𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalama alaikum malam dan Allah ka ba ni shawara duk mijin dana kawowa mahaifina sai ya ce baimaiba amatsayina nabazawara sabida yana so na koma gurin mijina kasancewar Dan'uwansane nikuma wllhi bana sonshi. gashi yanzu ina son na yi auran amma ya ƙi tun mutanan kirki nazowa har amfara samun nabanza gashi Allah ya jarabce ni da matsananciyar sha’awa ya ki barina na yi auran gashi wayanda suke nemana yanzu duk kusan saidai masumun maganar banza ina iya kokarina wajan kare kaina amma ina cutuwa gakuma shedan abun nema yake yazama min lalura wllhi ina iya bakin kokari wajan kare kaina daga yin zina amma ina shiga wani hali sabida nadade dafitowa amma babana ya kasa ganewa dan Allah malam kai ma ka kafadamin wata addu, a dazanyi domin kara kare kaina ko kaban shawara.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam;
Shawarar da zan ba ki shi ne, idan kin san wadda Baban ki yake jin maganar su
kamar manyan sa ko kuma wasu daga cikin abokan sa ko kuma wani malami na
Anguwar ku, toh kina iya zuwa gaban su ki yi musu cikakken bayani yadda za su
fahimce ki su gane me kike nufi. Na tabbatar da cewa indai kin gaya musu kuma
sun yarda da bayanin ki sun fahimta, toh in Sha Allah idan sun same shi sun yi
masa Nasiha da tunatar da shi tare da ba shi shawara akan abun da yake son yi
ba daidai ba ne, toh ba zai ƙi maganar su ba zai barki ki Auri
wadda kike so.
Ko kuma kamar yadda
na faɗa a sama, ki samu a
cikin Malaman Anguwan ku, ko limamin Masallacin da yake zuwa yin Sallah, sai ki
je har gidan sa ki yi masa bayanin komai ki ce don Allah ya yi masa Nasiha ga
halin da kike ciki kin zo gurin sa ne bawai don ki kawo karar sa ba ne sai
domin a fahimtar da ke da shi dukka akan abun Allah da Manzon Allah (Sallallahu
Alaihi Wasallam) Suka koyar, toh in Sha Allah zai kira shi kuma zai yi masa
Nasiha sosai, zai tunatar da shi kuma in Sha Allah indai mai jin nauyin Malamin
ne ko mai jin maganar sa ne, toh zai barki ki Auri abun da kike so. Kada ki ce
ai kunya kike ji ke ba za ki je ba, wannan babu maganar kunya kuma kafin ki
wasu ma sun yi a gaban Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sabida haka
akan ki Saɓawa Allah bayan kin
Auri wannan, toh gara kin samu kowa kin gaya masa indai bukatar ki zai biya ai
fasa yin Auren da wadda ba ki so.
Sai dai kuma idan har
babu waɗannan mutanen na gaya
miki Liman ko malami ko Yan'uwan sa ko abokan sa haka, toh shawara ta karshe
shi ne ki yi hakuri ki koma gidan Mijin ki kamar yadda Mahaifin ki yake so, ki
yi masa biyayya na zaman sa Mahaifin ki wadda babu yadda kika iya yi, yin
biyayya zuwa gare shi sai Allah ya ba ki Ladan wannan, kuma kema za ki samu
wadda za su yi miki biyayya a lokacin da kike neman haka Ido a rufe, kuma yiwa
iyaye biyayya matukar bai saɓawa faɗin Allah da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ba,
toh wajibi ne wannan, rashin yiwa iyaye biyayya matsala ne babba.
Don Haka idan babu
wadda za su yi masa magana ya ji, babu wadda za su yi masa Nasiha ko a
Masallaci ya ji, wato shi bai jin maganar kowa sai abun da zuciyar sa ta gaya
masa, toh sai dai ki yi hakuri ki danne zuciyar ki, ki jure ki yi abun da yake
so ko da kuwa zuciyar ki ba ta son hakan ko da kuwa hakan zai sa ki rasa
rayuwar ki sai ki jure ki yi masa ladabi da biyayya akan bukatar sa.
Yin biyayyar ki gare
shi hakan zai sa Allah Ya kara miki natsuwa da kwanciyar hankalin da ba ki taɓa yin tsammani ba, kuma
ki samu wadda za su yi miki haka nan gaba, rashin yin biyayya gare shi hakan na
iya sa Allah Ya jarrabe ki, ma'ana sai ki Auri wadda kike so kuma yake son ki
amma sai ki dawo kina neman hanyar rabuwa da shi sai ki ga wahalar da kika sha
a gidan tsohon Mijin ki da kika ƙi koma gidan sa yafi
na yanzu.
Bawai ina nufin cewa
Auren dole yana dakyau ba ne ko kaɗan wallahi, domin Annabi Muhammad (Sallallahu
Alaihi Wasalam) bai yarda da ayiwa Mace Auren dole ba, ai mun karanta wannan
Hadisin a cikin Zaduz-Zaujaini, kuma kawo kissar wasu zaurawa da Yan mata da
akayi musu Auren dole ga amsar da Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ba su
ko ga hukuncin da ya yi musu, toh amma yin biyayya ga Iyayen ki wajibi ne
matukar hakan bai saɓawa shari'ar
Musulunci ba.
Don haka indai babu
waɗannan mutanen, toh
kawai ki je ki same shi ki ce Baba kin yarda za ki koma gidan tsohon Mijin ki, sabida
haka a gaya nasa ya turo da Sadaki a daura Auren ku. Sa'annan sai ki nemi
gafarar shi Mahaifin ki akan kin bukatar sa a baya da kika yi sai ki ce ya yafe
miki, sa'annan ya yi miki fatan alkhairy a wannan Auren, sai dai a kira tsohon
Mijin naki a yi komai a rubuce, ta yadda idan kin koma an ci gaba da samun
matsala ba chanji toh a bakin Auren sa, sai ki dawo ki sanar da Mahaifin ki abun
da yake faruwa domin a karɓa miki haƙƙin ki, na raba Auren ko a sasanta ku.
