu wanda na fi jin masa damuwan talauci a bayana fiye da ke. A baya na ba ki kyautar ausuƙ ashirin na nonon dabino. Idan da tun a lokacin kin yanke shi kuma kin ƙaddara yawan shi a wurinki, da ya zama na ki. Amma yanzu ya zama dukiyar gado. Kuma su yan'uwanki ne maza biyu da mata biyu, don haka ku raba dukiyar a yadda Littafin Allaah ya nuna. (As-Sunanul Kubraa: 12298).

Sannan Ibn Ƙudaamah (Rahimahul Laah) shi kuma ya ce:

فَصْلٌ : فَإِنْ خَصَّ بَعْضَهُمْ لِمَعْنًى يَقْتَضِي تَخْصِيصَهُ ، مِثْلَ اخْتِصَاصِهِ بِحَاجَةٍ ، أَوْ زَمَانَةٍ ، أَوْ عَمَى ، أَوْ كَثْرَةِ عَائِلَةٍ ، أَوْ اشْتِغَالِهِ بِالْعِلْمِ أَوْ نَحْوِهِ مِنْ الْفَضَائِلِ ، أَوْ صَرَفَ عَطِيَّتَهُ عَنْ بَعْضِ وَلَدِهِ لِفِسْقِهِ ، أَوْ بِدْعَتِهِ ، أَوْ لِكَوْنِهِ يَسْتَعِينُ بِمَا يَأْخُذُهُ عَلَى مَعْصِيَةِ اللَّهِ ، أَوْ يُنْفِقُهُ فِيهَا ، فَقَدْ رُوِيَ عَنْ أَحْمَدَ مَا يَدُلُّ عَلَى جَوَازِ ذَلِكَ

Fasali: Idan ya keɓance waninsu da kyauta domin wata ma’ana da ta hukunta a keɓance shi ɗin, kamar saboda wata buƙata ta musamman, ko zaunannen rashin lafiya, ko makanta, ko yawan iyali, ko shagaltuwansa da ilimi, ko dai makamancin hakan daga cikin ayyukan falala, ko kuma idan ya ƙi bayar da kyautansa ga wani ɗansa domin fasiƙancinsa ko bidiarsa, ko kuma domin zai yi amfani da abin da ya ba shi a kan saɓon Allaah, ko kuwa zai kashe shi a kan saɓon, to an riwaito wani abu daga Al-Imaam Ahmad mai nuni ga cewa ya halatta mahaifin ya yi hakan. (Al-Mughnee: 12/297).

Sannan kuma a cikin Zaadul Mustaƙni’ ya ce:

فَصْلٌ : يَجِبُ التَّعْدِيلُ فِي عَطِيَّةِ أَوْلاَدِهِ بِقَدْرِ إِرْثِهِمْ

Fasali: Wajibi ne ya yi adalci wurin kyauta ga ’ya’yansa da gwargwadon gadonsu. (As-Sharhul Mumti’Alaa Zaadil Mustaƙni’: 11/79).

A wurin sharhin wannan maganar sai Al-Allaamah Ibnul Uthaimeen (Rahimahul Laah) ya ce:

وَأَفَادَنَا الْمُؤَلِّفُ ـ رَحِمَهُ اللهُ ـ بِقَوْلِهِ : «فِي عَطِيَّةٍ» أَنَّهُ بِالنِّسْبَةِ لِلنَّفَقَةِ لَا يَكُونُ التَّعْدِيلُ بَيْنَهُمْ بِقَدَرِ إِرْثِهِمْ ، بَلْ بِقَدْرِ حَاجَتِهِمْ ، فَيَجِبُ التَّعْدِيلُ فِي الْإِنْفَاقِ عَلَى وَلَدِهِ بِقَدْرِ الْحَاجَةِ

Mawallafin (Allaah ya ji ƙansa) ya ba mu muhimmiyar faida a cikin maganarsa cewa: (wurin kyauta) cewa: Idan kyauta mai alaƙa da nafaƙah ce, to adalci a tsakaninsu ba ya kasancewa da gwargwadon gadonsu sai dai da gwargwadon buƙatarsu. Don haka ciyarwa a kan ɗansa yana wajaba ne da gwargwadon buƙatar ɗan kawai.

