Ticker

6/recent/ticker-posts

Wasu Dalilan Saɓani a Zamantakewar Aure a Cikin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Akwai wasu dalilai waɗanda a mahangar al’ada su ne ake ganin a mafi yawan lokuta suke haifar da saɓani a zamantakewar aure, ga wasu daga cikin dalilan da adabi ya taskace su a cikin kare-karen maganan Hausawa kamar haka:

1. Makiyinka ba ya yabon ka, ko ka kama damisa ka ba shi

Damisa wata babbar dabbar daji ce mai jiki ɗabbare-ɗabbare mai zafin faɗa da mugunta, tana da kama da mage. Wannan karin maganar tana nuna cewa duk wanda ya ƙulla zamantakewa da maƙiyinsa, to duk irin ƙoƙarin da ya yi masa da duk kowane haɗari ya kutsa kansa ciki don ɗai ya hidimta wa abokin zamansa, ya kuma saka shi a cikin farin ciki da kyakkyawar rayuwa, matuƙar dai ba masoyinsa ba ne yake wannan cuɗanya da shi ba, to ba zai yaba masa ba, duk kuwa wahalar da ya sha; musamman a zamantakewar aure.

2. Laifin babba rowa, laifin yaro ƙyuya

Wannan karin magana tana nuna cewa babban dalilin da ke haifar da taɓarɓarewar zamantakewa a tsakanin abokan zama shi ne a duk lokacin da kowane ɓangare bai aiwatar da abin da ya dace ya aikata ba. Haka kuma, idan kowane bai sauke nauyin da ya rataya gare sa na ɗan’uwansa ba, hakan yakan kawo matsaloli musamman ta fuskar ma’aurata. A nan ana nufin shi magidanci shugaba ne, to ya riƙe girmansa tare da yin adalci ga matansa, muddun yana muzguna masu ko yana tauye wani haƙƙi nasu, to ba lalle ba ne su yi masa biyayya yadda yake so ba. Yana iya cewa ga yadda yake so a yi abu, su kuma su fanɗare masa, saboda rashin ɗaukar wannan nauyin nasu da aka rataya masa.

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments