TAMBAYA❓
Assalamu alaikum Dan
Allah a koya mana addu’ar ƙarfafa imani da ƙarin tsoron Allah da
kusantar Allah
ADDU'O'IN ƘARFAFA IMANI DA KARIN TSORON ALLAH
AMSA:‼️
Wa'alaikumun salamu
warahamatullah
Gaskiya na ji dadin
Wannan tambayan domin yakamata yan'uwa musani cewa mafi girman ni'ima bayan
shiriya ita ce ƙarfafan imani da taƙawa. Imani shi ne
hasken zuciya, kuma duk lokacin da imani ya ƙaru, kusancin bawa ga
Allah yana ƙaruwa, zuciya tana samun nutsuwa, kuma biyaya yia tana
zama mai sauƙi. Saboda haka, Manzon Allah (SAW)
duk da cewa shi ne mafificin halitta, ya kasance yana yawaita roƙon Allah Ya tabbatar
da zuciyarsa akan addini. Wannan yana nuna mana cewa kowane Musulmi yana buƙatar yawaita addu'ar
neman ƙarfafa imani, tsoron Allah da dawwama a kan shiriya.
Ga wasu kadan daga
cikin addu'o'in da suka zo a Al-Ƙur'ani da Sunnah waɗanda ake roƙon Allah dasu domin ƙarfafa imani, ƙara tsoronSa da
kusantarSa:
اللَّهُمَّ يَا مُقَلِّبَ
الْقُلُوبِ ثَبِّتْ قَلْبِي عَلَى دِينِكَ
Allahumma yā Muƙallibal-ƙulūb, thabbit ƙalbī 'alā dīnik.
Ya Allah, Mai jujjuya
zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan addininka.
> اللَّهُمَّ إِنِّي
أَسْأَلُكَ الْهُدَى وَالتُّقَى وَالْعَفَافَ وَالْغِنَى
Allahumma innī
as'alukal-hudā wat-tuƙā wal-'afāfa wal-ghinā.
Ya Allah, ina roƙonKa shiriya, taƙawa, kame kai da
wadatar zuci.
> رَبَّنَا لَا تُزِغْ
قُلُوبَنَا بَعْدَ إِذْ هَدَيْتَنَا وَهَبْ لَنَا مِن لَّدُنكَ رَحْمَةً ۚ إِنَّكَ
أَنتَ الْوَهَّابُ
Rabbanā lā tuzigh ƙulūbanā ba'da idh
hadaytanā wa hab lanā min ladunka raḥmah, innaka
Antal-Wahhāb.
Ya Ubangijinmu, kada
Ka karkatar da zukatanmu bayan Ka shiryar damu, Ka bamu rahama daga gareKa.
Lalle Kai ne Mai yawan baiwa. Wadannan addu'o'in yakamata mu yawaita shi acikin
addu'o'inmu da mukeyi na yau da kullun domin karfafa imani da karin tsoron
Allah,
Ya Allah, Ka ƙara mana imani mai ƙarfi, Ka cika
zukatanmu da tsoronKa, Ka sanya mu cikin bayinKa na gari, Ka bamu sonKa da son
duk abinda yake kusantar damu zuwa gareKa, Ka tabbatar damu a kan gaskiya har ƙarshen rayuwarmu, Kasa
ƙarshen
maganarmu ya zama Lā ilāha illallāh, Muhammadur Rasūlullāh (SAW)🤲
Wallahu ta'ala aalam
✍️MT
ABDULLAHI
Zauren Fatawoyi Bisa
Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.