Sai kuma ya buga misali:

فَإِذَا قَدَّرَ أَنَّ الْأُنْثَى فَقِيرَةٌ ، وَالذَّكَرُ غَنِيٌّ ، فَهُنَا يُنْفِقُ عَلَى الْأُنْثَى وَلَا يُعْطِي مَا يُقَابِلُ ذَلِكَ لِلذَّكَرِ ؛ لِأَنَّ الْإِنْفَاقَ لِدَفْعِ حَاجَةٍ

Idan aka ƙaddara cewa yarsa mace faƙiriya ce (talaka) namijin kuma mawadaci, to a nan zai ciyar da macen, kuma ba zai bayar da abin da ya yi daidai da wannan ɗin ga namijin ba. Tun da ciyarwar domin gusar da damuwa ce.

Har zuwa inda ya ce:

وَلَوِ احْتَاجَ أَحَدُهُمْ إِلَى تَزْوِيجٍ وَالْآخَرُ لَا يَحْتَاجُ ، فَالْعَدْلُ أَنْ يُعْطِيَ مَنْ يَحْتضاجُ إِلَى التَّزْوِيجِ وَلَا يُعْطِي الْآخَرَ

Kuma idan ɗayansu ya buƙatu ga yin aure, ɗayan kuma bai buƙatu ba, to adalci a nan shi ne ya bai wa wanda ya buƙatu ga yin auren, amma ba zai ba ɗayan ba. (As-Sharhul Mumti’Alaa Zaadil Mustaƙni’: 11/80).

A ƙarshe kuma ya ce:

وَلِهَذَا يُعْتَبَرُ مِنَ الْغَلَطِ أَنَّ بَعْضَ النَّاسِ يُزَوِّجُ أَوْلَادَهُ الَّذِينَ بَلَغُوا سِنَّ الزَّوَاجِ ، وَيَكُونُ لَهُ أَوْلَادٌ صِغَارٌ ، فَيَكْتُبُ فِي وَصِيَّتِهِ : إِنِّي أَوْصَيْتُ لِأَوْلَادِيَ الَّذِينَ لضمْ يَتَزَوذَجُوا، أَنْ يُزَوَّجَ كُلَّ وَاحِدٍ مشنْهُمْ مِنَ الثُّلُثِ

Don haka ne ake ɗaukar abin da waɗansu suke yi a matsayin kuskure, watau inda waninsu yake aurar da ’ya’yansa da suka isa lokacin aure, sauran ƙananan kuma sai ya bar wasiyya cewa idan sun girma su ma a yi musu aure a cikin sulusin dukiyarsa kafin rabon gado!

Sai kuma ya kammala maganr da cewa:

فَهَذَا لَا يَجُوزُ؛ لِأَنَّ التَّزْوِيجَ مِنْ بَابِ دَفْعِ الْحَاجَاتِ ، وَهَؤُلَاءِ لَمْ يَبْلُغُوا سِنَّ التَّزْوِيجِ ، فَالْوَصِيَّةُ لَهُمْ حَرَامٌ

Wannan bai halatta ba, domin yi musu aure yana babin gusar da damuwa ko buƙata ne, su kuma sauran ƙananan ba su kai lokacin buƙatuwarsu ga auren ba. Don haka yi musu wasiyya da hakan haram ne. (As-Sharhul MumtiAlaa Zaadil Mustaƙni: 11/81).

ABUBUWAN LURA:

Bai halatta mahaifi ya keɓance wani ɗansa da wata babbar kyauta irin wannan ba, kuma dole ne idan yana raye ya koma ya daidaita shi da sauran ’ya’yansa: Ko dai ta hanyar karɓe wannan kyautar gaba ɗaya ko kuma ta hanyar bai wa kowannensu irin wannan kyautar a bisa ƙaidar: Kowane namiji ya samu rabon mata biyu.

Idan kuwa har ya rasu mahaifin bai gyara ba, to dole ne wanda aka fifita shi ya dawo da wannan kyautar a saka ta a cikin kayan gado, a raba da sauran ’yan uwansa. Sai fa ko idan duk magadan sun yarda, sun bar masa wannan kyautar kamar yadda mahaifinsu ya ba shi a lokacin yana raye.

Kyautar gida ko filin gina gida ba su shiga cikin kyautar warware buƙata ga wani ɗa ban da sauran ’ya’ya ba. Watau ba su yi daidai da kyautar da ya bayar domin biyan kuɗin magani ko kuɗin makaranta ko taimakawa don warware talauci ko wata buƙata da makamanciyar hakan ba. Domin ai kowane ɗa yana da buƙatar gida ko filin gida, ko da jariri ne kuwa. Wannan ce fahimtata a nan.

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments