Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tusar Da Yake Fitowa Mata Ta Gabansu

TAMBAYA

Assalamualaikum warahmatullah malam Allah ya saka da alkhairi, Muna godia da yawa.malam tambayata ita ce meye hukunci tusar da take fitowa mata ta gabansu, bata dubura ba, tana Kara Amma bata wari, kuma idan kana da alwala, idan kaita, shin alwalarka tananan kota warfare? Allah ya saka da alkhairi

AMSA:‼️

Wa alaikumu salamu warahamatullah,

Wannan iska da take fita daga gaba tana warware alwala, ko da babu wari a cikinta kuma ko da ba najasa bace, domin malamai sun tabbatar da cewa Annabi Muhammad ya bayyana cewa duk abin daya fito daga wurare biyu na jiki gaba da baya yana cikin abin dake karya alwala, kuma wannan ya shafi maza da mata daidai domin abubuwan dake karya alwala sun haɗa da fitar da iska daga baya ko daga gaba, ko da kuwa iska ce kawai ba tare da najasa ta fita ba

Dalilin wannan ita ce hadisin da aka ruwaito daga Manzon Allah inda ya ce Allah baya karɓar salla in babu tsarki wato alwala, kuma malamai sun bayyana cewa duk abin daya fito daga gaba ko baya yana karya alwala, don haka idan aka fitar da iska daga gaba, dole ne a sake alwala kafin yin salla ko wata ibada da ke bukatar alwala Wannan shi ne ra'ayin malamai hudu na mazhabobi - Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, da Hanbaliyya - domin dukkansu sun yarda cewa fitar da kowane irin abu daga al'aura, ko gaba ko baya, yana karya alwala.

Don haka, duk lokacin da kin ji wannan tusan ya fito alhali kina da alwala, tilas ne ki sake yin sabuwar alwala kafin ki yi salla. Amma idan wannan halin ya zama akai-akai, wato kullum ko yawancin lokaci haka yake faruwa har baki samun lokacin tsarki mai tsawo, to a wannan yana yin za ayi miki hukuncin mai uzuri kamar mai ciwon yoyon fitsari istihada za ki yi alwala bayan shigar lokacin kowace salla, sannan wannan alwalar tana wanka har zuwa fitowar lokacin sallar da take biye, kuma fitowar iskar bayan kin riga kin yi alwala a wannan yana yin ba ta sake warware miki alwalar ba, sai lokacin salla na gaba ya shigo. Allah Ya sanya mana sauki, kuma Ya bamu lada bisa wahalar da muke sha wajen neman tsarki.

Wallahu ta'ala aalam

✍️MT ABDULLAHI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments