Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
‘Ya’yan Kishiya
‘Ya’yan kishiya su ne ɗiyan miji, waɗanda watar ta haifa a cikin gidan, wato ɗiyan kishiyoyinta. A zamantakewa ‘ya’yan kishiya sukan taka muhimmiyar rawa kan harkar kishi a cikin zamantakewar aure a gidan miji.
1. Ɗan kishiya, riƙon mai haƙuri
2. Babu dole ga goyon ɗan kishiya
3. Wayayyan hauka, goyon ɗan kishiya ga naki
4. Ban gane ba, an daki ɗan kishiya
5. Isa da mallaka, biyan bashi da
ɗan kishiya.
Agola
Agola yaro ne wanda aka auro
mahaifiyarsa, ta zo tare da shi gidan sabon miji. Agola wani yaro ne mai
shekaru ƙanana,
wani lokaci har da mai watanni ana zuwa da su agolanci a gidan miji, shi dai
agola mahaifiyarsa ce ta auri miji wanda ya kasance shi wannan mijin wanda ta
aura ba ubansa ba ne, amma ta zo da shi ne a gidan. Akwai jerin karin magana da
suka taskace yanayin zaman agola a gidan da mahaifiyarsa take aure a al’adar Bahaushe. Misalansu
sun haɗa da:
1. Agola ka fi ɗan masu gida.
2. Agola mai wuyar ban nama,
kadan aka ba shi tsoka, sai ya cinye da sauri ya ce ba a ba shi ba.
3. Agola mai wuyar ban nama, sai
dai a ba shi ƙashi.
4. Dole a bai wa ɗan mata hura.
1. Agola ka fi ɗan masu gida
Wannan kirarin yana nuna irin
yadda agola yakan samu karɓuwa
da tagomashi ga maigida, matuƙar dai maigidan yana tsananin son
mahaifiyarsa. Irin wannan agola ne mutanen gida suke yi wa karari da cewa ‘Agola ka fi ɗan masu gida’, wani lokaci
akan cika karin maganar da cewa saboda uwata aka so.
2. Agola mai wuyan ban nama sai
dai a ba shi ƙashi
Ita ma dai wannan karin maganar
irin wadda ta gabace ta ce, tana muna cewa a yi wa agola alheri ko kyauta da
abin da ba ya saurin ɓoyuwa
don gudun ƙulla
makircin cewa ana nuna masu wariya.
Ƙunshiyar kare-karen maganan guda biyu,
idan aka yi warwarar saƙonsu na zahiri, za a ga cewa idan aka ba yaro tsokar nama yana
iya saurin cinyewa ya yi kamar ba a ba shi ba, amma idan aka ba shi ƙashi,
sai ya ɗauki lokaci
mai tsawo yana gurgura.
3. Dole ko tilas a bai wa ɗan mata hura
Hura, abin sha ce wanda ake yi da
gero (CNHN,2005:203), kuma abin sha ce sananniya a ƙasar Hausa. Wannan karin
magana tana nuna al’adar
nan ta Hausawa ta ciyar da ɗan
matarsa (agolansa) da ma ɗaukar
wasu ɗawainiyoyinsa.
4. Dole a ce wa mijin iya baba
Wannan karin maganar tana nuna
yadda dangantaka take kasancewa tsakanin mijin uwa da ɗan mata, watau kamar dai yadda ga al’ada mijin
uwa yake zama matsayin uba ga agola. To shi ma agola al’adar ta tilasta masa ɗaukar mijin uwa a matsayin
uba, domin cuɗanyarsu
da mu’amalarsu ta kyautatawa a zamantakewa.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.