Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Zamantakewa da ke gudana yau da kullum tsakanin mutane ba abu ne mai yiwuwa ba a iya kauce wa saɓani da rashin jituwa, musamman tsakanin ma’aurata (miji da mata) waɗanda suka fi kusanci da juna koyaushe fiye da sauran mutane. Akwai jerin karin magana da dama waɗanda suka yi nuni da dalilan da suke sa dole ne a samu saɓani a zamantakewa a wasu lokuta. Ga wasu daga cikin karin maganan kamar haka:
1. Zo mu zauna, zo mu saɓa
Wannan karin maganar tana nuni ƙarara da cewa matuƙar aka samu zamantakewa tsakanin
al’umma, to ba makawa wata rana za
a ci karo da saɓanin ra’ayi da fahimta saboda cuɗanya da mu’amalar rayuwa da take gudana tsakaninsu a zaman
tare na yau da kullum. Wannan karin magana tana nuna cewa, a ko’ina sai an sanya haƙuri ake cin ribar wasu abubuwa,
don haka shi ma aure ko zamantakewa harkar cuɗe-ni-in-cuɗe-ka ne, dole ne wata rana sai an
sami saɓani, don haka, Hausawa suka ce
tsakanin harshe da haƙuri
ma sai an saɓa, suna la’akari da kusanci da
ke tsakanin harshe
da haƙori, to in dai za a samu saɓani to ko ina fa za a iya samu, sai dai maganin saɓanin shi ne haƙuri,
“Haƙuri maganin zaman duniya”.
2. Ido wa ka rena? Wanda nike gani kullum
Wannan karin magana tana nuna cewa, a zamantakewa an fi
samun yawaitar saɓani tsakanin makusanta
kasancewar koyaushe suna tare da juna, to wannan sabo yana taka rawa sosai
wajen samar da saɓani. Wannan karin magana tana
nuna cewa, a zamantakewa akwai juriya, saboda shi zaman aure an gina shi ne da
niyar har sai mai rabawa
ta raba (wato mutuwa), don haka ko a kowane irin lokaci ana tare, ke nan tsakanin kishiyoyi da
maigidansu za a iya samun irin wannan rainin ya shiga tsakaninsu saboda zamansu a tare a koyaushe.
Don haka ba abin mamaki ba ne a samu raini tsakanin maigida da matansa ko kishiya da kishiyoyi.
3. Tsakanin harshe da haƙori ma ana saɓawa
Wannan karin magana tana nuna cewa komai kusancin mutane da
kuma duk tsananin so da ƙauna
tare da tausayin da suke yi wa junansu, a kwana a tashi, wata rana sai an samu
saɓani. Alaƙar miji da mata, za ta iya
yiyuwa a wani lokaci a samu saɓani, saboda kusancinsu da zama a
tare a kowane lokaci.
4. ‘Da sabon gini gara yaɓe’ da ginar rijiya gara yasa’
Wannan karin magana tana nuna cewa yin haƙuri da ci gaba da juriya game da saɓanin da yakan faru yau da kullum tsakanin abokan
zamantakewa, musamman miji da mata ya fi zama alheri bisa ga yanke wannan
zamantakewar da nufin ƙulla
wata sabuwar zamantakewa. Haka kuma, wannan karin maganar tana iya kallon idan miji
ya saki matarsa, tana can tana zawarci, sai kuma kwatsam ya zo da maganar wani
aure, to sai a nuna masa
cewa, da ya yi wani sabon aure, gwara ya dawo da tsohuwar matarsa, wadda ya
saka, wata ƙila ma ƙaddara ce ta raba auren, shi ne
Hausawa ke cewa, ‘da ginar rijiya gwara yasa’ da kawo wata wadda ma ba a san halinta ba dole sai an tsaya
an karance shi, ko kuma halinta ba mai kyau ba ne, to gwara wadda aka saba da
ita, aka san halinta na zahiri da baɗini, na ciki da na waje.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.