Citation: Malami, U. T. (2026). “Nason Kirari a Waƙoƙin Baka: Nazari a cikin Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai” In Ɗunɗaye Journal of Hausa Studies, Vol. 04, No. 01, Pp. 49 – 56. www.doi.org/10.36349/djhs.2026.v04n01.007.
NASON KIRARI A WAƘOƘIN BAKA: NAZARI A CIKIN WAƘOƘIN ALHAJI MUSA ƊANBA’U GIDAN BUWAI
Na
Malami, Umar Torankawa
Sashen Gudanar da Shirye-shirye,
Rima Television Sokoto
Tsakure:
Sunan wannan maƙala shi ne nason kirari a waƙoƙin baka: nazari a
cikin waƙoƙin Alhaji Musa Danba'u Gidan Buwai. Manufar maƙalar ita ce nazarin waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai tare da fito wa da baiwa da hikimomi da zalaƙar harshe da Allah ya ba shi wadda yake amfani da su wajen
sarrafa kirari a cikin waƙoƙinsa. An gudanar da binciken ta hanyoyi daban-daban, waɗanda suka haɗa da tattaunawa da
abokan hulɗarsa, musamman waɗanda
suke taimaka masa, da kuma duba littattafai da kundin waƙoƙi. An kuma ziyarci
gidajen rediyo da talabijin kamar Rima Radio, Rima TV, da NTA Sokoto don
tattara bayanai. An dora binciken ne bisa ga littafin Farfesa Sa'idu Muhammad
Gusau mai taken Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Sakamakon bincike ya nuna akwai Kirari mai yawa a
cikin waƙoƙin nasa.
Gabatarwa
An tsara wannan maƙala ne da niyyar kallon yadda makaɗa da mawaƙa
suke sarrafa harshe cikin hikima da zalaƙa don su kambama ko kwanzarta uwayen gidansu ta nuna fifiko a tsakanin su da abokan adawa ko kuma nakasa wa ga
abokan hamayya. Alhaji Musa Ɗanba’u
Gidan Buwai ɗaya ne daga cikin shahararrun mawaƙan baka a ƙasar
Hausa, waɗanda Allah ya ba hikima da fasaha, da azanci wajen gudanar
da waƙa. An kalli wasu
daga cikin waƙoƙinsa, kuma aka yi ƙoƙari aka fito da
kirari a ciki. Kamar kowane
nazari akan sami tsari na musamman da ya kamata a gabatar kafin gudanar da shi, wannan maƙala an dubi waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u ta hanyar nazarin kirarin da suke ɗauke da su da kuma kafa misalai daga ɗiyan waƙoƙinsa tare da yin sharhi dai-dai gwargwado. An kasa wannan aikin maƙala zuwa matakai
guda huɗu kamar haka:- Mataki na farko kuwa shi ne gabatar
wa ga aikin gaba ɗaya sai mataki na biyu inda aka yi waiwaye akan yadda masana
da manazarta suke kai komo waje tattara bayani game da ma’nar kirari da
kashe-kashensa. Mataki na uku ya ƙunshi bayanai a kan kirari da yadda Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ke sarrafa shi a cikin waƙoƙinsa tare da kawo
misalai daga cikin wasu ɗiyan waƙoƙinsa da kuma yin sharhi dai-dai gwagwado. Mataki na huɗu kuwa shi ne kammalawa.
Kirari
Kirari na nufin
wasu zaɓaɓɓun kalmomi da ake furtawa a tsare don zuga ko kambamawa.
(CNHN: 2006:466). A ra'ayin Gusau (1984:1) ya bayyana kirari da
cewa "wata tsararriyar magana ce, 'yar doguwa ta hikima, da akan
shirya musamman don kambama mutum ko wani abu, ko
kuma mutum ya yi don kambama kansa da kansa".
