Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Maraya (namiji) ko marainiya (mace) ko marayu (jam’i) yara ne da suka rasa iyayensu, ko suka rasa mahaifi. Maraya wani yaro ne da ya rasa mahaifiyarsa ko mahaifinsa, wanda idan aka auro wata matar, sai ubansa ya hannunta mata shi a matsayin amana, saboda rasa mahaifiyarsa da ya yi, sai ta zame masa uwar riƙo. A ƙasa an kawo misalan wasu karin magana da suka shafi maraya:
1. A ƙi maraya da rigar buzu, a
gan shi da ta ƙarfe.
2. Babu maraya sai rago
3. Maraya ba ya gudun mutuwar
uwar kowa.
4. Sauran tuwo na masu uwa ne,
maraya ka dangana.
Ga tsokaci game da wasu daga
cikin waɗannan
kare-karen magana:
1. Maraya ba ya gudun mutuwar
uwar kowa
Wannan karin maganar tana nuna
cewa tun da dai shi maraya ya riga ya rasa mahaifiyarsa wadda ita ce mafi
tausaya masa da kula da shi bisa bayan ƙasa, don haka, ba ya gudun mutuwar uwar
kowa a halin yanzu, musamman idan ya samu kansa a gidan da ake ƙuntata
masa. Haka kuma, abin yake ga kusan duk wani wanda ya rasa gata.
2. Sauran tuwo na masu uwa ne,
maraya (sai) ka dangana
Wannan karin maganar tana nuna
irin yadda ake ba maraya rashin cikakkiyar kulawa da kuma nuna masa wariya da
bambanci tsakaninsa da masu iyaye a wasu gidaje. Watau, saƙon
karin maganar shi ne idan dai har shi maraya ya samu wata ‘yar kulawa kaɗan, to sauran wasu abubuwa
ba zai same su ba, ko da kuwa abin da ya samu bai ishe shi ba, dole ya haƙura.
3. A ƙi maraya da rigar buzu, a
gan shi da ta ƙarfe
Buzu na nufin fatar rago ko
tunkiya wadda aka gyara ake zama ko sallah a kai (CNHN, 2005 sh. 58). Ana kuma
bayyana ƙarfe
da cewa, wani abu ne dangin ma’adanai
da ake tonowa daga ƙasa, akan narka shi don yin makamai ko abubuwan hawa ko kayan
noma (CNHN, 2006 sh. 277). Wannan karin maganar tana nuna cewa idan aka nuna wa
mutum ƙiyayya
tare da yunƙurin
hana shi samun wani abu mai muhimmanci, sanadiyyar wannan ƙiyayyar
sai ya samu abin da ya fi wannan abin muhimmanci da daraja.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.