ƊAN RIƘO DA ‘YAR ZAMAN ƊAKI A FARFAJIYAR KARIN
MAGANA
Daga
Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani
Ɗan Riƙo
Ɗa shi ne abin da aka haifa, mutum ko dabba ko wata halitta. Riƙo shi ne kula ko ɗaukar nauyin yin wani abu. Duba da wannan ma’ana ta ƙamus, za mu iya cewa, ɗan riƙo wani mutum ne da ake kula da shi ko ɗaukar nauyin shi a ƙarƙashin waɗanda ba mahaifansa ba.
1. Ɗan
wani da uwar wani tagwayen ‘yan wuta
2. Ko ɗan riƙo ya san kifinsa
Yana da kyau a fahimci cewa “ɗan riƙo” a cikin wannan karin magana na biyu ya sha bamban da
ma’anar da aka kawo a sama. Ɗan nan yana
nufin ‘ɗan kaya’ wato yaron da yake riƙe ko kula kayan masunci yayin da ya shiga ruwa, Galibi
akan sallame shi da kifi ne. Wannan ne ya sa ake cewa ɗan
riƙo ya san irin kifin da ya dace da shi
domin kuwa masunci ba zai zaɓe kifi mai girma da kyau ya ba shi ba. Duk da haka, ana
iya faɗaɗa ma’anar domin ya shafi ɗan
riƙo da aka sani a gidan aure. Yana iya
fuskantar wariya da ƙasƙanci domin ba shi da “uwa a gindin murhu” don haka dole
ya yi “kukan miya” ba ma kifi ba.
Waɗannan karin magana guda biyu, suna nuna irin zamantakewar da ke tsakanin shi ɗan riƙon da uwar riƙonsa.
‘Yar Zaman Ɗaki
Muhammad (2020 sh. 57) ya bayyana ‘yar
zaman ɗaki da cewa; wata yarinya ce ƙarama kimanin shekara huɗu
zuwa biyar da ake bar wa amarya ta kwana biyu don ta ɗebe
mata kewa don baƙunci. A wasu wuraren akan bar wannan
yarinyar har ta girma, kai wani lokaci ma har zuwa aurenta, amma wani lokaci da
zaran ta ɗan kwana kaɗan amarya ta saba, to sai a mayar da ita gidansu.
Hikimar ɗaukar ‘yar zaman ɗaki ita ce, taimaka wa amarya wajen ɗebe mata kewa da yi mata wasu ‘yan aikace-aikace don kai
wani abu ko karɓowa daga ‘yan gida, kasancewar
ta baƙuwa a gidan. Dalili kuwa shi ne,
a al’adar Hausawa, amarya tana da
kunya da kawaici, don haka ne ma ba za ta iya bayyanar da kanta ba a tsakar
gida, mutanen gida su gan ta kasancewar ta amarya, kuma baƙuwa a gidan (Adamu, 2014 sh. 4),
wani lokaci takan zauna ne tsawon wata uku (Yahya da wasu, 1986 sh. 180).
Wannan al’adar a halin yanzu, idan har ba ta mutu ba, to ta
kama hanyar ɓacewa. An samu karin maganar
Hausa wadda ta taskace wannan al’adar ta ‘yar zaman ɗaki kamar haka:
1. Ba ni tsoron amarya da ango balle ‘yar zaman ɗaki
Wannan karin maganar tana nuna irin yanayin zafin kishin da
yake gudana tsakanin uwar gida da amarya musamman a ranakun farko – farko na
amarci, inda uwargida take fitar da kishinta a fili tare da bayyana cewa ba ta
tsoron kowa a gidan, kama daga mijinta har amarya ballantana ‘yar zaman ɗaki da wa’adinta a gidan gajere ne. Uwargida kan faɗi
karin maganar ne
don tsokanar faɗa ko huce haushi.
Mutane da kishiyoyi suna amfani da wannan karin magana mai ɗanɗanon habaici domin su nuna cewa, mutum mai muhimmanci ma a wurin ba sa shakkar shi, balle wani wanda yake raɓe da shi.
Manazarta
Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.