Ticker

6/recent/ticker-posts

Sa-Daka a Madubin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Sa-ɗaka baiwa ce wadda aka riƙe ta a matsayin matar aure. Bayan wannan suna na ‘sa-ɗaka’, Hausawa sukan kira ta da sunaye kamar ‘ƙwarƙwara’ ko ‘kuyanga.’ Akwai fahimtar da take nuna cewa, akan kira ta da sa-ɗaka ne kasancewar wanda ya mallaki ƙwarƙwara, yana iya saka ta a ɗaka a matsayin mata kai tsaye ba tare da bin dogin matakan auren ‘ya mai ‘yanci ba.

A al’adar Hausawa a da can, gidan sarki ko wani attajiri ana sawo wasu mata da ake cewa baiwa, wadda wani lokaci ana ciwo su ne a fagen yaƙi, sai a zo a sayar da su. Ita baiwa ko sa-ɗaka ana killace ta ne kamar matar aure a cikin gida, kuma ba ta da ikon zuwa wani wuri, kawai ana ajiye ta ne domin hidimar gida da maigida da iyalansa. Kuma duk abin da maigida ke yi da matansa ita ma za a iya yi da ita, amma ba a rabon kwana da ita, tana da damar kowane irin lokaci ne ubangidanta ya buƙaceta da ta zo sai ta zo. Tana haihuwa, kuma ana gudanar da komai na gidan tare da ita, amma ba ta kai darajar matan gidan ba. Kuma ba a aje sa-ɗaka sai da matan aure a al’adar Hausawa.

1. Faɗi ke matar aure, ni sa-ɗaka in na faɗi gida nike kwana

2. Sa-ɗaka ba mata ba, sai da iyali

1. Faɗi ke matar aure, ni saɗaka in na faɗi gida nika kwana

Wannan karin magana tana nuna cewa saɗaka ba ta faɗa a ji kamar yadda matar aure take, saboda haka dole ne ta yi hattara matuƙar tana son zamanta ya ɗore a gidan aure.

2. Sa-ɗaka ba mata ba sai da iyali

Wannan karin maganar tana nuna cewa duk da yake sa-ɗaka an keɓance ta daga sauran bayi, har yanzu al’ada na kallonta a matsayin baiwa ba matar aure ba, har sai ta haihu ta tara iyali, sannan za a iya bambanta ta da sauran bayi, ta kama hanyar shiga sahun matan aure ta fuskar daraja, musamman ma dai idan ‘ya’ya maza ne ta fi haifa. A al’adar Hausawa wadda aka gada kaka da kakanni, wannan hukunci ne wanda suke ganin cewa haka ya dace da ita sa-ɗaka.

Daga wannan bayani, a fahimci cewa a al’adar Hausawa, Sa-ɗaka ba mata ba ce mai wata daraja ko matsayi a gidan aure ba, matuƙar ba ta da ‘ya’ya. Ana amfani da wannan karin magana a nuna cewa wani bai isa ba har sai ya mallaki abin da zai yi gogayya da abokan tarayyarsa ko mu’amalar sa ko jayayyarsa.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments