Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Aka Yi Amfani Da Insme Domin Damfara a Kan Intanet

Daga

Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi

Damfara a Duniyar Intanet

An fara shi a shekarar: 2020

An rufe shi a shekarar: 2021

Sun yi amfani da kafar intanet ta: www.apps.insmeapp.com

Daga baya sun koma: www.app.xx00xx00.com

Ga duk wanda ya san intanet, daga kallon wannan liƙau ɗin kafar tasu ta biyu zai ɗora wa harƙallarsu ayar tambaya. Kafa ce wadda ba ta yi kama da na amintattun kamfanoni ba.

An gina wannan harƙalla a kan cewa fitattun (mashahuran) mutane (celebrities) suna bayar da kwangila ga kamfanin Insme domin kamfanin ya sama musu jinjina da tsokaci ga abubuwan da suke ɗorawa a kafafen sada zumunta. Haɗakar jinjina da tsokaci da kuma rabawa (sharing) na abubuwan da ake ɗorawa a kafafen intanet, shi ake kira da ‘engagment.’ A zahiri ana iya biyan mutum ga aiki makamancin wannan, amma bai kai a ce an tara mutane masu yawa domin gudanar da aikin ba. Daga ambatar irin wannan kasuwanci, waɗanda suka san tsarin neman kuɗi a kan intanet za su fahimci cewa ba abu ne wanda zai iya ɗorewa ba.

Waɗanda suka yi rajistar wannan kasuwanci, jingar da aka riƙa ba su ita ce yin jinjina da tsokaci ga abubuwan da aka ɗora a kafafen sada zumunta. Farko an fara da Instagram. Daga baya aka haɗa har da Facebook. Za a tura musu liƙau ɗin waɗansu abubuwa da aka ɗora, su kuma za su hau su yi tsokaci da jinjina.

Dangane da rajista kuwa, akwai buƙatar mutum ya saka wasu kuɗaɗe kafin ya yi. Kuɗaɗen da mutum zai saka sun danganta da matakin (level) da yake so ya samu. Suna da mataki na ɗaya (1) zuwa na tara (9). Kowane mataki sukan kira shi da ‘Insme’ (ke nan suna da ‘Insme 1’ zuwa ‘Insme 9’). Suna kiran jingar da ake gudanarwa da suna ‘mission.’ A jadawali na 4.1 da yake ƙasa, an bayyana yadda tsarin yake:

Jadawali Na 4.1: Tsarin Rajistar Insme

Mataki (Level)

Kuɗin Rajista (Subscription Fee)

Adadin Jinga a Kowace Rana

Kuɗin Kowace Jinga

Insme 1

1,680

3

28

Insme 2

6,888

5

69

Insme 3

62,888

25

125

Insme 4

148,888

38

195

Insme 5

298,888

70

213

Insme 6

638,888

290

256

Insme 7

1,488,888

290

256

Insme 8

2,988,888

580

258

Insme 9

6,388,888

1238

258

Madogara: Kafar Insme (www.apps.insmeapp.com) da sanarwa a kafafen sada zumunta

Idan aka nazarci jadawali na 4.1 da aka kawo a sama, za a iya kula da cewa, an gina harƙallar ne a kan tsarin “iya kuɗinka, iya shagalinka.” Iya adadin kuɗin da mutum ya saka, shi yake nuni da adadin jinga da za a ba shi a kowace rana, da kuma kuɗin da za a biya shi ga kowace jinga.

Kowane tsarin mataki da aka saya yana yin esfaya ne a cikin kwanaki sittin (60). Da zarar kwanaki sittin sun cika, to za a cire rajistar da mutum ya yi. Ba zai iya sake samun sababbin jinga ba har sai idan ya sake yin rajista.

Shi ma Insme yana da tsari na gayyata. Idan mutum ya yi gayyata, to zai riƙa samun kamasho a duk lokacin da wanda ya gayyata ya kammala wata jinga. Wannan yana nuna cewa, yawan kamashon da zai samu ya danganta da adadin hannun jari (kuɗin rajista) da wanda ya gayyata ya saka. Bugu da ƙari, gayyata a Insme ta kasance a cikin tsarin matakai biyu kamar haka:

a. Gayyata a Mataki Na 1 (Level 1 Referral): Waɗannan su ne waɗanda mutum ya gayyata kai-tsaye.

b. Gayyata a Mataki Na 2 (Level 2 Referral): Waɗannan su ne waɗanda mutanen da mai gayyatar farko ya gayyato su suka gayyato.[1]

Da suka tashi guduwa sun tafi da kuɗaɗen mutane da yawa. Wasu kuɗin aron su aka yi aka saka a ciki, wasu kuma sun saka kuɗin gado na mutane. Wasu kuma kuɗin adashe, wasu har bashin banki suka ci. A. Sani (keɓantacciyar tattaunawa, 21 ga watan Nuwamba 2024) da M.M. Manga ((keɓantacciyar tattaunawa, 24 ga watan Nuwamba 2024).



[1] Ma’ana a nan ita ce, idan Sallau ya gayyato mutane uku, to kowanne daga cikin mutane ukun yana mazaunin Gayyatar Mataki Na 1 ne a gare shi. Idan kuma wani daga cikin su ukun ya gayyato wasu mutane, to mutanen da ya gayyato ɗin suna matsayin Gayyatar Mataki Na 2 ga Sallau.

Manazarta: 

Sani, A-U.,  Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307

Post a Comment

0 Comments