Ticker

6/recent/ticker-posts

Abokan Ango Da Kawayen Amarya a Cikin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Abokan Ango

Wasu mutane ne makusantan ango waɗanda suke taya shi hidimar aure, a lokacin bukin aure. Abokan ango, su ne waɗanda ke tare da ango yayin shagulgulan aure, su ne masu ɗawainiya ga ƙawayen amarya ta hanyar ba su duk wani abu da ake bai wa ƙawayen amarya wanda ya danganci al’ada a wurin gudanar da bukukuwan aure, kuma da su za a sa ango lalle da duk wata al’ada da ake yi wurin gudanar da bukin auren, kuma su ne za su ɗauko amarya su kaita har ɗakin mijinta, a kuma gudanar da al’adar nan ta sayen baki, sannan kowa ya watse a bar ango da amaryarsa a ɗaki. Ga misalai a ƙasa:

1. Abokin ango mai wahalar banza

2. Daga yau sai yau, rawar barin ango

3. Izgili angwaye wasa bakin rijiya

4. ‘Yan matan ango makafi ne, na amarya ke yi masu jagora

Ƙawayen Amarya

Su ma wasu makusanta amarya ne, waɗanda suke taya ta hidimar buki a yayin gudanar da bukukuwan aure, tun daga sa ta lalle har ya zuwa raka ta gidan miji. Ƙawayen amarya, su ne budare ko ‘yan mata waɗanda suke tare da amarya a lokacin da aka sa ta lalle, suna tare da ita a duk gidan da za ta zauna da kuma duk inda za ta tafi da inda za ta kwana. A al’adar Hausawa ba a barin amarya ita kaɗai a ɗaki ko gida, dole ne akwai ‘yan tanyon zama domin ɗebe mata kewa da kuma yi mata wasa da wasu hidimomi na wannan tsakanin lokacin bukin aure. Haka kuma, su ke girka abin da amarya za ta ci tare da su, hatta ma gumbar da ake ba wa amarya tare suke sha, sukan gudanar da komi a tare har lokacin da za a kai amarya ɗakinta, in aka yi sayen baki su ma sai ko wace ta kama gabanta sai gobe a ƙara dawowa domin kimtsa mata wasu kayayyaki da kuma dafa mata abincin da za ta ba angonta. A ƙasa an kawo misali:

1. Ko mi daɗinki da miji, inji ƙawar amarya

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments