Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Nafila Bayan Sallar Asuba

TAMBAYA

Salam Malam dafatan kana lafiya ya karatu, Allah ya karawa rayuwa Albarka

Tambaya?

Meye hukuncin yin sallar nafila bayan sallar Asuba ya halatta ko akasin hakan?

Bissalam

AMSA:‼️

Wa alaikumu salaam warahmatullah,

An haramta yin sallar nafila bayan an gama sallar Asuba, har sai rana ta fito sosai wato ta tashi kimanin tsawon mashi daya, kusan minti 15 zuwa 20 bayan fitowarta. Wannan hukunci ne da jumhur malamai Hanafiyya, Malikiyya, Shafi'iyya, da Hanbaliyya suka yarda a kai, sabanin sallar da take da dalili na musamman kamar sallar da aka bata (ƙada'i).

Hujjar wannan ita ce hadisan da Manzon Allah ya hana yin salla a wasu lokuta guda uku, daya daga cikinsu shi ne bayan sallar Asuba har saj rana ta fito. Daga cikin hadisan akwai fadin Manzon Allah : "Babu salla bayan Asuba har sai rana ta fito, kuma babu salla bayan La'asar har sai rana ta faɗi" (Bukhari da Muslim ne suka ruwaito). Haka kuma an ruwaito daga Umar Ibn Al-Khattab (RA) inda ya ce Manzon Allah ya hana yin salla bayan sallar Asuba har sai rana ta fito, da kuma bayan sallar La'asar har sai rana ta faɗi.

Dalilin wannan hani, a cewar malamai, shi ne domin toshe hanyar da za a rikita al'amarin bautar rana da ake yi a wancan lokaci domin kafirai suna sujjada wa rana a lokacin fitowarta da faduwarta, don haka Musulunci ya bambanta al'ummar Musulmi da wannan hali ta hanyar hana salla a wancan lokacin na musamman.

Sai dai akwai wasu 'yan bambance-bambance a tsakanin malamai kan wasu salloli na musamman dana ke so na yi bayani akai:

1: Idan wani ya bar wata sallar farilla ya manta ko ya yi barci har lokacinta ya wuce, sa'an nan ya tuna bayan Asuba, jumhur malamai sun ce zai iya yin ƙada'inta ramawa ko da a wannan lokacin ne, domin akwai dalili na musamman wato uzuri.

2: Idan wanda bai yi raka'atanil fajir raka'a biyu na kafin farilla ba kafin ya shiga masallaci, ya halatta ya yi ta bayan sallar farilla, kamar yadda hadisin Ƙais bin Amr ya nuna, inda Manzon Allah ya gani ya yi raka'a biyu bayan Asuba, sai ya tambaye shi, ya ce bai yi sunnar Asuba ba tukuna, Manzon Allah bai hana shi ba.

Amma in banda wadannan hallayen na musamman, yin nafila ba tare da wani dalili na musamman ba a wannan lokacin bayan Asuba har zuwa fitowar rana haramun ne. Allah Ya kara mana ilimi mai amfani.

Wallahu ta'ala aalam

✍️MT ABDULLAHI

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments