Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Uwork
An fara yin sa a ƙarshen
shekarar: 2020.
An rufe a farkon shekarar: 2021.
Sun yi amfani da wannan a matsayin kafar intanet ɗinsu: www.uwork.com.ng.
Sun fito a matsayin kamfanin da
suke dillancin kayayyakin manyan kamfanoni da kasuwannin kafafen intanet. Sun
nuna cewa, suna da haɗin guiwa da kasuwannin kan
intanet irin su Jumia. A kullum za su bai wa waɗanda suka yi rajista tallace-tallace domin su ɗora a kafafen sada zumunta irin su Facebook da Instagram. A
nan za a iya lura da cewa, sun fito da wata hanyar da ta so ta kama hankali. An
dai san da cewa ‘talla’ hanya ce da ake samun kuɗi
da ita a kan intanet. Duk da haka, ba zai yiwu a ce an tara mutane da yawa ba,
kuma kowa ya riƙa samun
wasu ƙayyadaddun kuɗaɗe a kullum.
Suna da tsarin matakai daban-daban har guda uku. Kamar dai
yadda aka yi a Insme, mutum zai biya kuɗi ne domin sayen mataki mai
daraja. A kowane mataki mutum yake, talla guda biyu (2) za a ba shi a rana.
Abin da ya bambanta su shi ne, iya darajar matakin da mutum yake, shi yake nuni
ga kuɗin da za a biya shi ga duk tallan da ya yi. Ga matakan kamar haka:
a. VIP 1: Ana sayan sa ne a kan
dalar Amurka goma sha biyar ($15). Kuɗin
da ake biya ga kowane talla a wannan mataki shi ne dalar Amurka sifili da ɗigo shida ($0.6).
b. VIP 2: Ana sayan sa ne a kan
dalar Amurka ɗari da
hamsin ($150). Kuɗin
da ake biya ga kowace talla a wannan mataki shi ne dalar Amurka uku ($3).
c. VIP 3: Ana sayan sa ne a kan
dalar Amurka ɗari uku
($300). Kuɗin da ake
biya ga kowace talla a wannan mataki shi ne dalar Amurka biyar da ɗigo biyar ($5.5).
Shi ma Uwork yana da tsarin
gayyata. Duk wanda ya yi gayyata, to za a biya shi garaɓasar
gayyatar farko (initial referral bonus). Yawan abin da za a biya shi ya
danganta da hannun jarin da wanda ya gayyata ɗin ya saka. Bayan wannan garaɓasar
gayyata, akwai kuma kamasho da za a bai wa wanda ya yi gayyata a duk lokacin da wanda ya gayyata ya
kammala wata jinga.
Waɗanda aka gayyata sukan kasance
cikin mataki biyu, kamar haka:
i. Mataki Na 1 (Level 1): Waɗannan
su ne waɗanda mai akawun ya gayyata
kai-tsaye.
ii. Mataki Na 2 (Level 2): Waɗannan
su ne waɗanda mai akawun ba kai-tsaye ya
gayyato su ba. A maimakon haka, ‘yan Mataki Na 1 da ya gayyato ne suka gayyato
su.
Kamashon da ake samu daga gayyata a Mataki Na 1, ya
ninka wanda ake samu daga gayyata a Mataki Na 2.
Sun yi wani takun yaudara a
daidai lokacin da za su ‘ci wawa su watse.’ Asali suna amfani ne da
Flutterwave (https://www.flutterwave.com)
da Paystack (https://www.paystack.com)
a matsayin hanyar hadahadar kuɗi
da biyan kwastomomi. Daf da lokacin guduwarsu, sai suka kawo hanyar biyan kuɗi nasu na kansu mai suna Uworkpay (www.uworkpay.com). Daga nan kuma sai suka ce kwastomomi sun yi musu yawa.
Suka nuna cewa, bankuna suna ba su matsala wajen gudanar da hadahadar kuɗaɗen kwastomominsu. Sun bayyana
cewa, saboda a shawo kan matsalar, sun ninka kuɗin
yin rajista ga sababbin kwastomomi. Bugu da ƙari, sun yi ƙarin
kuɗi ga tsofaffin masu akawun wanda
kowa sai ya biya kafin ya ci gaba da hadahadar kasuwancin. Mutane da yawa sun sanya kuɗin da aka buƙata.
Daga nan kuma, kamfanin Uwork ya yi ɓatar
dabo!
Getapp
An fara shi a ƙarshen
shekarar: 2020.
An rufe shi a farkon shekarar:
2021.
Sun yi amfani da wannan kafar
intanet ɗin: www.getapp666.com
Tsarin Getapp kusan daidai
yake da na Insme. Yana da tsarin biyan mutane yayin da suka yi jinjina a
wasu abubuwan da aka ɗora a kafafen sada zumunta,
kamar hotuna ko bidiyoyi ko rubutu. Bugu da ƙari, yana da tsarin gayyata iri ɗaya da na Insme. A ƙasa an kawo matakan rajistarsu a cikin jadawali.
Jadawali Na 4.2: Tsarin
Rajistar Getapp
|
Mataki (Level) |
Kuɗin
Rajista (Subscription Fee) |
Adadin Jinga a Kowace Rana |
Kuɗin
Kowace Jinga |
|
VIP 1 |
₦20,000 |
5 |
₦266.6 |
|
VIP2 |
₦50,000 |
10 |
₦333.3 |
|
VIP 3 |
₦100,000 |
15 |
₦444.4 |
|
VIP 4 |
₦200,000 |
20 |
₦666.6 |
|
VIP 5 |
₦500,000 |
25 |
₦1333.3 |
Madogara: Kafar Getapp (www.getapp666.com)
da sanarwa a kafafen sada zumunta
A cikin jadawali na 4.2 da yake
sama, za a iya kula da cewa, Getapp sun yi amfani da VIP (VIP 1
zuwa VIP 5) a maimakon Insme (Insme 1 zuwa Insme 9).
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.