Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Aka Yi Amfani Da MyBonus2u Domin Damfara a Kan Intanet

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

An fara shi a shekarar: 2020

An rufe shi a shekarar: 2021

Kafar intanet ɗin da suka yi amfani da ita: www.mybonus2u.com

MyBonus2u ya fito da tsarin kasuwancin kan intanet a shekarar 2020. An bayyana shi a matsayin kasuwancin da yake ba da dama ga mutane su saka hannun jari. Bayan sun saka hannun jari, su kuma kamfanin MyBonus2u za su riƙa yi musu talla tare da sayar musu da kayayyakin zuwa ga kwastomomi masu tarin yawa a kan intanet. Sun bayyana cewa suna da haɗin guiwa da manyan kasuwannin kan intanet na duniya irin su Amazon da Alibaba da eBay da Jumia.

Waɗannan kafafen kan intanet suna daga cikin manyan kasuwannin intanet na duniya. Ana iya duba su kai-tsaye ta hanyar shiga liƙau ɗinsu kamar haka:

a. Amazon (https://www.amazon.com)

b. Alibaba (https://www.alibaba.com)

c. eBay (https://www.ebay.com)

d. Jumia (https://www.jumia.com)

Yadda ake gudanar da harƙallar kuwa shi ne, da farko mutum zai yi rajista a kafarsu, sannan ya sanya hannun jari. Ba a ƙayyade adadin hannun jarin da mutum zai saka ba. A kullum za a ba shi jerin kayayyaki waɗanda zai saka musu ƙima (rating). Wannan jingar ba ta wuce ‘yan mintuna kaɗan. Za a iya lura da cewa, wannan ma salon yaudara ne da ya taimaka wajen ɗauke hankalin mutane. Akwai mutanen da suke da fahimtar cewa, lallai wannan jinga da ake bayarwa ta kai matsayin aikin da ta cancanci kamfanin ya biya kuɗaɗen da ya yi alƙawarin biya dominta.

A kowace rana, mutum zai samu ribar kashi uku (3%) na hannun jarin da ya saka. Mutum zai iya cire kuɗaɗen da ya saka da kuma ribarsa a duk lokacin da ya ga dama. Hakan ya sa abin ya bayyana tamkar gaskiya ga mutane da yawa inda suka ruɗu da wannan garaɓasar ribar da ake samu a kullum. Abin da ba su sani ba shi ne, kuɗaɗen da sababbin mambobi suke sakawa yayin da suka yi rajista, da su ne ake biyan tsofaffin mambobi.

Ganin wannan garaɓasa ta sa mutane ba sa ko cire ribar da suka samu, saboda idan suka bar ta, uwar kuɗinsu za ta ƙara yawa, wanda hakan yana nufin ƙaruwar ribar da za su samu a kullum. Kamar yadda A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga watan Nuwamba 2024) ya bayyana “wasu ma a kullum idan suka samu riba a wurin sana’arsu, sukan saka kuɗin ne a MyBonus2u domin ribar da suke samu ta ƙara yawa.”

A gefe ɗaya kuwa, akwai tsarin gayyata. Za a bai wa mutum wani kamasho ga duk wani mutumin da ya gayyato. Wannan tsarin ma ya ƙara yaɗa harƙallar a tsakanin mutane. Aboki zai sanar da abokinsa cewa ai shi ma ya samu riba. Yayin da wanda ake gayyatar ya ga banza gasassa, shi ma sai ya shiga da rawar jiki. A haka suka tara kwastomomi masu tarin yawa.

Za a iya lura da cewa, manyan abubuwa guda biyu ne suka sa wannan kasuwancin damfara ya yaɗu, sannan ya samu karɓuwa sosai a tsakanin Hausawa. Dabarun kuwa su ne:

1. Tsarin da ya bayar da damar cire kuɗi a duk lokacin da ake so. Wannan tsari ya gina yarda a zukatan masu saka hannun jari.

2. Tsarin bayar da kamasho a sakamakon gayyata ya ƙara dasa yarda ga waɗanda za a gayyato tare da zaburar da mutane domin yin gayyatar.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments