Daga
Abu-Ubaida Sani
Jibril Yusuf
Muhammad Sulaiman Abdullahi
Bayan misalan kasuwancin kan intanet na damfara da aka tattauna a sama, akwai wani nau’in da duk ya fi waɗannan alamun rashin gaskiya. Shi ne nau’in kasuwancin kan intanet wanda yake da tsarin sha yanzu magani yanzu. Ana gabatar da shi ne a matsayin kasuwancin da mutum zai sanya hannun jari, sannan a ninka masa uwar kuɗin a cikin awanni uku (3) zuwa ashirin da huɗu (24) kacal!
An fi amfani da akawun ɗin kafafen sada zumunta da aka
yi wa kutse wajen yaɗa wannan damfara. Yayin da aka
yi kutse a akawun ɗin wani mutum mai mutunci, za a
yi amfani da yardar da al’umma suka yi masa domin a yaudari waɗanda ba su farga ba. Ana yawan amfani da akawun ɗin mutane na Facebook da WhatsApp domin yaɗa wannan damfara.
Misali irin wannan kasuwancin sha yanzu magani yanzu
shi ne Access Real Investment. Wannan wani nau’in kasuwancin damfara ne
wanda aka ɗau lokaci ana
yaɗa shi a kan kafafen WhatsApp da
na Facebook. A duba hoton da yake ƙasa:
Hoto Na 4.1: Zauren WhatsApp na Access Real
Investment
Madogara: Hoto
daga zauren Access Real Investment na WhatsApp
A wannan hoto, za ga a cewa akwai har mutane ɗari huɗu da casa’in da shida (496) a
cikin zauren (a ranar 24 ga watan 12 na shekarar 2024). Suna tattara waɗannan mambobin ne ta hanyar tura saƙonni a WhatsApp da Facebook waɗanda suke ɗauke da liƙau ɗin shiga zauren. Saƙonnin
suna ɗauke da bayanin kasuwancin kan
intanet wanda ake yi a samu kuɗi nan take. Kamar yadda suka
nuna, a cikin awa ɗaya ana samun riba ninkin abin
da aka saka sau uku (x3). Su za su riƙe
kashi ɗaya cikin uku, sannan su turo wa
wanda ya sa kuɗi kashi biyu cikin uku. Ga yadda
abin yake:
a. Wanda ya saka 100,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 200,000
b. Wanda ya saka 150, 000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 300,000
c. Wanda ya saka 200,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 400,000
d. Wanda ya saka 250,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 500,000
e. Wanda ya saka 300,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 600,000
f. Wanda ya saka 350,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 700,000
g. Wanda ya saka 400,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 800,000
h. Wanda ya saka 450,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 900,000
i. Wanda ya saka 500,000, a cikin awa ɗaya zai samu ribar 1,000,000
Ire-iren waɗannan kasuwancin damfara suna
nan a kan intanet. Suna yaudarar makwaɗaita da cewa za su samu ninkin
abin da suka saka cikin awa ɗaya ko biyu ko dai wani ƙanƙanin lokaci. Za a iya lura da cewa, a cikin hoto na 4.1 da
aka kawo a sama, sun rufe zauren ta yadda su kaɗai ne suke iya tura saƙonni. Sun yi hakan don hana
mutane tura saƙonnin
gargaɗi ga waɗanda ake faman damfara.
Ire-iren waɗannan zaurukan sukan yi amfani da ‘yan
kore. Lokaci zuwa lokaci ‘yan korensu sukan tura saƙonnin godiya kan cewa sun samu
riba daga wannan kasuwancin da aka ɗora su a kai. Har sukan turo
hoton alat ɗin banki na shigowar kuɗaɗen da suka samu. A duba misalin
da yake hoto na 4.2 a ƙasa:
Hoto Na 4.2: ‘Yan kore a zauren WhatsApp na
Access Real Investment
Madogara: Hoto
daga zaurensu na WhatsApp
A wannan hoto, za a ga wanda ya turo saƙon yana iƙirarin cewa ya samu kuɗi naira miliyan bakwai bayan (₦7,000,000)
ya saka hannun jarin miliyan uku da dubu ɗari biyar (₦3,500,000). Kada a manta, duk wannan riba ya same ta ne
cikin awa ɗaya kacal!
Manazarta:
Sani, A-U., Yusuf, J. & Abdullahi, M.S. (2025). Damfara a duniyar intanet. SAS Publishers. ISBN: 978-978-695-575-9. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513307
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.