Ticker

6/recent/ticker-posts

Tazuru a Madubin Karin Magana

Daga

Shafa'atu Salihu Labbo
Abu-Ubaida Sani

Aure a Kunshiyar Karin Magana

Mutumin da ya shafe shekaru masu yawa ba tare da auren fari ba, shi ake kira tuzuru. Hausawa suna kallon mutum mai shekarun da suka kai 30 zuwa 40, ya kai munzalin ya yi aure amma bai yi ba, kuma babu wani dalili wanda ya hana shi yin auren a matsayin tuzuru. Turuzanta/tuzurantaka/tuzurci abin tsangwama ne a al’adar Hausa.

Hausawa sukan alaƙanta gwauro da tuzuru da lalaci da ɓarna a cikin al’umma. Za a iya ganin wannan a cikin waƙar da sarkin gwauro yake yi a lokacin wasan kamun gwauro a lokacin azumi. Ga yadda waƙar take:

Sarkin Gwauro: Sarki ya kama ɓarawo,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Ya manta da gwauro,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Wai ɓarayi ne ke da ɓarna,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: An manta da gwauro.

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Tunda sarki ke kamun ɓarayi,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Ni ko zan kama gwauro,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Wasa muka zo ba faɗa ba,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Mun zo mu kama gwauro,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Mai mata ba mai taɓa ka,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Amma za mu kama gwauro,

‘Y/Amshi: Ga gwauro a titi.

Sarkin Gwauro: Ya yi azumi tara daidai,

‘Y/Amshi: Cikinsu babu na zaɓe.

    (Sani da Gobir, 2021 sh. 417-418)

Kare-karen magana da Hausawa suka ƙirƙira kan tuzuru suna ƙara nuni da tsangwamar da yake sha a wurin al’umma. Ga wasu daga ciki:

1. Ba sai an faɗi cewa ga sauyi ya zo, wai tazuru da ya ga dallof a ɗaki har da ‘yan filalla gefe

2. Gyarawa, ɗakin tuzuru na zaure

3. Gyarawa, tazuru ya yunƙura zai yi aure

4. Mi ya kai tuzuru leƙa tukunyar ɗumame

5. Tuzuru wanda ya fi gwauro ɓarna

Manazarta

Labbo, S.S. & Sani, A-U. (2025). Aure a ƙunshiyar karin magana. Amsoshi Academic Publishers. ISBN: 978-1-257-07209-5. DOI: https://doi.org/10.5281/zenodo.19513449 

Post a Comment

0 Comments