Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Uwar kishiya wata muhimmiyar macce ce mai taka muhimmiyar rawa a cikin zamantakewar aure a gidan ɗiyarta. Uwar kishiya ita ce uwar matar da aka auro a gidan da ke da matan aure fiye da ɗaya. Ta kasance wata mai ba da shawara ta musamman ga yarta, kuma ita ce mai ba da gudummawa ta musamman a kan harkar kishi tsakanin ‘yarta da kishiyoyinta, haka kuma duk wani abu da ɗiyar take so na harkar gyaran aure ita ce ke ƙullo mata ko jiƙo mata ko kawo mata a gidan mijinta domin ta gyara aurenta.
1. Ba kukana ba, uwar kishiya ta
mutu.
2. Ɓatan kai, shawara da uwar kishiya.
3. Da zaman banza, gara aikin
uwar kishiya.
4. Ribiɗin leɓo,
shawara da uwar kishiya.
5. Salula, shawara da uwar
kishiya.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.