Ticker

6/recent/ticker-posts

Falala Kiran Sallah Da Bin Mai Kiran Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Malam Khamis, da fatan kana cikin ƙoshin lafiya. Malam, muna ƙara godiya, Allah ya saka ma da mafificin alheri, ya biya ma dukkanin buƙatunka. Tambayata ita ce: Ya aka yi aka samu kiran salla? Mene ne falalar kiran salla da bin mai kiran salla? Kuma idan ana kiran salla a lokaci guda daga mabanbanta masallatai, sai na fara bin masallacin da na fara jin kiran sallarsa, ina farawa kuma sai na ji wani masallacin shi ma an fara kiran salla, ya zan yi ke nan? Zan yi shiru ne ko kowane zan bi? Kuma ya hallatta ana kiran salla in yi salla ko sai an gama kiran salla sannan zan yi kabbara? Kuma wace irin addu'a ingantacciya mutum zai iya yi bayan kiran salla? Allah ya saka da alheri, ya ƙara ma Malam lafiya da ilimi mai amfani.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Daga Ibnu Umar Allah ya yarda da su ya ce: Musulmai sun kasance a lokacin da suka iso Madina, suna taruwa su kintaci lokacin Sallah ba tare da an yi kira ta ba. Sai suka tattauna wata rana a kan haka, sai wasunsu suka ce: Ku riki kararrawa kamar kararrawar Nasara. Wasu kuma suka ce: A'a, sai dai kaho kamar kahon Yahudawa. Sai Umar ya ce: Shin ba za ku tura wani mutum ya yi kira Sallah ba? Sai Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: «Ya Bilai, tashi ka kira sallah» [4]. [4] Bukhari ne ya ruwaito shi, a lamba ta (604), da Muslim, a lamba ta (377).

Akwai ruwayar data zo cikin sunan na Abi Dauda 420, wadda ta nuna cewa Abdullahi Bn Zaid ibn Abdi Rabbihi wata rana yana tsakanin bacci da falke sai wani yazo masa ya koya masa kiran sallah, da gari ya waye yazo wajen Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya baya yia masa, Ashe Umar bin khaddab ya dade da yin mafarki kiran sallah kusan kwana ashirin amma bai gaya wa Manzon Allah (Sallallahu alaihi Wasallam) ba sai ranar da Abdullahi ya gaya wa Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) bai ce umar me yasa baka gaya mun tun tunni ba. sai ya ce ya kai bilal tashi kaje ka kira sallah. Wannan shi ne tarihin samuwar kiran sallah.

Imam Ibn Kudamah Al-Makdisi ya ce: "Al'umma ta yi ijma'i akan cewa an shar'anta kiran sallah domin salloli biyar". [5] al-Mugni: (1/ 293).

Kiran sallah yana da babban matsayi da falala mai girma a Musulunci, Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: "Da mutane sun san babban alherin da ke cikin kiran sallah da iƙamah, da sun yi kuri'a a kan wanda zai yi shi saboda girman ladansa. (Bukhari da Muslim suka ruwaito).

A wani hadisi Daga Abi-Hurairah Ya ce: Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Da Mutane Sun San Abinda Ke Cikin Kiran Sallah da Sahun Farko, Idan Akace Bazaka Samesu ba Sai Anyi Ƙuri'a da Sun Yarda Ayi Ƙuri'ar (Bukhari da Muslim).

Allah na gafarta wa mai kiran sallah gwargwadon tsawon muryarsa. Ba wani aljani ko wani mutum ko wani dabba ko wani abu da zai ji muryar mai kiran sallah sai ya yi shaida gareshi ranar Alƙiyama. Duk wanda ya yi sallah tare da jama'a a bayan kiran sallah da iƙamah, mai kiran yana samun rabon ladan sallar dukkan su ba tare da an rage na kowa ba. A ranar tashin kiyama, masu kiran sallah za su fi kowa tsawon wuya (wato daraja da shugabanci zuwa rahama), domin su ne ke kira zuwa ga bautar Allah.

Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: «Idan mai kiran sallah ya ce: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, sai ɗayanku ya ce: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, sannan ya ce: ASH'HADU ALLA ILAHA ILLALLAHU, kuma shima ya ce: ASH'HADU ALLA ILAHA ILLALLAHU, sannan ya ce: ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH, kuma shima ya ce: ASH'HADU ANNA MUHAMMADAN RASULULLAH, sannan ya ce: HAYA YIA ALAS SALLAH, sai ya ce: LA HAULA WALA ƘUWWATA ILLA BILLAH, sannan kuma ya ce: HAYA YIA ALAL FALAH, sai ya ce: LA HAULA WALA ƘUWWATA ILLA BILLAH, sannan ya ce: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, kuma shima ya ce: ALLAHU AKBAR ALLAHU AKBAR, sannan ya ce: LA'ILAHA ILLALLAH, kuma shima ya ce: LA'ILAHA ILLA ALLAH, daga zuciyarsa, zai shiga Aljanna» [37]. [36] Bukhari ne ya ruwaito shi a lamba ta (611), da Muslim a lamba ta (383). [37] Muslim ne ya ruwaito, a lamaba ta (385).

