𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salamu Alaikum akaramakallah barka da wannan lokaci don Allah a amsa min wannan tambayar; shin dole ne sai mace ta yi iƙama idan za ta yi sallah, kamar yadda maza suke yi idan za su yi sallah?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Toh shi Sallah dai
babu wani banbanci a tsakanin Namiji da kuma mace a wajen yin sa. Ya tabbata a
cikin Hadisin Maalik Bn Al-Huwairith (Radiyal Laahu Anhu) cewa Manzon Allaah
(Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« ﻭَﺻَﻠُّﻮﺍ
ﻛَﻤَﺎ ﺭَﺃَﻳْﺘُﻤُﻮﻧِﻰ ﺃُﺻَﻠِّﻰ »
Kuma ku yi sallah
kamar yadda kuka ganni ina yin sallar. (Sahih Al-Bukhaariy: 631)
Wannan gamammiyar
dokar ta haɗe maza da mata daga
cikin musulmi, sai in an samu wurin da ya cire matan daga hakan.
Al-Imaam Al-Mujaddid
Al-Albaaniy a ƙarshen littafinsa: Sifatu Salaatin Nabiy (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya baya yiana cewa: Babu wani abinda ya zo a cikin
Sunnah da yake hukunta cire mata a cikin siffar Sallar Annabi (Sallal Laahu
Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Har kuma ya kawo maganar da Ibn Abi-shaibah ya
riwaito da ingantaccen isnadi daga Ibraahim An-Nakha’iy
(Rahimahul Laah) ya ce:
ﺗَﻔْﻌَﻞُ ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﻓِﻲ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓُ ﻛَﻤَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻞُ ﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ
Mace a cikin sallah
tana aikata irin abinda namiji yake aikatawa ne. (Aslus-Sifah: 3/1040)
Sabida haka yadda Maza
suke yi da kuma yadda Mata za su yi nasu kamar duk abu ɗaya ne kamar yadda
Sunnar Manzon Allah (Sallallahu Alaihin Wasallama) Ya koyar kuma Ya ce ayi, sai
dai wasu lokutan akwai dan banbanci a tsakanin Sallar Namiji da kuma Mace.
Shi Namiji an
Shar'anta masa cewa idan zai yi Sallah ya yi kiran Sallah ko da a ce a dokar
daji yake ko shi kaɗai ne, hakanan idan
zai yi karatun Sallah ko Mace na kusa da shi, ko Maza ne a kusa da shi an
Shar'anta masa cewa ya Ɗaga muryar sa a inda ake baya yiana karatun Sallah ɗin, wato ya baya yiana
karatun ko da kuwa wanda suke Meter uku ko huɗu za su iya jin Sautin karatun nashi
babu matsala wannan.
Amma ita Mace bahaka ba
ne, matukar akwai Namiji a kusa da inda take yin Sallah, toh bai halatta a ce
ta Ɗaga
sautin muryar ta har na nesa ko na waje suna jin ta ba, ko da wanda suke tare
ya kai Meter 1 ne, sai dai ta yi shi ta yadda na kusa da ita ba ya jin Sautin
karatun ta, ita mace zatayi karatun ne a hankali domin kada ta Ɗaga muryar ta ya dawo
fitana, kuma ba zatayi kiran Sallah ba. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya
ce Ku yi Sallah a inda ake kiran Sallah Maza ke nan, amma mata
bahaka ba ne, idan an ce wannan Masallacin ba su kiran Sallah haka kawai suke
shiga su yi Sallar su, toh bai kamata na bi su ba sai na tafi inda ake kiran
Sallah na yi Sallata a wajen don Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne Ya ce
haka. Amma su mata A'a. Kin ga ke nan akwai banbanci a tsakanin Sallar namiji
da kuma Mace.
Sa'annan a gurin wasu
malaman suka ce baya Halatta Mace ta yi karatun Sallah a baya yiane kawai sai
dai ta yi sa a Ɓoye kamar yadda take yi a Sallar Azahar da La'asar, an
samu saɓani akan hakan suka
ce ai muryar Mace Al'aura ce, waɗanda suka ce za ta iya baya yiana karatun ta,
su kuma suka ce idan ma za ki baya yiana karatun, toh iya kunnen ki ne kaɗai ke jin sautin
muryar naki bawai za ki ɗaga murya sosai irin
yadda Maza yake yi ba, ko a aikin Hajji idan an je gurin Talbiya Mace ba ta buɗe Bakin ta da karfi
irin na Maza, aka ce ta yi kasa da muryar ta. Kuma Mace idan zatayi Sallah abun
da ake so shi ne za ta haɗe Jikin ta ba za ta bubbude
jiki sosai kamar yadda Maza suke yi ba. kin ga ke nan akwai banbanci tsakanin
Sallar namiji da na Mace, Namiji duk waɗannan ba a ce kada ya yi su ba, amma mace
akwai yadda aka ce ta yi, sabida haka akwai banbanci a wasu lokutan.
Ki duba cikin
Littafin (Ibnu Ƙudama a cikin Almugni) Ya ce Ijma'in Malamai sun tafi
akan cewa ba dole ba ne idan Mace za ta yi Sallah sai ta yi kiran Sallah, ko
sai ta yi iƙamar Sallah ba wannan Ijma'i ne na Malamai inji Ibnu Ƙudama, akan cewa ba
dole ba ne idan Mace za ta yi Sallah sai ta yi iƙama, ko ta yi kiran
Sallah ba. Amma Maza an shar'anta musu yin haka, sun din ma idan a Jam'i ne, toh
iƙamar
da Ladan ya yi ko wanin sa ta wadatarwa dukkan Mamu bawai kowa sai ya yi nashi
daban ba.
Amma idan kin yi iƙamar ba tare da kin Ɗaga Muryar ki, sautin
muryar ki ya fita har can-can ba ta yadda ko na Meter 2 ba zai ji ki ba wato
kin yi a hankali, toh wannan Malamai sun ce babu laifi Mace
ta yi iƙamar ta kamar irin su Imamul Shafi'i, da Imam Ahmad sun
ce babu laifi ta yi.
Amma ki sani cewa ba
wajibi ba ne ga Mace a ce sai ta yi sa, idan kuma ta yi toh ba ta yi laifi ba
hakan ya yi wannan shi ne Ra'ayin Sheikh Muhammad Nasiruddeen Albani a cikin
Littafin sa Tamamul Minnah. Sa'annan ki nema darasin mu na Siffatul Salatul
Nabiya yii ki karanta su domin mun kawo misalan sosai tare da hujjoji. Allah
muke roko har kullum Ya kara mana Imani Ameen.
WALLAHU A'ALAMU
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.