Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Sulhu na nufin sasantawa ko shiryawa tsakanin wani da wani. Shi kuma, rarrashi na nufin buga tufa ko wani abu da hannu sama-sama. Sulhu da rarrashi ana amfani da su ne domin a natsar da masu saɓani a kuma ba su haƙuri, duk dai da manufar samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsu.
Akwai jerin karin magana masu nuni a kan haka. Ga wasu daga cikinsu:
1. Rarrashi shi ne fadanci
Fadanci na nufin daɗin baki da zuga da nufin neman
shiga ga wani babba. Wannan karin maganar tana nuna cewa rarrashi yana da matuƙar muhimmanci wajen bayar da haƙuri da kuma samun daidaito
tsakanin waɗanda suka samu saɓani ko rashin jituwa, ta hanyar kwatanta shi da fadanci.
2. Komai ka haƙura da shi ka ga bayansa
Wannan karin maganar tana nuna cewa duk wani abu wanda mutun
ya yi juriya a lokacin faruwarsa, wata rana zai ga ƙarshen wannan matsalar ko
yanayin.
3. Duƙa wa wada ba ya hana ka tashi da tsawonka
‘Wada’ na nufin mutumin da aka haife shi da gajarci ƙwarai. Wani lokaci akan kira shi
Malam Dogo (CNHN, 2006 sh. 464). Wannan karin maganar tana nuna cewa duk wanda
ya girmama na ƙasa da
shi a girman daraja ko wani matsayi na rayuwa, kuma ya mutunta shi, to shi ma
zai ci gaba da
kasancewa da girmansa da mutuncinsa. Hakan yana nufin, idan kishiya ta mutunta
ta gaba da ita,
kuma ta ba ta
girmanta na zama shugaba a gareta. Hakan ba zai hana ta samun duk wata ɗaukaka da daraja ga maigidan da sauran mutanen gida ba. Hasali
ma, idan ta yi hakan, za ta ƙara
samun ƙima da
daraja a gidan da ma wanda ya ajiye su. Shi ake ce wa: “Duƙa
wa wada ba gajiyawa ba ne”.
4. Babba juji ne
‘Juji’ na nufin wurin da ake tara shara, daidai da bola ko
jibji (CNHN, 2006 sh. 220). Wannan karin magana tana nuna cewa babba matattarar
ajiye kowace matsala da damuwa da koke da sauran abubuwan da ba daidai ba ne,
saboda haka sai ya yi ta haƙuri
da juriya a kan matsaloli da halayen rashin daidai da zai yi ta fuskanta daga ƙanana da ke ƙarƙashinsa. Haka yake a zamantakewar aure tsakanin kishiya da
kishiyoyinta, dole ne sai ta yi haƙuri
da juriya da duk wasu abubuwa a matsayinta na uwargida, domin kuwa duk abin da babu ko wata matsala aka samu za a ce laifinta ne don ita
ce babba a cikin gidan, shi ya sa
duk abin da ya tari kanta za ta ɗauka ba tare da ta nuna ɓacin rai ba. Wasu Hausawa suna cika karin maganar kamar
haka: Babba juji ne, kowa ya ɗebo shararsa, ya watsa.
5. Matar na tuba, ba ta rasa mijin aure
‘Tuba’ na nufin neman gafara daga wani da dawowa kan hanya
ta gari da daina aikata laifi (CNHN, 2006 sh. 440). Wannan karin maganar tana
nuna cewa duk matar da take neman gafarar miji a duk lokacin da ta aikata ba
daidai ba, kuma take ƙoƙarin dawowa zuwa ga aikata abin
da ya dace, tare da barin aikata abin da bai dace ba, to wannan mata ba za ta
rasa miji a zamantakewar aure ba. Aurenta zai yi ƙarko, saboda ta yarda ta bayar da haƙuri idan ta yi laifi.
6. Kowa ya hau dokin zuciya ya sauka da sauri
Dokin zuciya na nufin aikata wani abu cikin fushi, daga baya
a yi da-na-sani. Wannan karin magana tana nuna cewa duk wanda ya yi yunƙurin aiwatar da wani abu cikin fushi a yanayin zamantakewar
aure, to ya yi gaggawar nisantar aikata haka, don gudun nadama.
7. Idan hankali ya ɓata,
hankali ke
nemo shi
‘Hankali’ na nufin lura da sanin ya kamata. Wannan karin
maganar tana nuna cewa lokacin da abokin zamantakewa ya rasa natsuwa ya kuma
fita hayyacinsa, yana aikata rashin ya kamata. To shi ɗayan abokin zamantakewarsa ya yi amfani da natsuwarsa da
lurarsa ya dawo da shi bisa ga abin da ya dace, madadin ya biye masa su taru su aikata
ba daidai ba, daga nan nadama ta biyo baya. Haka kuma an cewa:
8. Idan rai ya ɓaci hankali ba ya gushewa
Wannan karin magana tana nuni ne, a kan cewa, duk abin da mutum zai
yi na rashin mutunci ne ko faɗa, to ya riƙa aunawa, saboda ba kowa ne ake
ci wa
mutunci ba, ta yi yu sai ka gama rashin arzikin sai kuma ka gano ashe bai dace
ba. Haka a wurin zamantakewa, ya yiwu idan kishiya ta tashi rashin kunyarta, to ta san irin
kalaman da za ta yi amfani da su wurin mayar da martani, kila abin da za ta faɗa zai zame mata abin da na sani
a nan gaba. Ana amfani da wannan karin magana wurin shiga tsakani na mutum da
mutum ko mata da miji, kishiya da kishiya ko mata da uwar miji ko danginsa,
domin kwaɓa da hannun ka mai sanda ga
mutum ya san irin kalaman da zai dinga furtawa ga abokin faɗa, ta yiwu wannan kana amfana da shi.
