Ticker

6/recent/ticker-posts

Neman Izinin Miji Fita Zuwa Ziyara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Matar da ta tambayi mijinta cewa za ta je gidan iyayenta ziyara, to ko ya halatta ta shiga waɗansu gidaje a can unguwa ko garin iyayen da ta je, ba tare da ta sake neman izinin mijin ba?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Yana daga cikin manyan haƙƙoƙin miji a kan matarsa cewa, ba za ta fita daga gidansa ba sai da izinin mijinta kuma da yardarsa. Kuma yana daga haƙƙoƙin ita matar a kan mijin ya riƙa yi mata izinin ta fita zuwa ziyarar iyaye ko yan uwanta musamman idan duk a gari ɗaya su ke zaune. Amma idan a wani gari ne mai nisa, a nan sai dai tare da muharraminta. Saboda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« لاَ تُسَافِرِ الْمَرْأَةُ إِلاَّ مَعَ ذِى مَحْرَمٍ »

Kar wata mace ta yi tafiya sai dai in tana tare da muharraminta. (Al-Bukhaariy; Muslim).

Bayan ta isa can, ba za a hana abin da al’ada ya gudana a kansa na leƙa gidajen waɗansu ’yan uwa da abokanan arziki ba, ko da kuwa tun farko ba ta tambaye shi ba. Domin rashin yin wannan kan iya haifar da matsala a tsakanin ta da waɗansu ’yan uwanta.

Hanya mai sauƙi dai kawai sai ta sanar da shi ta waya duk gidajen da ta buƙatu ga shiga, ko da kuwa a waɗansu unguwanni ko ƙauyuka ko ma garuruwan ne. Amma haƙiƙa ba ƙaramar magana ba ce, miji ya yi wa matarsa izinin ta tafi Kano daga Kaduna misali, amma kuma ya ji labarin tana Maiduguri ko Abuja ko Lagos ba da izininsa ba!

Haramun ne ga Mace ta fita gidan ta ba tareda izinin Mijinta ba. Duk matar dake fita ba tare da izinin mijinta ba, fushin Allah yana samunta har sai ta dawo ta nemi yafewarsa.

Wal Laahu A’lam.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments