𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum mlm
ina yini Dftn kn lfy Allah yasa hk amin
Mlm ina so a taimaka mim da addua wlh mlm ina yawan yin mugayen mafarkai, sannan na yi wani mafarki daya tadamin hankali sosai nakasa samun natsuwa kwata kwata shi ne kamar haka naga kawanta datarasu taxo gidan mahaifiyata nikuma sai muka hadu da ita a kofar gidan lokacin za ta shiga sai na yi murnar ganinta a yana yi mai kyau saina ce daman kinanan sai ta ce eh yanzu ma gurin mahaifiyarmu na zo sai na ce mushigato amma mekika kawomim sai ta ce babu saidai naji an ce kema kinkusa zuwa garinmu saina ce a a ni ba zan zo garinku ba sai ta ce ai babu komai nima karama ai naje shi ne shiga gurin mahaifiyartamu, shi ne fa tunda na farka nakasa samun natsuwa mlm, sainajika nagode Allah yasaka da alkhairi
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumussalam
warahmatullahi wabarakatuh.
Mafarkin da kika yi
cewa ga mamaci (kanwarki) tazo gidan ku ta ce kin kusa zuwa garinsu, yana sanya
tsoro amma ba ya nufin mutuwar ki ta kusa ba. Wannan mafarki yana iya zuwa ne
saboda tsananin tunani, ko damuwa, ko kuma saboda kin dade kina kewar
marigayiyar a zuciyar ki ko kuma jan hankali zuwa ga tuba da tsoron Allah.
Abin da za ki riƙe don samun natsuwa
yanzu shi ne; Kar ki sa a ranki cewa mutuwa za ki yi, domin rayuwa tana hannun
Allah ne Shi kaɗai. Ki yawaita
istigifari da neman tsarin Allah daga shaiɗan da mugayen mafarki. Kafin ki kwanta barci,
ki rika karanta Ayatul Kursiyyi da suratul Ikhlas, Falak, da Nas, sannan ki
tofa a jikinki. Idan kin tashi da mummunan mafarki, ki tofa a gefen hagu sau
uku, ki nemi tsarin Allah daga Shaiɗan, sannan ki juya gefe ɗaya. Ki yi alwala
kafin ki kwanta kuma ki kwanta a gefen dama. Sannan kiyi Sadaka, Sadaka tana
kore bala'i kuma tana kawo kwanciyar hankali a zuciya. Ki Tuba da yawan
Istigifari da yawan salati ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Kada ki damu da
wannan mafarki, domin ba zai cutar da ke ba, kuma ba yana nufin mutuwa ko wata
mummunan abu. Mafarkin yana nuna tsoron rashin kanwarki da kike so, da kuma
tunani mai tsanani a zuciyarki game da marigayiyar kanwar da ta rasu.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.