Shi kuwa Umar (1987:3) ya ce "kirari
wasu kalmomi ne na kambamawa ko cicciɓawa da ake yi wa wani ko mutum ko shi yake yi wa kansa da ke
zuwa ta sigar siffanta mutum ko wani kan shahararren ƙarfi ko alfarma ko daraja. Ya ƙara da zayyano abubuwan da ake kirari da su waɗanda suka haɗa da giwa da zaki
ko aljani da gobara da baƙin kumurci da
iyaye da sauransu". Har wa yau "kirari na nufin waɗansu irin maganganu ne da ake yi wa sarakuna ko muhimman
mutane da take bayyana halayensu da kuma kamanninsu ta hanyar kambamawa".
(Kafin Hausa, 1981:2). "Kirari wasu maganganu ne na zuga da
kambamawa da suka shafi halaye da akan tsara cikin hikima da
balagar harshe".(Garba 1998:21). Haka kuma "kirari
wata tsararriyar maganar hikima ce da akan shirya ta don a yabi wani mutum ko a
bayyana halayyar wani abu ko yanayinsa ko siffarsa".
(Galadanci da wasu, 1993)
Ta la'akari da waɗannan ra'ayoyi na masana da suka gabata a kan wannan nau'in
azanci za a iya cewa, kirari wasu maganganu ne na hikima da
fasahar harshe da akan tsara don a yabi wani mutum ko a bayyana halayyar
wani abu ko yanayinsa ko siffarsa ta hanyar zuga ko kambamawa
ko cicciɓawa da nufin ɗaukaka
darajarsa ko ƙimarsa ko ƙarfinsa
ta nuna ƙauna ko ƙiyayya.
Wannan nau'in na
daga cikin zantukan azanci da makaɗa ke
amfani da shi don su zuga ko kambama wani ko koɗa kansu da kansu don nuna bajinta da faranta ran ubangidansu ko
sanya shi yin kyautar da bai tashi yi ba ko don a razana abokan
gaba. Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai
na daga cikin makaɗan baka na Hausa da suke amfani da wannan nau'in kamar yadda
misalai za su nuna haka daga cikin wasu waƙoƙinsa.
Kirari Mai Nasaba
Wannan kirari na nasaba ya danganci kirari da mawaƙa suke yi wa al'umma musamman uwayen gidansu ta
dangantasu da kakanninsu ko iyayensu ko matansu ko 'ya'yansu ko iyayen gidansu
da kuma aminansu da sauransu. Anan za muga yadda Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai ya yi amfani da kirarin nasaba a waƙoƙinsa kamar haka. A cikin waƙarsa ta Salihu Barade mai taken "Salihu
baa jan ka ran yaƙi"
Gindin waƙa: Yara ku tashi za ni Wamakko,
'Yan’amshi: Don mu
ishe Barade garkarsa,
Salihu
ba a jan ka ran yaƙi,
Jagora: Kar ka sake Barade Wamakko,
Kai ka
halin Barade Jaɓɓi,
Ka yi
halin Ruwa Mai Sandare,
Ka yi
halin Barade Aliyu,
'Yan Amshi: Kai ka
halin Barade Gainako. +2
Jagora: Sarakunan ga da ni lissahwa,
Dud
martabarsu tana hannunka,
'Yan Amshi: Kai ka
hwaɗi a yarda ko dole.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: waƙar "Salihu ba a jan ka ran yaƙi”)
A wannan ɗan waƙar Musa Ɗanba'u ya yi amfani da azancin magana
na kirari da ya danganci nasaba inda ya kawo bayani mai nuna cewa gwarzonsa shi
ne Barade, kuma ɗan Barade Jaɓɓi kuma jikan Barade Sandare da Barade Aliyu da kuma
Barade Ganako. Duk wata martaba da daraja da nagarta da suke da ita yanzu, shi
Barade Salihu shi ne yake riƙe da ita. Ya ƙara kambama shi ta nuna a yanzu ba wani
mai faɗa aji kamarsa tun da shi ka riƙon Wamakko.
Haka kuma a waƙar Mukhtari Shehu Shagari
mai take "Ɗan Marafa jikan Basharu" a wannan ɗan waƙa Alhaji Musa Ɗanba'u ya zo da
misalin kirarin nasaba kamar haka:-
Jagora: Ɗan Marafa jikan
Basharu,
Baba uban Abdullahi,
Lahiya
namijin zaune.
