Ticker

6/recent/ticker-posts

Kagaggun Labaran Hausa a Karni Na Ashirin Da Daya

Kagaggun Labaran Hausa a Karni Na Ashirin Da Daya

ƘAGAGGUN LABARAN HAUSA A ƘARNI NA ASHIRIN DA ƊAYA

Wallafar:

Dr. Aishatu Shehu Maimota
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Northwest, Kano.
Lambar Waya: +2348066054705
Imel: maimotaaisha@gmail.com

Rubutattun ƙagaggun labaran Hausa ɓangare ne na adabin Hausa da ya samu bayan Bahaushe ya sami ilmin karatu da rubutu na boko. Haka zalika adabin al’umma yana bunƙasa idan wannan al’umma tana karɓar duk wani cigaba da sauyi da zamani ya zo da shi. Haka ce ta faru ga ɓangaren ƙagaggun labaran Hausa ta yadda Hausawa ke karɓar duk wani cigaba da aka samu na zamani ta yadda za a dama tare da su. A taƙaice za a iya cewa da ilmin boko ya zo a ƙarni na ashirin an sami mawallafa ƙagaggun labaran Hausa tun daga kan Turawa har zuwa kan ‘yan ƙasa Hausawa, haka kuma da ƙarni na ashirin da ɗaya ya zo da fasahar intanet sai aka sami ɓullowar mawallafa ƙagaggun labaran Hausa a wannan ɓangare. Kasancewar ƙarni na ashirin da ɗaya ya zo da fasahar intanet ya sa duka al’ummomin duniya ciki har da Hausawa hankulansu ya karkata kan lalube da karance-karance da nazarce-nazarce kan shafukan intanet mai amfani da netiwak (network). Wannan dalili na samuwar ƙagaggun labaran Hausa a shafukan intanet ya sa aka yi tunanin samar da wannan ɗan littafi. An kawo bayanai dangane da samuwa da yawaita da kuma bunƙasar waɗannan labarai na Hausa na kafafen intanet. A ɓangare ɗaya littafin ya kawo yadda makomar wallafar littattafan ƙagaggun labarai ta koma a ƙarni na ashirin da ɗaya ta yadda idan ana son cigabansu da bunƙasarsu dole bayan an wallafa su a matsayin littattafai a kuma watsa su kan shafukan intanet. An kasa wannan littafi zuwa ɓangarori ko kashi-kashi guda huɗu. Kashi na farko gabatarwa ce inda aka kawo ma’ana da rabe-rabe tare da waiwaye kan tarihi da bunƙasar samuwar ƙagaggun labaran Hausa a zanguna daban-daban, kamar yadda masana irin su, Ɗangambo (1984/2008) da Yahaya (1988) da Mukhtar (2004) da Malumfashi (2006) da Ɗangambo (2024) suka kawo. A ɓangare na biyu kuma an bayyana yadda aikin wallafa da karatu, da cinikin  littattafan ƙagaggun labaran Hausa ta koma, ma, ma’ana ta ja da baya sakamakon karance-karance ta shafukan intanet.Ɓangare na uku kuma an bayyana samuwar ƙagaggun labaran Hausa a shafukan sada zumunta tare da mawallafan waɗannan shafuka da yadda suke samar da waɗannan labarai da duk wani abu da ya shafe su. A ɓankare na huɗu an samar da hanyoyi da ya kamata a tunkari nazari ko tarken ƙagaggun labaran Hausa a ƙarni na ashirin da ɗaya, wanda ya haɗa da yadda za a nazarci na littattafai da na shafukan sada zumunta na intanet, an kawo fitattun hanyoyi na masana kamar Mukhtar (2004) da Ɗangambo (2024) suka samar, sannan aka haɗa da wasu da aka samar a wannan littafi ta yadda za su tafi da tsarin nazari a ƙarni na ashirin da ɗaya. Littafin ya ƙara bayyana yadda sabuwar Fasahar Ƙirƙira ta AI  take tasiri a kan ƙagaggun labarai na Hausa. Daga ƙarshe an kawo rataye na wasu kalmomin fannu na adabi da Hausa da Turanci don sauƙaƙawa mai nazari fahimtarsu.Ana sa ran wannan litttafi zai yi wa masu nazarin adabin Hausa ɓangaren ƙagaggun labarai amfani ta yadda za su ga tarihin wanzuwar ƙagaggun labaran Hausa a zanguna daban-daban. Haka kuma zai yi wa masu nazari amfani ta yadda za su ga yadda ya kamata a tunkari nazari ko tarken ƙagaggun labaran Hausa rubutattu na littattafai da na shafukan intanet a ƙarni na ashirin da ɗaya.

A tuntuɓi marubuciyar domin fansar kwafe.

Post a Comment

0 Comments