Kuma idan mai kiran sallah ya ce a sallar Asuba: "ASSALATU KHAIRUN MINAN NAUM, " to shi ma mai sauraro zai faɗi irinsa; saboda faɗin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) "Idan kun ji mai kiran sallah, to ku faɗi irin abin da yake faɗi. Sai kuma ku yi mini salati, domin shi wanda ya yi mini salati guda Allah zai yi masa salati goma. Sannan sai ku roƙa mini waseelah a wurin Allaah, domin ita wani matsayi ne a cikin Aljannah, ba ta dacewa sai ga wani bawa guda daga cikin bayin Allah, kuma ina fatar in zama ni ne wannan bawan. Duk wanda ya roƙa mini waseeilah to lallai ceto ya tabbata gare shi" (Sahih Muslim: 875).

Bin kiran sallah, sunnah ce mustahabbiya ga kowane musulmi babba ko yaro, namiji ko mace, mai tsarki ko mara tsarki, kamar mai janaba, ko mai haila, ko mai nifasi. Har mai bayar da darasi (wa'azi) ko mai zikiri ko mai karatun Alƙur’ani ma, duk an so su dakatar da abin da suke yi a lokacin da aka fara kiran sallah. Sai a bayan sun gama maimaitawa da yin addu’o’in da suka biyo bayan hakan, sannan sai su cigaba.

Bayan kammala kiran sallah, akwai matakai da addu'o'i na musamman da Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya koyar damu, mu karanta domin samun lada da cetonsa a ranar kiyama.

أَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ، وَأَنَّ مُحَمَّدَاً عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ، رَضِيتُ بِاللهِ رَبَّاً، وَبِمُحَمَّدٍ رَسُولَاً، وَبِالْإِسْلَامِ دِينًا

"Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kaɗai, ba shi da abokin taraya yia. Kuma lalle Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Na yarda Allah shi ne Ubangijina, kuma Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) Manzo ne, kuma Musulunci shi ne addinina."

Bayan haka, sai mutum ya yi salati ga Annabi Muhammadu (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi):

اَللّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اَللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ، وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارِكْتَ عَلَى إبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ

Ya Allah! Ka yi rahama (da yabo) ga Muhammad da kuma alherin gidan Muhammad, Kamar yadda Ka yi rahama ga Ibrahim da kuma alherin gidan Ibrahim, Lalle Kai Abin Yabo ne, Mai Girma. Ya Allah! Ka albarkaci Muhammad da kuma alherin gidan Muhammad, Kamar yadda Ka albarkaci Ibrahim da kuma alherin gidan Ibrahim, Lalle Kai Abin Yabo ne, Mai Girma.

Sai addu'a Neman Wasilah:

اللَّهُمَّ رَبَّ هَذِهِ الدَّعْوَةِ التَّامَّةِ، وَالصَّلَاةِ الْقَائِمَةِ، آتِ مُحَمَّدَاً الْوَسِيلَةَ وَالْفَضِيلَةَ، وَابْعَثْهُ مَقَامَاً مَحْمُودَاً الَّذِي وَعَدْتَهُ

"Ya Allah! Ubangijin wannan kira cikakke (na kadaita Ka), da sallah da za a tsayar da ita. Ka ba wa Muhammadu (Sallallahu Alaihi Wasallam) Wasila (matsayi na musamman a Aljanna) da daukaka, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo (na yin ceto) wanda Ka yi masa alkawarinsa.

Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: Duk wanda ya karanta wannan addu'ar cetonsa ya tabbata a gare shi ranar kiyama.

Bayan ka kammala wadannan zikirai, za ka iya rokon Allah duk abin da kake bukata na alherin duniya da lahira. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya baya yiana cewa addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama ba a maida ita (ana karbarta cikin sauri).

Idan ana Kiran sallah a lokaci guda daga mabanbantan masallatai, ba sai ka dinga sauyawa daga wannan zuwa wancan ba. Ka amsa kiran farko da ka fara bi har ya gama. Idan masallacin da ya fara kiran sallar shi ne mafi kusa da gidanka, to shi ne ya fi cancanta ka bi. Idan masallacin farko ya gama, kuma na biyun yana kiran sallah har yanzu, za ka iya amsa sauran kiran sallar tasa idan kana so. Babu wajibci akan duka. Amsa kiran sallah sunnah ce mai ƙarfi (ko mustahabbi), saboda haka amsa kiran sallah guda ɗaya ya wadatar da kai.

Ba a yin sallah idan aka fara kiran sallah sai dai a saurari kiran sallah a kuma amsa masa. Saboda haka Kada ka shagala da wani abu da zai sa ka kasa amsa kiran sallah koda karatun Alkur'ani ne. Kar ka kabbarta sallah a dai-dai lokacin da kiran sallah ke gudana har sai an kammala. Amma idan akwai dalili, kamar kana tsoron lokacin zai ƙure ko za ka rasa jam'i, ya halatta ka fara sallah tun ana kiran sallah. Ba haramun ba ne, sai dai bin ladan kiran sallah ya fi.

Allah Ya karɓi ibadunki, Ya ƙara mana ilimi mai amfani da aiki nagari.🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam  

Post a Comment

0 Comments