9. Mahaƙurci mawadaci
Wannan karin maganar tana nuna cewa wanda ya kasance mai haƙuri, shi ne wanda yake samun
yalwar arziki da kwanciyar hankali a yanayin zamantakewa.
10. Kowa ya yi haƙuri shi ke samun riba
‘Riba’ na nufin ƙarin
kuɗi da ɗan kasuwa ke samu bayan ya sayar da kaya sama da farashin da
ya sayo (CNHN, 2006 sh. 370). Wannan karin magana tana nuna cewa duk wanda ya
yi haƙuri a kan wani abu da bai yi
masa daɗi ba a zamantakewa, shi ne yake
samun abin da ya fi wannan amfani a rayuwa.
11. Haƙuri maganin iyakar kissa
‘Magani’ na nufin abin da samuwar sa kan kore wani daban.
Ita kuwa kalmar ‘kissa’ na nufin yaudara, daidai da kisisina. Wannan karin
maganar tana nuna cewa mai haƙuri
shi ne yake samun cimma nasarar ganin ƙarshen
kowace irin mugunta da kuma yin galaba a zamantakewa. Wannan karin magana tana
nuni da irin haƙuri da
juriya na kishiya mai kishiyoyi
a gida, saboda duk irin makirci da kisisina da ake yi mata da nuna mata tsana a
cikin gidanta ba ta
tayar
da hankalinta ba balle abin ya yi tasiri a gare ta, wanda idan ta fito da abin da ake yi mata, wata ƙila za ta sami rashin jituwa
tsakaninta da maigidanta, wani lokaci ma har abin ya taɓa aurenta da rayuwar ‘ya’yanta,
to amma idan ta haƙura, duk
abubuwan za su wuce, za a kai ga lokacin da ma kamar ba a yi ba, sai dai tarihi
da kuma ba da
labari ga ‘yan baya.
12. Mai haƙuri yakan dafa dutse har ya sha romonsa
‘Dutsi’ na nufin wani dunƙulallen abu mai tauri da ƙarfi da ake samu a ƙasa.
Ita kuwa kalmar ‘Romo’ na nufin miyar da ake yi marar kauri wadda ba a kaɗa mata komai ba, daidai da romuwa. Wannan karin magana tana
nuna cewa haƙuri abu
ne wanda yake ɗaukar lokaci mai tsawo ana yin
sa, kuma duk wanda ya yi dogon haƙuri,
shi ne yake samun jin daɗin rayuwa fiye da yadda yake tsammani a
zamantakewa. Kasancewar a zahiri dutsi ba ya da romon da idan aka dafa shi za a
samu. Wannan karin magana tana nuna cewa, idan kishiya ta yi haƙuri a gidan mijinta akan wata
muzgunawa da ake yi mata a tsakanin kishiyoyin ta, hakurin da juriyar da ta yi shi
zai ba ta damar samun
ɗaukaka ita da ɗiyanta, wanda da ba ta yi haƙurin
ba, da hakan bai samu ba, ‘Mahaƙurci Mawadaci’.
13. Da garin marar haƙuri akan sha ruwa
‘Gari’ na nufin niƙaƙƙe ko dakakken hatsi, ko wani abu
kamar rogo da sauransu, wanda ga al’ada sai an jira an sarrafa shi sannan a sha
shi. Wannan karin maganar tana nuna cewa duk wanda ya kasance ba ya da haƙuri, ko kuma yana da gajeren haƙuri, to ba a kan more wa amfanin
lamuran zamantakewa da aka gina tare da shi ba, a lokacin da cin moriyar abin
ya yi. Wannan karin magana tana nuna cewa, irin matan nan da ba su da haƙuri kan wasu abubuwa, waɗanda suka jiɓinci gidan aurensu, ɗan
abu kaɗan zai tayar mata da hankali har ma ta kai ga
sun rabu, kan abun da bai kai ya kawo ba, daga baya ta gano ta yi kuskure wanda
a lokacin da ta
yi nadama, ba shi da wani amfani a gare ta, saboda hakan ya haifar mata da tsana da ƙi ga shi mijin ko uwarsa ko ma
danginsa, da hakan za su hana a dawo da ita, anan sauran kishiyoyinta sun samu abin
da suke so ke nan,
ta bar masu gida, ita kuma saboda rashin haƙurinta ya ja mata illar.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.