Jarumi na Obasanjo,
'Yan Amshi: Na Atiku Turaki,
Maza
suna shakka ja nai.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai:
waƙar "Ɗan Marafa Jikan Basharu")
Wannan ɗan waƙar ya zo da kirarin nasaba ne ta danganta gwarzonsa da cewa shi ne jikan
Basharu kuma uban Abdullahi. Haka kuma a layi na huɗu da na biyar ya
yi amfani da kirarin nasaba amma ta haujin iyayen gida da aminai, inda ya ambaci
gwarzonsa da dangatashi da iyayen gidansa wato shugaban ƙasa Obasanjo da Mataimakinsa Alhaji Atiku ta nuna zamantakewarsu a
matsayinsa na minista a cikin gwamnati, wato ya yi masa kirari da cewa shi
gwarzo ne maza suna saunarsa don ba ya ɗaukar raini.
Haka ma a wannan ɗan waƙar ya yi masa
kirarin nasaba ta danganta shi da matansa kamar haka
Jagora: Mijin
Salamatu dottijo,
Mijin Maryam mai bantsoro,
Mijin Kuluwa 'yar Shehu,
Mijin Sa'a mai sa'a,
'Yan Amshi: Ba a
kai maka ganganci,
Kuma
bai ɗaukar wasa.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai: waƙar "Ɗan Marafa Jikan Basharu")
A wannan ɗan waƙar Makaɗin ya bayyana nasabar zamantakewa ta miji da mata, inda ya bayyana
dangantakar gwarzonsa da matansa ta yi masa kirari da ambaton sunayensu wato
mijin Salamatu da Maryam da Kuluwa da kuma Sa'a.
Ita ma waƙar Yusuf Suleman
mai taken: "Isuhun Sulemanu Minista" Makaɗin ya yi amfani da
kirarin nasaba wajen fitowa da tarihin gwaninsa don ya nuna wa abokan adawa
cewa fa ubangidansa mutunne sananne kuma mai asali mai kyau da kuma ɗaukaka a idon
al'umma. Ga abin da ya ce:
Jagora: Bari dai in ta da gwanina ni,
Ina
gwanin wani ga nawwa,
Isuhu na Shehu na Tambari,
Arzukinka
ya fasa dutsi,
'Yan Amshi: Ka ƙara hattara Isuhu na
Sada.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai: waƙar "Isuhun Sulemanu Minista")
Wannan ɗan waƙa ya zo da kirarin nasaba inda mawaƙin ya yi kirari ga
gwaninsa da danganta shi da yayanninsa wato ya nuna cewa gwarzonsa ƙane ne ga Shehu Suleman
da kuma Tambari Suleman. A nan da Shehu da
Tambari duk yayanni ne ga gwaninsa. Haka ma a layi na
biyar ya ƙara danganta shi da Sarkin Musulmi
Sada don nuna zumunci da soyayya da ke tsakanin gwaninsa da mai
alfarma Sarkin Musulmi na ashirin, wato
Muhammad Sa'adu Abubakar na uku da ƙara nuna cewa shi gwarzonsa yana daga cikin Magada Sarautar.
A waƙar Shugaban ƙasar Nijar Tanja mai taken "Shugaban Ƙasar Mai Sulken Yaƙi." Ɗanba'u ya zo da irin wannan azancin magana na kirarin nasaba kamar yadda zaa gan shi a cikin wannan ɗan waƙa:-
Jagora: Dogo ɗan Lamiɗo,
'Yan Amshi: Gaba jikan Lamiɗo,
Jagora: Ga ɗan HadiTanja,
'Yan Amshi: Baban Hadi Mamman,
Jagora: Na
Laraba mijin Faɗima,
Giwa sha masu,
'Yan Amshi: Mai
maganin walaƙanci,
Tanja ɗan Mamman.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwa: waƙar "Shugaban Ƙasar Mai Sulken Yaƙi")
A cikin wannan ɗan waƙar Alhaji Musa Ɗanba'u ya yi amfani da nau'in azancin
magana na kirarin nasaba inda ya danganta Tanja da kakanninsa da uwayensa waɗanda suka haɗa da babansa Lamiɗo da kakansa Lamiɗo da kuma mahaifiyarsa
Hadi, duk don nuna asalinsa ta danganta shi da su. Haka kuma a layi na uku ya
ambaci nasabar ta danganta shi da 'ya'yansa da matansa "Na Laraba mijin Faɗima"tare
da siffanta shi da wasu kalmomi na kambamawa da cicciɓawa kamar dogo da giwa.
Haka kuma Ɗanba'u ya zo da
irin wannan kirari na nasaba a waƙar Sarkin Yamman
Sakkwato Aliyu Magatakar daWamakko mai taken "Ƙi Sake Bajinin Gwarzon Maza Ali Sarkin Yamman Sakkwato".
Jagora: Kai bari dai in tada gwanina,
Bari
dai in wasa ubana,
Ɗan Barade jikan Umar,
Baba
gizago baka da sabo,
'Yan Amshi: Mai
sassaƙa ya tsare
hannunsa,
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai: waƙar "Ƙi sake bajinin gwarzon
maza, Ali Sarkin yamman Sakkwato")
A wannan ɗan waƙa Musa Ɗanba'u ya yi amfani da dabarar
azancin kirarin nasaba inda ya danganta gwarzonsa Aliyu Magatakarda Wamkko da cewa ɗa ne ga Barade Jaɓɓi shi kuwa Barade
Jaɓɓi ɗa ne ga Baraden Wamakko Umaru, wato ya nuna nasabar gwarzonsa fitowa da alaƙanta shi da Ubansa da kakansa cewa duk sun yi Baraden Wamakko, musamman wannan nasaba ta fito ne a layi na
uku.
A cikin waƙa Mai taken
"Janjunan Gidan Buwai, Arna Ba Su Ja Da Kai"
Ɗanba'u ya yi amfani da irin wannan azanci na kirarin nasaba a lokacin da yake zuga
ubangidansa da ya yunƙura ya karɓi
Raɓa. Ga abin da ya ce
Jagora: Ga maganar da niy yi ma,
Janjunan
Gidan Buwai,
Jikan Audu Bayero,
Shin
wai mi ka kai da Rara,
Kimtsa
ka amshe Raɓa,
'Yan Amshi: Komai
a kai ayi.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai:
waƙar "Janjunan Gidan Buwai, Arna Ba Su
Ja Da Kai")
Wannan kirarin ya zo ne a layi na uku na ɗan waƙar inda ya zo da nasabar ta nuna cewa ubangidansa jika ne
ga Audu Bayero. Wato Sarkin Raɓa da ya gabaci
wanda ke kan karaga, shi kuwa Audu Bayero jika ne ga Mujaddadi Shehu Usmanu Ɗanfodiyo.
Kirari Mai Dangantawa
Wannan wani nau'in kirari ne da mawaƙi yake yi wa iyayen gidansa ko waɗanda suke yi wa waƙa don su samu fada ko don su yi musu wata kyauta ta musamman. Misali Alhaji
Musa Ɗanba'u cikin waƙar Sarkin Musulmi Macciɗo mai taken"Gwauron Giwa Jikan Hasan Ɗan Amadu", ya
yi masa kirari ta siffanta shi da waɗansu kalmomi masu nuna kwarjini ga idon
jama'a kamar haka:-
Jagora: Tauraron
duniya
Na Maisango
'Yan Amshi: Baba Zakin
na Mu'azu
Hasken musulmin
duniya
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai: waƙar "Gwauron
Giwa, Jikan Hasan, Ɗan Amadu")
Wannan ɗan waƙa Ɗanba'u ya zo da kirarin wani inda ya yi
wa gwarzonsa kirari ta fitowa da kalmomi masu nuna kwarjini da ƙarfi a tsakanin jama'a, wato nuna ɗaukaka kan abokan
adawa. A layi na farko ya yi amfani da kalma mai nuna cewa gwarzosa kwarjininsa
da farinjininsa ya game duniya kamar yadda taurari suke bice sama da haskake
duniya. Haka ma a layi na uku ya kira shi da zaki don ya fayyace irin ƙarfinsa a tsakanin jama'a da 'yan sarki kamar yadda zaki
yake taƙama ta nuna ƙarfi da kwajini adawa. A layi na huɗu ya ambace shi da hasken musulmin duniya wato alheri ne ga musulmin duniya, kuma ya
zo da sigar kambamawa a wannan kirari domin nuna irin yadda ubangidansa yake
yin ƙwazo wajen hidima ga al'umar musulmi na
ganin adinnin musuluci ya sami ɗaukaka.
A waƙar Attahiru Bafarawa mai taken "Bai San Tsoro Ba,
Bafarawa Attahiru" Musa Ɗanba'u
ya yi amfani da irin wannan kirarin a cikin waƙar kamar haka:-
Jagora: Ga dai mulki
gare shi,
Ga nera ta tsaya,
Ga jama'a nan gare shi,
Ga ilimi ya yi yawa,
Turanci,
'Yan Amshi: Ko Amerikan gogawa su kai.
Jagora: Mijin Alhajiya Amina,
Angon
Murja,
Uban
Sagiru da Babangida,x2
'Yan Amshi: Shelto mai maganin ƙuda ko da sun yawa.
(Musa Ɗanba'u: waƙar "Bai San Tsoro Ba,
Bafarawa Attahiru")
Wannan ɗan waƙar Ɗanba'u ya yi kirari ga gwarzonsa Alhaji
Attahiru Bafarawa ta kambama shi da cewa shi ƙwararre ne wajen gudanar da mulki, haka kuma shi attajiri ne da ke tallafa wa
jama'a don haka al'umma su ke ƙwaunarsa. Har wa
yau makaɗin ya ci gaba da yi masa kirari ta danganta shi da matansa da kuma
‘ya’yansa da kuma mallakar dukiya da Allah ya hore masa, ga kuma jama'a da suke
ƙaunarsa. Ya cigaba da yi masa kirari
inda ya kambama shi ta nuna ƙwarewa a fannin ilimi
da iya Turanci inda ya nuna ko daga Amerika ka fito albarka.
Haka kuma a ɗan waƙar da yake bi masa Ɗanba'u ya yi masa kirari ta siffanta
shi da Shelto wato wani abu da ke maganin ƙuda komai yawansu da zaran an fesa shi za a ga sun mutu, to haka gwarzonsa
yakan watse taron magabta komi yawansu.
Ita ma waƙar Matawallen
Sakkwato mai taken "Ɗan Waziri Ka Ƙara Shirawa, Aminu Yau Kai Am Matawalle", tana da
irin wannan kirari, inda Ɗanba'u ya yi
amfani da kalmomin siffantawa don ya yi kirari ga ɗaya daga cikin
aminan Matawalle da suka yi masa kyauta kamar haka;
Jagora: Ga dogo
mai halin kyauta, x2
Kyautarka
ta fi jarin yaro,
Rai ya
daɗe ma Kabiru Marahwa,
Ɗan Uban ƙasar
Alkammu,
Kabiru rini kere itace.
(Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai: waƙar "Ɗan Waziri ka ƙara shirawa")
A wannan ɗan waƙa Musa Ɗanba'u ya yi wa
gwarzonsa kiarari ta amfani da kalmomin siffantawa, inda
daga farko ya ambace shi da dogo. A layi na biyar kuwa ya kira shi da rimi kere itace duk dai yana ƙoƙarin nuna cewa gwarzonsa kamar yadda rimi ke kere itace saboda tsayinsa haka
ubangidansa Kabiru Marafa a duk inda ya shiga za a gan shi wato kamar yadda
yake da tsawo haka kyautarsa da alherinsa yake. Ya ƙara da nuna irin yadda yake kyauta tamkar ya baka jari ne saboda yawanta, "kyautar
ka ta fi jarin yaro". Haka kuma a wani wurin a cikin wannan ɗan waƙa mawaƙin ya yi masa
kirarin nasaba ta nuna cewa ɗa ne ga uban ƙasar Akamu wato Marafan Alkamu mahaifinsa ne don haka gwazonsa Ɗangaladima ne a masarautar Alkamu ko a ce Yarima.
