𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum. Ina matsayin maigidan da a kullum ba ya fita zuwa sallah a masallaci sai an tayar da iƙamah?
HUKUNCIN WANDA BA YA
FITA ZUWA SALLAH A MASALLACI SAI AN TAYAR DA IƘAMAH
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam
Wa Rahmatul Laah.
Hikimar kiran sallah
ita ce a sanar da musulmin da suke nesa cewa lokacin sallah ya yi, don haka sai
kowannensu ya tashi ya yi shirin zuwa masallaci, domin bayar da wannan
farillar. Shiyasa a cikin kiran Ladan yake faɗin: Haya yia Alas Salaah da Haya yia
Alal Falaah sau bibbiyu.
Amma ita iƙamah ana yin ta ne
domin a sanar da waɗanda suka amsa waccan
kirar ta farko har suka tabbata a cikin masallacin cewa, yanzu za a fara
sallah. Shiyasa a cikinta ladan yake maimaita faɗin: Ƙad Ƙaamatis Salaah har
sau biyu a cikinta.
Don haka, da zaran
musulmi ya ji muryar ladan mai kiran sallah sai ya daina komai, ya shiga shirin
amsa wa wannan kiran. Ya tashi ya kintsa ya taka cikin natsuwa zuwa masallaci.
Ya shiga, ya samu wuri a sahun farko, ya tsaya ya yi gaisuwar masallaci da
sauran nafilolin da aka so a Sunnah, sannan ya zauna ya jira Iƙamah.
Masu makara waɗanda ake tayar da iƙama alhali ba su a
cikin masallaci suna da kaso a cikin maganar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa
Alihi Wa Sallam) ya yi cewa:
« وَالَّذِى
نَفْسِى بِيَدِهِ لَقَدْ هَمَمْتُ أَنْ آمُرَ بِحَطَبٍ يُحْتَطَبُ ، ثُمَّ آمُرَ
بِالصَّلاَةِ فَيُؤَذَّنَ لَهَا ، ثُمَّ آمُرَ رَجُلاً فَيَؤُمَّ النَّاسَ ، ثُمَّ
أُخَالِفَ إِلَى رِجَالٍ فَأُحَرِّقَ عَلَيْهِمْ بُيُوتَهُمْ ، وَالَّذِى نَفْسِى
بِيَدِهِ لَوْ يَعْلَمُ أَحَدُكُمْ أَنَّهُ يَجِدُ عَرْقًا سَمِينًا أَوْ
مَرْمَاتَيْنِ حَسَنَتَيْنِ لَشَهِدَ الْعِشَاءَ ».
Na rantse da Wanda
raina yake a hanunsa, haƙiƙa! Na yi aniyar yin umurni da a tattaro kirare, sannnan
in yi umurni da a kira sallah, sai kuma in umurci wani mutum ya yi limancin
sallar, sai kuma in koma ga mutanen (da ba su zo masallacin ba), in kona
gidajensu a kansu. Na rantse da wanda raina ke ga hanunsa, in da ɗayansu ya san zai
samu ƙashi mai tsoka ko kofaton tunkiya masu kyau guda biyu da
ya halarci sallar isha’i. (Sahih Al-Bukhaariy: 7224).
Idan da ya zartar da
wannan aniyar to da kuwa masu makara sun shiga cikin waɗanda zai samu a cikin
gidajensu, kuma ya ƙoƙƙona su.
Maganin wannan shi ne
mutum ya riƙa gaggawan yin shirin zuwa masallaci da zaran an fara
kiran sallah, kafin sheɗan ya dawo ya fara
nauyayar da shi da waswasi, kamar yadda Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya
riwaito daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) cewa:
« إِنَّ
الشَّيْطَانَ إِذَا سَمِعَ النِّدَاءَ بِالصَّلاَةِ أَحَالَ لَهُ ضُرَاطٌ حَتَّى
لاَ يَسْمَعَ صَوْتَهُ فَإِذَا سَكَتَ رَجَعَ فَوَسْوَسَ فَإِذَا سَمِعَ
الإِقَامَةَ ذَهَبَ حَتَّى لاَ يَسْمَعَ صَوْتَهُ فَإِذَا سَكَتَ رَجَعَ
فَوَسْوَسَ »
Idan sheɗan ya ji kiran sallah
sai ya juya yana tusa har sai ya kai inda ba ya jin kiran sallar. Idan ladan ya
yi shiru sai ya juyo ya fara sanya waswasi. Idan kuma ya ji iƙama sai ya sake
tafiya har sai ya kai inda ba ya jin muryar, idan kuma ya yi shiru sai ya komo
ya shiga sanya waswasi. (Sahih Al-Bukhaariy: 608; Sahih Muslim: 882).
A taƙaice dai: Abin da ya
kamaci duk mai hankali shi ne, ya yi wa kansa faɗa, haka ma makusanta - kamar iyalinsa
- su taimaka da tuna masa har ya riƙa halartan masallaci
a kan lokaci.
Su ma ladan da liman
su taimaka ta hanyar kashe ƙarar amsa-kuwwa (loudspeakers) a
lokacin tayar da iƙamah da karatun sallah, tun da dai an shar’anta
su domin waɗanda su ke cikin
masallaci ne. Su ma suna taimakawa wurin zuwa masallaci a makare. Domin galibi
sai sun ji Iƙamar ce sannan suke tashi, maimakon daga sun ji kiran
sallah.
Allaah ya ƙara mana fahimta.
Wal Laahu A’lam.
Sheikh Muhammad
Abdullaah Assalafiy
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.