Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Shimfiɗa
A babi na uku, an tattauna wasu daga cikin nau’o’in damfarar da ake gudanarwa a kan intanet. Kamar yadda aka ambata a babin, nau’o’in damfarar kan intanet suna da yawa. An yi ƙoƙarin taƙaitawa ne ga waɗanda suka fi shafar Hausawa. A wannan babi na huɗu kuwa, an ɗauki ɗaya daga cikin nau’o’in damfarar kan intanet, wato damfara ta kasuwanci, domin tattauna shi sosai tare da misalai. An yi hakan ne saboda Hausawa masu yawa sun faɗa komar masu yin irin wannan damfarar a baya. Haka kuma, da wasu masu yawa suna ƙoƙarin faɗawa a yanzu (shekarar 2024).. Babin ya kawo misalan kasuwancin damfara da aka yaudari Hausawa da su, aka raba su da kuɗinsu.
An Ci Wawa An Watse
A shekarun baya, akwai nau’o’in damfara daban-daban da aka yi wa Hausawa
masu alaƙa da kasuwanci. Ƙasar Hausa za ta daɗe ba ta mance da labaran waɗanda aka damfara da injin buga kuɗi ba. Ana iya alaƙanta abin da ƙarancin
ilimin yadda ake buga kuɗi a
lokacin da aka fara amfani da kuɗaɗen takarda. Da wannan jahilcin al’ummar
lokacin ne ‘yan damfara suka yi amfani domin cimma muradunsu. Waɗanda aka yaudara kuma kwaɗayi ya rufe musu idanu. Suka kasa tambayar
kansu dalilin da zai sa mai injin kuɗi ya sayar da shi a maimakon ya yi ta buga wa
kansa.
Haka kuma, za a daɗe ana
labarin “adashen gata” a ƙasar Hausa. Wannan nau’in adashe ne wanda ake zuba kuɗi, sannan a kwashi ninkinsu bayan makwanni
biyu ko wata guda (ko wani abu mai kama da hakan). Yadda har yanzu hoton
damfarar nan yake fitowa a adabin Bahaushe shaida ce ta tasirinsa. Shiri mai
dogon zango mai suna Daɗin Kowa (wanda
Arewa24 take kawowa) an nuna yadda Malam Barau ya yi irin wannan damfarar. A.R.
Ɗangulbi (keɓantacciyar
tattaunawa, 25 ga watan Nuwamba 2024) ya bayyana yadda aka gudanar da irin
wannan damfara a garin Gusau. Sun zo da kamfanin saka hannun jari mai suna Oil
and Gas. Sun zauna a Tudun Wada cikin garin Gusau (wajajen 2005). A.R. Bakura
(keɓantacciyar tattaunawa,
25 ga watan Nuwamba 2024) ya bayyana makamancin wannan da aka gudanar a
shekarar 1990 a Mafara, a lokacin Sarkin Mafara Mai Martaba Muhammadu Barno.
Sun zo da kamfani mai suna Versata (Ba Sata). Wannan ya faru a kusan dun ƙananan
hukumomi na jihar Sakkwato. M.F. Gummi (keɓantacciyar tattaunawa, 14 ga watan Mayu
2025).
Bayan samuwar intanet, a yanzu ana amfani da ƙarancin ilimin[1] da mutane suke da shi
dangane da abin da yake iya yiwuwa da wanda ba ya yiwuwa a kan intanet, domin
damfarar al’umma. Ɗaya daga cikin nau’o’in damfarar kan intanet ana
yin sa ne ta sigar kasuwancin kan intanet. Daga shekarar 2020 zuwa 2021 an
gudanar da manyan damfarar kasuwancin kan intanet da suka ritsa da Hausawa masu
yawa.[2] Abin ya kai a ce an sha
mutane sun warke, amma sai ga shi a shekarar 2024 an sake dawowa da wasu
guda biyu[3] masu zubi da tsari na waɗanda aka damfari Hausawa da su.
Ana iya cewa wannan salon gargajiya ne aka sabunta bayan shigowa da bunƙasar
intanet. A ƙasa an kawo misalan damfara guda biyar (5) daga cikin ire-iren waɗannan kasuwancin damfara da suka yi marfi
da kuɗaɗen wasu Hausawa. Ga su kamar haka:
a. MyBonus2u (2020 – 2021)
b. Insme (2020 – 2021)
c. Uwork (2020 – 2021)
d. Getapp (2020 – 2021)
e. Sha Yanzu Magani Yanzu (Instant Profit Investment)
[1] Har
yanzu bincike a cikin harshen Hausa dangane da intanet ba su yawaita ba. Duk da
haka, ana ci gaba da gudanar da bincike game da intanet a matakai daban-daban.
Daga cikinsu akwai Abubakar (2007) da 'Yartsakuwa (2017) da Gana (2020) da Sani
(2022) da Sani et al. (2023) da Sani & Yusuf (2024).
[2] (i)
MyBonus2u (2020 – 2021) da (ii) Insme (2020 – 2021) da (iii) Uwork (2020 –
2021) da (iv) Getapp (2020 – 2021)
[3] (i)
52u da (ii) Anchor
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.