Kirarin Kwatantawa
Makaɗan Hausa na amfani da wannan dabara ta
kirari ta amfani da salon kinaya ko alamci musamman lokacin da suke kambama
gwarazansu, inda suke siffanta su da dabbobi ko ma wata halitta ta Ubangiji don
su bayyana su ta yadda za su nuna fifiko tsakaninsu da abokan hamayya ko
magabta. Alhaji Musa Ɗanba'u Gidan Buwai yana amfani da
wannan dabara ta kirarin kwatantawa a cikin waƙoƙinsa kamar yadda misalai za su nuna.
Wannan waƙa ta Alhaji Yusuf
Suleman mai taken "Na Bello Ba A Ja Nai A Ci Riba, Isuhun Sulemanu Minista".Alhaji
Musa Ɗanba'u Gidan Buwai ya yi amfani da
wannan azancin magana na kirari kamar haka:-
Yaro: Dutsin fashin tama jikan
Ali,
Gamji matattarar namun
daji,
Kowaj
ji yunwa ya gangaro,
Ya ɗauki abinci ya kai gida,
'Yan Amshi: Kowag ganai
yana gyara gidansu.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar "Na Bello Ba A Ja
Nai A Ci Riba")
A wannan ɗan waƙar ya zo da kirarin kwatantawa ne ta amfani da salon jinsantarwa mai nuna abuntarwa, inda a layi na farko da na biyu ya zo da kalmomin abuntarwa ta ambatonsa da dutsin
fashin tama wato ya nuna irin ƙarfin da ubangidansa yake da kamar yadda dutsin fashin tama
yake a tsakanin duwatsu haka ubangidansa yake. Don haka maƙiya da mahassada su yi haƙuri ba su iyawa. A
layi na biyu kuwa ya faɗi irin alheri da yawan kyauta da
gwarzonsa ke yi ta yi masa kinaya da inuwar gamji wadda ke da faɗi da yalwa. Ta
nuna hakan gwarzonsa yake biya wa al'umma buƙatunsu na yau da kullum, gwargwadon hali.
Ita ma waƙar PDP mai taken
" PDP Hasken
Najeriya, Fati Mai Ƙarhi Da Martaba". Musa Ɗanba'u ya yi amfani da wannan kirari na kwatantawa kamar haka:-
Jagora: Hajji
Modi na Yabo a gaishe ka,
Zaki mai ƙarhin mutum dubu,
Ka gama da 'yan kwakwar baya,
Yanzu kwakwa ba ta da
tasiri,
'Yan Amshi: Sai
dai su yi bammi su sha giya.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan
Buwai: Waƙar "PDP Hasken Najeriya")
Wannan ɗan waƙa yana ɗauke da azancin magana a layi na biyu inda mawaƙin ya ambaci gwarzonsa ta siffanta shi da Zaki,wato ya yi masa kinaya ta nuna yadda Zaki yake da ƙarfi da kwarjini a tsakanin dabbobi haka ubangidansa yake
a tsakanin jama'a kuma ya yi amfani da ƙarfin ya murƙushe abokan gaba ko adawa.
Haka ma a waƙar Alu Magatakarda
Wamakko mai taken "Aliyu Zaɓaɓɓen Gwamna", a nan ma Ɗanba'u ya zo da irin wannan kirarin a ɗan waƙar da yake tafe kamar haka:
Jagora: Tauraron
gabas mijin Arziki,
Gaishe
ka na Murja,
Ɗan Garba Farin wata
Ali,
'YanAmshi: Ka iske
mutanen birni,
Har da mutanen ƙauyuka.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: "Aliyu Zaɓaɓɓen Gwamna")
Kirarin kwatantawa ya zo ne a farkon
layi na ɗaya da kuma tsakiyar layi na biyu a wannan waƙa, inda mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya wajen
yin kirari ga gwarzonsa ta fuskar kiran sa tauraro, wato yadda tauraro yake haskewa haka ubangidansa yake. A
layi na uku kuwa ya yi amfani da kalmar farin wata don nuna irin yadda farin
wata ya zame game duniya, haka wanda ya yi wa waƙa yake. Haka shi ma ubagidansa alheri da kyautarsa ta game jama'a na birni
da ƙauyuka.
Kirarin Koɗa Kai
A wannan kirari mutum ko mawaƙi kan yi wa kansa kirari don ya koɗa kansa ko kuma ya nuna fifikonsa da
sauran abokan kiɗansa ko waƙa ko ma don firgita abokan gaba ya nuna
ƙwarewarsa ta fi tasu da makamantan
haka. Alhaji Musa Ɗanba'u ya zo da irin wannan dabara ta azancin magana na koɗa kai a waɗansu ɗiyan waƙoƙinsa kamar haka.
A waƙar Sarkin Musulmi
Macciɗo mai taken "Gwauron Giwa, Jikan
Hasan Ɗan Amadu", Ɗanba'u ya zo da irin wannan dabara ta azancin magana na yi wa kansa kirari
kamar haka:-
Yaro: Ɗanba'u mai kiɗa,
Mamaki ɗai ni kai,
Mamakin
duniya,
Ni ko
duniya,
Ina jin
tsoron ki,
Ka ga
harakar 'yan Adam,
Tana
ban mamaki,
Wasu
sun ce,
An hana
ni waƙa nan Sakkwato,
Ƙarya ƙaryar ƙasa,
Zancen
banza,
Don ƙarya ba magana ba,
Wasu
sun ce,
An hana
ni waƙa,
Nan
Sakkwato,
Ni ko
na gaya masu,
Kura ko bata ci,
Kare na saunan ta,
Yanzu ko da ba ni waƙa,
Ƙafata ta tsaya,
Tun da duk Nijeriya,
Wani mai kyauta da naira,
Ƙasar nan na sani,
Wani mai kyauta da mota,
Ƙasar nan na sani,
Ko ba Nijeriya ba,
Musa in tsallake,
In tahi Nijar,
Mu iskikke,
Tanja Mammadu.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar Gwauron Giwa, Jikan
Hasan Ɗan Amadu")
A wannan ɗan waƙa kirarin koɗa kai ya fito ne tun daga layi na goma sha
bakwai zuwa na ƙarshe inda ya nuna cewa ga yanzu fa ya
wuce a yi mai raini don ya kai duk inda mawaƙi, ka son kaiwa ta amfani da karin magana mai nuni ga habaici don ya ƙara nunawa magabta da masu kushe, da cewa "Kura ko ba ta ci, kare na saunan ta" wato ga yanzu sai dai su yi haƙuri don na gaba ya yi gaba na baya ko sai labari, inda ya
siffanta kansa da kura su ko magaba da kare ya siffansu wato akwai tazara mai
yawa a tsakaninsu,sai su yi haƙuri
da ikon Allah. Har wa yau dai ya kara nuna fifikonsa da su a layi na sha tara zuwa ƙarshen ɗan waƙar da cewa “'Yanzu ko da ba ni waƙa, ƙafata ta tsaya”. Wato ya riga ya kai duk inda makaɗi yake buƙatar kaiwa don nuna gwaninta da samun karɓuwa ga jama’a na ciki da wajen ƙasar nan.