Toh in Sha Allah
indai kin yi haka sai ki ga duk wasu abubuwan da kike gudu zai faru idan kin
koma sai ki ga Allah Ya tsare ki da su dalilin kin sanya Mahaifin ki cikin
farin ciki, daman fushin Allah yana tare da fushin Iyaye, don haka ki yi abun
da ya dace duniyar ma kwana nawa ta rage? Mutuwa ko yanzu ko anjima ne, kin ga
ba wani abu anan.
Toh amma idan shi
Mijin bai da dabi'u masu kyau, halayyen sa ba nagari ba ne, kamar misalin ace
bai yin Sallah, bai da riko da Addini, zamantakewar sa sai a hankali, Addinin
sa sai a hankali, ibadar Allah bai yin su yadda yakamata, ga shi bai sauke Haƙƙoƙin da Allah Ya daura
masa a kanki da Yaran ki, ga shi yana saɓawa Allah, toh gaskiyar magana kada ki koma, domin
ba a yiwa Iyaye biyayya gurin saɓawa Allah, domin duk namjin da bai cika waɗannan abubuwan ba, kuma
ace bai yin su, toh ai bai kamata a ba shi Auren Mace ba idan ma yana Auren mace
ana iya raba wannan Auren. Amma idan ya cika su toh don Allah ki koma gidan
tsohon Mijin ki, indai babu wadda za su yi wa Mahaifin ki Nasiha ya ji, toh ki
bi ra'ayin sa kawai, idan kuma akwai toh ki same su ki sanar da su haka
Shari'ar Musulunci ya ce ki yi domin samun maslaha, kada ki ce ai idan kin yi
haka kamar kin kai karar sa ne wannan ba shi ake kira kai mutum kara ba. Ina
fatan kin gane ko???
Sa'annan kira zuwa ga
Iyaye, gaskiyar magana abun da Iyayen wasu suke yi hakan ya saɓawa shari'ar
Musulunci, ita bazaura ita ce ta ke da damar kawo Mijin da ta ke so sai a
bincika a gani mun yi bayanin nan a darasin mu na Zaduz-Zaujaini, sabida haka
idan an bincika ya cika abun da ake so, wadda za a Aura da shi duk sun yi
Istihara sun ji zaɓin Allah akan
alkhairi ne kuma bincike ya nuna bai da matsala shike nan sai a ba shi Auren ta,
idan bai cika ba ko kuma an yi bincike ta yi Istihara an ga akwai matsala a tare
da shi ba alkhairi ba ne, toh sai a lallaba ta, a ba ta shawara ta rabu da shi
sai ta sake kawo wani daban.
Ita Bazaura Baba ta
fi ka sanin yaya halin tsohon Mijin ta yake, duk Macen da ta ce ba za ta koma
gidan tsohon Mijin ta ba, wallahi a matsayin ki na Uwa a matsayin ka Uba, toh
bai kamata ace ka tilasta ta ka ce dole sai ta koma gidan tsohon Mijin ta ba, domin
bawai kai ne za ka zauna da mijin ba, ita da ta san halin Mijin ta da dabi'un
sa har ta ce ma gaskiya a'a ba za ta ta koma ba, toh yakamata a bar ta ta zaɓi abun da ta ke so, mace
ai idan ta rabu da mijin ta wallahi indai daɗi ta ke ji a gidan sa, toh ita ne ma za ta bi
duk hanyar da ta sani domin mijin ya dawo da ita, amma idan ta ce ba za ta koma
ba, toh ba karamin wahala take sha ba, sabida haka wallahi cutarwa ce sosai mace
ta ce ba za ta koma ba, kai kuma ka ce dole sai ta koma wannan zalunci ne.
Kamar yadda na faɗa a sama ai idan
mijin mutumin kirki ne, toh wallahi ba sai ka ce Mata gidan waye za ki koma ba
ita da kanta za ta nemi ta koma gidan sa ko ba ka son hakan sabida shi mutumin
kirki ne da dabi'u nagari, amma idan mace ta ce ba za ta koma ba gidan tsohon
Mijin ta ba, toh Iyaye bai kamata ku tilasta musu ku ce dole Sai ta koma gidan
sa ba. Ku rika yiwa Ɗiyar ku uzuri domin wani abun ba su son sanar da ku ne
domin suna jin nauyin ku da kunyar ku, kuma shedar da matar
mutum za ta bayar akan mijin ta, wallahi ko Mahaifiyar mutum ba ta isa ta bayar
da irin wannan shedar ba, don haka yakamata ku rika bincike kuna yin Shari'ar
adalci ga Yaran ku domin sai Allah Ya tambaye ku akan wannan, sabida haka
kuskure ne mace ta zo da matsalar gidan Mijin ta kuma hakan na faru da ita, amma
kayi banza da ita ka ka ce wai ki yi hakuri ki koma gidan mijin ki, wallahi sai
Allah Ya tambaye ku akan wannan.
Ko Budurwa ce ai
Addinin Musulunci bai yarda kayi Mata Auren bole ba, ballatana ace Bazaura
wadda ta mallaki hankalin ta kuma gidan tsohon Mijin ta ake so ta koma ta ce
a'a. Mu ji tsoron Allah Iyaye kada don biyan bukatar ku ya kai ku ga saɓawa Allah gurin cutar
da rayuwar Yaran ku da jefa su cikin zinace-zinace wallahi sai kun Yi bayani a
gaban Allah. Allah Ya shirya.
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.