A waƙar Macciɗo Yarin Gandi, Ɗanba'u ya yi
amfani da wannan dabara ta kirarin kai a wani ɗan waƙa kamar haka:-
Jagora: A ni na sha wahala a Raɓa,
Haji Ɗanba'u mai waƙa,
Ni na
sha wahala Raɓa,
Ga
siyasa wadda ta zarce,
Mamaki
ya kama ni,
Ana yi
man harakar ganganci,
Tun da ƙarhina bai zo ba,
Ɗanba'u ba zai magana ba,
To yanzu kan ƙarhina ya kai,
Mai auren matar mai waƙa,
Tun da siyasa tai muku fancal,
Don Allah ka sako akuyar nan,
'Yan Amshi: Ta sha ruwanta ta koma garge.
(Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai: Waƙar “Uban Aminu Sadaukin Sarki”)
A wannnan ɗan waƙar Ɗanba'u ya zo da kirarin koɗa kai, inda a layi na tara ya nuna cewa yanzu kan ƙarfinsa ya kai, don haka ba zai aminta
da reni ba da harkar ganganci da ake masa a baya ba. Ya yi amfani da salon dabbantarwa don ƙara fitowa da kirarin a layi na goma sha biyu inda ya yi amfani
da akuya mai makon ya ambaci sunan matarsa da wani ɗan siyasa ke aure
sai ya yi dabbantarwa da cewa to yanzu kan ƙarfinai ya kai kuma ga shi siyasarsu ta fanɗi wato tai musu
facal, fancal na nufin harakarsu ta siyasa duk ta kwaɓe ba su da wata
madogara. To a nan ne mawaƙin ya yi dabbantarwa
da cewa 'Don Allah ka sako akuyar
nan, ta sha ruwanta ta koma garge”,wato a sako masa matarsa da yake aure don ga
yanzu mijin ba shi da ƙarfin riƙe ta, sanadiyar faɗuwa zaɓe da ya yi.
Kammalawa
A wannan takarda an fahinci yadda Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai ya yi amfani da dabaru da hikimomi
daban-daban ya saka kirari a cikin waƙoƙinsa, mabambanta da ya yi saboda isar da saƙon da ke ciki. A takardar an ga yadda kirari ke ƙawata waƙoƙin baka na Hausa don yin armashi wajen rerawa da kuma
samar da nishaɗi ga masu sauraro ba tare da gajiyawa ba ko ƙosawa. An kuma ga yadda yake nuna yabo da kambama uwayen gidansa ko kushewa
da nakasa abokan adawar uwayen gidansu.
Manazarta
CNHN, (2006) Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello
University Press.
Garba, M. (1998).
"Azancin Magana A Waƙoƙin Makaɗan Baka". Kundin
Digiri Na Biyu. Kano: Jami'ar Bayero
Galadanci, M. K. M. da
wasu (1993), Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare Longman Nigeria Plc.
Gusau S. M. (1984)
‘Nazarin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Baka na Hausa’. Cyclostyled Edition.
Gusau, S.M.
(2002). Sarkin Taushi Salihu Jankiɗi. Nazari
da Ratayen Wasu Waƙoƙinsa
Baraka Publishers Limited, Kaduna.
Gusau, S.M.
(2023). Jagoran Nazarin Waƙar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Gusau, S.M.
(2015). Mazhabobin Ra'i da Tarke A Adabi
Da Al'adu Na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.
Gusau, S.M.
(2016). Makaɗa Da Mawaƙan Hausa, Littafi
Na Biyu.Kano: Century Research
and Publishing Limited.
Umar, M.B. (1987). Dangantakar
Aadabin Baka da Al'adun Gargajiya.Kano, Nigeria: Trumph Publishing Company.
Torankawa, M.U
(2006). "Adon Harshe A Waƙoƙin Sarauta Uku Na Makaɗa Rabo
Ango Yabo" Kundin Difilomar gaba da Digirin Farko (PGDHS) A Fannin Hausa. Kano: Jami'ar
Bayero.
Torankawa, M.U
(2025) “Nazarin Azanci A cikin Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai” Kundin Digiri Na Biyu. Sakkwato:
Jami’ar Usmanu Danfodiyo.
Yahya, A.B.
(2016). Salo Asirin Waƙa.
Sokoto: Guaranty Printers.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.